Sashe 1
Yarinyar Baba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
YARINYAR BABA
[01:02 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 1-10
"Gaskiya ni Momy bazani school d'innan ba,
kawai sai mutum yaje wannan banzan malamin
yari'ka yimashi kallon banza, kamar wata tsiya
yafika, Ilham tafad'a tana shagwa6a.
Matar data kira da Momy tace "ke ilham banison
shashancin banza da wofi, ki maza ki tashi kitafi
tun kafin ranki yayi mugun 6aci cikin gidannan.
Wasu 'kyawawan yara su biyu mace da namiji
'yan kimanin shekaru bakwai, suka fito sanye
cikin uniform d'insu, gwanin ban sha'awa sukace
"momy mun shirya, sannan suka maida dubansu
ga ilham wacce keta zo6ara baki ita a dole
bazata school ba, sukace "aunty ilham dan Allah
ki shirya mutafi kinsan idan muka makara uncle
zemana duka.....
Cikin masifa ta kallesu ta daka masu uwar tsawa
"bazaniba nace ku wuce Ku bani wuri idan ba so
kuke in 6ata maku rai ba, dan uwarku ni
sa'arkuce dazakuce sai kunjera dani kuntafi
school.....
Saukar wani lafiyyayen mari taji wanda momynta
ta shimfid'a mata a kunci, wasu star's tagani
suna zagaya mata kai saboda bala'in zafin marin
saida ta fasa 'kara.
Hakan yayi dai-dai da fitowar dadynsu daga
d'akinsa,
Ganinsa yasa ilham fad'uwa 'kasa kan kafet d'in
dake shimfid'e tsakiyar falon tana kuka "wayyo
Allah nashiga ukku dady ka taimakeni....
Da sauri yazo yakamata ya d'agota sannan ya
rungumeta jikinsa yana tambayarta "lafiya ilham
waye yata6a min ke,?
Cikin muryar kuka da shagwa6a take magana
"momy ce wai dole sai naje school nikuma nace
bazaniba.
Haba ilhama danme bazaki school ba ga
'kannenki sun shirya suna jiranki,
'Kara shagwa6ewa tayi tare da 'Kara narkewa
jikin dad d'inta tace "ni bazaniba.
Cike daso da 'kauna dady ke rarrashinta yace
"shikenan tunda baki zuwa je d'akinki ki kwanta
ki huta, kukuma Hassan da hussaina kuje driver
ya kaiku.
Yaran sukace "dady meyasa yau bazaka kaimu da
kanka ba? Yace "saboda yayarku bazataba, dama
saboda ita nake kaiku....
Yaran suka tafi suna turo baki, duk da suna yara
basu son abinda dady yake masu, 'kiri-'kiri yake
nuna yafison yayarsu akansu.
Cikin takaici Momy ta kalli dady tace "wallahi
karage tsananin son da kake nunama ilham,
saboda duniyar nan batada tabbas, kaso naka
duniya ta 'kishi, ka'ki naka duniya tasoshi,...
Cike da jin haushin momy dady yafita yabar
gidan, dan bayason jin maganar yarage nuna
soyayya ga ilham, kullum fatanshi Allah 'kara
ninka mashi son dayake mata a cikin zuciyarshi.
Cike da takaici momy ta nufi d'akinta, a zuciyarta
tana cewa *Hmm yau naci sa'a ba'a rufeni da
fad'a ba*
Dan some time duk randa tayima ilham fad'a
itama ranar sai ranta ya 6aci...
love u all
Zee Elkaseem
YARINYAR BABA
[01:18 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
YARINYAR
BABA
Written & Edited
By Zee Mmn Khady
*```Just a short story```*
*Page* 11-20
Ilham kuwa tana shiga d'akinta kan gado ta fad'a
ta jawo wayarta 'kirar iPhone6 tashiga danne-
danne, kusan kullum haka take batada wani ayki
daga karatun novel's sai games a waya, kuma a
haka dadynta ya d'aure mata gindi yahana Momy
ta tsawata mata, acewarshi Momy tabarta ta
huta tunda itama Momyn ba wanda yahanata ta
huta, tunda gidansu cike yake damasu yimasu
hidima kome yaimasu ake hatta da sharar d'akin
dasuke kwana akwai meyi.
Haka ilham tayita game a waya data gaji ta ajiye
ta d'auko wani English novel tacigaba da
karantawa, kusan awa biyu tana karatu, saida taji
idanunta na zafi sannan ta tashi ta kashe fankar
daketa faman juyawa tana ba d'akin iska, Ac ta
kunna lokaci guda d'akin yad'au sanyi takoma
tabi lafiyar gado, bacci me dad'i yayi awon gaba
da ita.
