← Book details Yarinyar Baba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 7

Sashe 4

Yarinyar Baba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

YARINYAR BABA
[05:04 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By
Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```*
*Page* 91-100 Da misalin 'karfe d'aya aka tashi
su Hassan da hussaina driver yazo d'aukarsu
ilham naganin haka ta tattara yanata-yanata
tayima 'kawayenta sallama, duk da ba wannan
lolacin bane na tashinsu tunda yanzu ilham tana
ss 3 ne sai 'karfe biyu ake tashinsu, yan biyu
kuma suna primary 2 ne ana tashinsu 'karfe
d'aya, abinda yasa zata bisu shine tanaso tayi
amfani da wannan damar taba 'kungiuarsu jinin
momynta, dan bakin iya 6acin rai yau momy ta
6atamata, amma daga yau angama. Saboda haka
'yan biyu na isa gurin motar itama tana isowa,
sun Shiga itama shiga kawai tayi ta zauna batare
datacema kowa 'kala ba, husaina ce ta kalleta
tace aunty ba'afa tashekuba kuma naga kin
shigo mota,..... Ilham ta daka mata tsawa na
shigo d'in dan ubanki kinfini sanin ba'a
tashemuba d'in, ainasani yanzu nakeson tafiya.
Hassan yace "mudai ki sauka kibari daddy yazo
ya d'aukeki tunda dama kullum shine ke kawoki
kuma yana d'aukok....... Kafin ya ida fad'a tasa
hannu ta dokemar baki, cikin masifa tace tunda
bansan da hakaba Kaine zaka gayamani
shashasha...ta buga uban tsaki mtswww...
Sannan ta kalli driver Wanda yake zaune shi
betafiba kuma bece uffan ba, cikin d'aga murya
tace dallah Malam mutafi kana 6atamin lokaci.
Jiki na 'kyarma driver yaja mota suka d'au hanya,
dan yasan akan ilham ze iya rasa d'an Albashin
dayake samu, kuma gashi dashi ya dogara.
Montocin da basu wuce sha biyuba suka sadasu
da gida, sukayi horn megadi ya bud'emasu get
suka shige. Bayan ya ajiye motar inda aka
tanada domin ajiye motoci, ilham ce tafara
bud'ewa tafita, d'akinta ta wuce kai tsaye tafad'a
toilet tayi wanka sannan ta canja 'kaya, ta
kwalama Ameeno kira, saida gaban Ameeno yayi
mugun fad'uwa danjin ilham a gida yanzu, kuma
tasan indai taje school ba yanzu bane lokacin
dawowarta, jiki na 'kyarma ta isa ta dur'kusa
tace gani, ilham tace jeki kawomin lemu da cake
yauba saikin yimin girkiba, cike da farin ciki
Ameeno tabar d'akin zuwa kitchen dan kowoma
*_YARINYAR BABA_* abinda ta bu'kata. Saida ta
kammala sannan tafita zuwa d'akin momynta,
bata isketa d'akiba sai motsi dataji a kitchen
saboda haka nan tanufa dan tasan yanzune
lokacin da Momy ke shiga kitchen domin
had'ama daddy abinci. Ranta yayi fari dan ganin
Momy zaune kan kujera a kitchen tana yanka
d'anyar ku6ewa, domin yau abinda zata had'ama
megidan kenan tuwom semo da miyar d'anyar
'ku6ewa. Love u all Zee Elkaseem