Kusan awa ukku tana bacci, ba sallah ba salati,
wannnan shine baccin asara, sai bayan sallar
la'asar sannan ta tashi mi'ka tayi tare dayin wata
uwar hamma, sannan ta fita falo, zama tayi kan
dining sannan ta 'kwalama Ameeno kira,
"Ameenoo.... Da gudu tazo har tana tuntu6e
kad'an yarage yafad'i tace gani, cike da isa da
gadara ilham take magana, "maza ki kawomin
abincina, da sauri Ameeno ta amsa da "to
,sannan tanufi kitchen jiki na 'kyarma, Ameeno
itace yarinyar dakema ilham hidima, wacce da
kad'an ilham d'in ta girmemata, dan yanzu lham
bata wuce shekara sha tara ba yayinda Ameeno
takeda shekaru sha shida zuwa sha bakwai,.
Haka Ameeno takawo abincin tajera gaban ilham
sannan tanufi pridge ta d'auko mata lemu da
ruwa, saida ta tabbatar tagama had'ama ilham
duk wani abu dazata bu'kata sannan takoma
d'akinsu na 'yan aiki, saratu meyima su Hassan
da hussaina hidima ta kalleta tace "hmm 'yar
mulkin taki tatashi kenan, naga sai hidima kike
tun d'azu, Ameeno tace kedai bari wallahi bacin
Albashin da ake bani yanada tsoka da tuni nayi
ritaya da aikin waccan 'yar izgilin.
Inna jummai dake zaune tana jin duk firarsu
wacce itakuma itace me aikin Momy, a gidan
dady ne kawai beda me aiki dan momy tahana
tace itace zatari'ka yimashi kome, hatta da girki
indai name gidanne ita ke Shig kitchen tayi
dakanta.
Inna jummai tace "Hmm aini narasa halin wannan
yarinya, wallahi Albasa batayi halin ruwaba,
iyayenta mutanen kirki basuda wula'kanci, amma
ita sai ahankali.
Haka 'yan aikin suka ri'ka tattauna matsalolinsu,
da kokawa akan yanda ilham ke wulakantasu,
hatta inna jummai wacce a girme ta girmi uwarta
amma bata ganinta da gashin arzi'ki...
Love u all
Zee Elkaseem
YARINYAR BABA
[01:26 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
YARINYAR
BABA
written & Edited
By Zee Mmn Khady
*```Just a short story```*
*Page* 21-30
Ilham na kammala abinda take d'akinta tanufa
toilet tafd'a kai tsaye ta she'ka uban wanka, tana
fitowa taje gaban dressing mirror tafara
d'and'asa kwalliya saida tagama sannnan tanufi
wadrope d'inta wacce ke sha'ke da kaya ta tsaya
tana tunanin wane zata Sanya, zuwa can ta
hango wasu riga da wando English wear's shi ta
d'auko haka ta sanya wando wanda yayi masifar
d'ameta domin irin pencil d'innanne , sannan ta
d'auko wata riga wacce zamu iya kiranta akwai
ya babu, dan rigar purple colour ce tanada
kwalliyar fari agabanta sai akayi ado da purple
d'in duwastu aka rubuta *TOUCH ME* haka tasa
rigar wacce ko hannuwan kirki batadasu
gashinnan na kanta yasha gara ta d'aureshi ya
zubu har kan kafad'unta.
Ba 'karamin kyau ilham tayiba kamar wata
baturiya, dan kusanma tafi turawan kyau dan
ilham kya'kkyawace ajin farko, farace me madai-
daicin tsayi, tanada shafe me kyau, ga dogon
hanci manyan idanuwa sai d'an 'karamin baki.
Bayan tagama shiri saida ta kalli kanta a madubi
ko ita tasan tayi masifar kyau, sannan tajawo
takalminta kalar purple me matsakaicin tudu ta
Sanya, wani d'an yalolon gyale ta yafa a kanta
wanda zamu iya kira akwai ya babu, dan kusan
beda wani qmfani.
Haka tafito daga d'akinta tana taku ahnkali kamar
wacce ke tausayin 'kasa.
Falo ta iske momynta, kallonta kawai tayi sannan
tanufi 'Kofa tace Momy zanje Unguwa, Momy
bata tanka mataba saida takai bakin 'kofa zata
fita taji muryar momy tana magana cikin d'aga
murya...
"Ilham kada ki kuskura kibar gidannan, cak ta
tsaya dan duk abinta tana shakkar momynta,
shiyasa tafison idan zatayi abu yakasance
dadynta nanan, dan idan yana kusa momy bata
Isa ta taka mata burkiba.
Muryar momyce ta dawo da ita Daga duniyar
tunanin data Lula,
"Wallahi bazaki fita a hakaba kamar d'iyar kafirai,
wai ilham kinada hankali kuwa?.....
Tsaye tayi bakin 'kofar batada niyyar motsawa,
ringing d'in wayarta yasa ta motsa ta fiddo wayar
Daga side bag d'inta, tana dubawa sunan
'kawarta tagani Leena, saboda haka da sauri ta
danna OK dan tasan tare suka tsara tafiyar,
sannan ta kara a kunnenta........