YARINYAR BABA
[07:16 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 101-110
cikin ladabi ilham ta rissina "Momy sannu da aiki,
cike da mamaki Momy ta d'ago ta kalleta ta
girgiza kai tace "yauwa, tare da tambayarta "ya
akayi kika dawo yanzu Alhalin kuma nasan
lokacin tashinku beyiba,?
Ilham tad'an 6ata fuska tadafe kanta cikin
marairaicewar murya tace "Kaine ne yakemun
ciwo shine na dawo amma nasha magani, Momy
ta tausayamata tace "ayya Allah sauwa'ke ilham
ta Amsa da "Ameen,
daga nan suduka ba wanda ya'kara magana
Momy ta maida hanakalinta kan yankan ku6ewar
datakeyi.
Wani shu'umin murmushi ilham tayi sannan takai
dubanta ga hannun Momy dataketa ayki da
sabuwar wu'ka sai wal'kiya take, tsawon minti
biyar tana kallon wukar tare da hannun Momy ko
'kiftawa batayi, wani haske yafito daga idanunta
yafada kan wu'kar hakan yayi dai-dai da fad'uwar
'ku6ewar da Momy ke yanakawa 'kasa tare da
shigewar wukar cikin tafin hannunta, wani irin
mugun 'yanka wu'kar tayimata, aiko kamar jira
take jini yafara kwarara ba tsai-tsayawa.
Momy ta ri'ke hannunta dake zubar jini tanata
salati, cikin rud'ewa ilham takama momy tana
tambayarta lafiya, Momy kasa yimata magana
tayi saboda tsabar rad'ad'in da gurin keyimata,
ga jini sai zuba yake ba tsai-tsaiyawa.
Cikin rud'ewa ilham tad'auki waya takira dadynta
tagayamshi halin da Momy keciki dan ganin
datayi Momy ta galabaita, numfaahinta na niyyar
d'aukewa.
Da sauri daddy yabaro office d'insa dukda
d'umbum jama'ar dake jiransa hankalinshi tashe
yake tu'kin bako sallama yashigo gidan kwance
ya iske momy tsakiyar falon ba Alamar numfashi
tattare da ita, gefe kuma ga ilham da 'yan biyu
sai faman kuka suke.
Cikin kuka ilham tanufi dadynta tafad'a jikinsa
tana kuka "daddy ka taimakemu kada Momy ta
mutu, wayyo nashiga ukku wayyo daddy....
Cikin tsananin rud'ewa daddy yacire ilham daga
jikinsa yanufi inda momy take kwance ba Alamar
numfashi tattare da ita, ga kuma hannunta har
yanzu jini na zuba, cikin tsananin rud'ewa
yacema ilham "taimakamin musata mota mukaita
asibiti,
Haka kuwa akayi da taimakon ilham akasa Momy
mota suka nufi asibiti ilham sai kuka take duk ta
wani firgice ta fita hayyacinta yanda kasan
batada masaniya akan ciwon Momyn.
Sun Isa asibiti emergency aka nufa da ita, nan
likitoci suka taru kanta, sun gano tarasa jini sosai
ajikinta saboda haka idan ba'ayi gaggawar
'karamata jiniba za'a iya rasa rayuwarta.
Ilham kuwa yanzu nadamar gaske tayi datasan
hakane da bata amince da zama cikin 'kungiyar
_*JIN DADIN RAYUWA*_ ba dan gashi tana gani
zata rasa momynta.
Daddy kuwa cewa yayi a d'ebi jininsa a'karama
Momy, cikin sa'a aka auna jinin akaga ze iyabata
cikin 'kankanin lokaci aka eba aka 'karamata.
Kwanan Momy biyar asibiti aka sallamota, duk
ilham tabi ta rame saboda fargaba, tana gudun
kada wataran awayi Gari Momy ta mutu.
Cikin sati Momy ta warware kamar batasha
jinyaba, sannan hankalin ilham yadawo jikinta,
Sosai daddy ke kula da Momy tun ranar datayi
rashin lafiya, ba'karamar Shiga damuwa yayiba,
yanzukam Alhmdlh sunkoma normal Kowa yasaki
jikinsa suncigaba da rayuwa kamar yanda suka
saba.
Love u all
Zee Elkaseem

YARINYAR BABA
[07:21 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 111-120
A yau 'kungiyar *Aji dad'in rayuwa* tayi bikin
karrama ilham akan namijin 'ko'karin datayi gurin
kawo jinin momynta, hakan ba 'karamin cigaba
yakawoma 'kungiyarsuba, dan tsafi ya nuna cewa
shigowar Ilham wannan 'kungiya babban
cigabane agresu.
Saboda haka Abigael ta tabbatarma ilham daga
'yau batada sauran 6acin rai danagane da wani
d'an Adam adoron 'kasar nan, kuma daga yau
zata fara jin dad'in rayuwarta batare da momynta
ta takurataba, dama batada matsala da daddy,
Hakeem kuwa sai Kallon ilham yake yanamata
murmushi, itama murmushin take tare dajin dad'i
acikin ranta.
***********************
Tun daga wannan lokacin ilham tari'ka yin abinda
taga dama fita kuwa idan zatayi Momy bata isa
tahanataba, kaya sai wanda taga dama take
sanyawa, mini siket da body hug, da wando
pencil sune kayan fitar ilham zuwa unguwa
daddy kuwa yana gani beta6a hanataba, saima
duk abinda take bu'kata ya sakarmata mukullin
ma'ajiyar kud'insa kullum ta eba yanda takeso
bedamuba domin kud'in akwaisu.
Mota ilham ta gayama daddynta tanaso
yasiyamata, gaban momy suka ajiye magana ta
fad'amashi irin wacce takeso yayimata
Al'kawarin zuwan motar cikin wannan satin,
Momy kuwa data yun'kura zatayi magana tanaso
tahana amma bakinta sai yakasa furta kome
kamar ansa kwad'o da makulli an rufemata baki.
Saida suka gama maganarsu daddy yacema
ilham taje ta shirya ze kaita shopping, aiko cike
da murna tanufi d'akinta shima nashi d'akin
yawuce.
Sunfito cikin shiri daddyn ilham sanye cikin jaket
masu ruwan 'kasa ilham kuma wani matsiyacin
wando tasanya wanda yafito da duk wani shape
na jikinta, sai wata riga wacce batada maraba da
bes, kanta bako d'an kwali tayi parking d'in
gashinta, sannan suka wuce momy tana zaune
tana kallonsu tanason magana amma takasa.
Sai bayan fitarsu wani kululun ba'kin ciki
yatokaremata a wuya, da sauri tashige d'aki
tafad'a gado tafashe da kukan ba'kin ciki.
Kuka tayi sosai sannan tatashi jikinta duk ba
kwari tafad'a toilet tayo Alwala ta kabbara sallar
nafila, bayan tagama ta dad'e zaune tana addu'oi
sannan taji sau'kin ba'kin cikin dake damunta.
Cikin satin motar ilham ta 'karaso had'ad'iyar
mota 'kirar camry dunkulalliyar kalar ja me duhu,
ilham tayi farin ciki sosai, tun daga lokacin
ta'karo wulakanci tacigaba da baza tsiyarta.
Momy kuwa ta du'kufa da addu'a kullum ba dare
ba rana, saboda tayi imanin addu'a itace takobin
mumuni.
Love u all
Zee Elkaseem
Chapter 4 · 0% Book details