Sashe 2
Yarinyar Baba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
YARINYAR BABA
[01:49 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
Written & Edited
By Zee Mmn Khady
Just a short story
*Page* 31-40
hellow Leena kin isone, a d'ayan 6anagaren
Leena tace "kefa nake jira ina a mota bakin get
d'in gidanku kinsan su big boy basu san westing
time, ilham tace "na dad'e da sanin haka gani
nan fitowa yanzu, tafad'a tana niyyar ficewa
daga falon.
Jitayi an shaqota an d'auketa da wani lafiyayyen
mari wanda saida taga wani duhu ya gifta mata,
Momy ce ke cika tana batsewa tace "wallahi
ilham bazaki fita a hakaba, kodai ki canja shiga
kokuma ba inda zaki, ko ubanki daya d'aure maki
gindi kina abinda kikaga dama nasan baze barki
kifita a hakaba, kamar ba jinin musulmi ba.
Ilham kuwa dafe kunci tayi tana zubar da wasu
zafafan hawaye, da gudu tanufi d'akinta kan
gado tafad'a tana sharar hawaye, hankalinta be
'kara tashiba saida taduba madubi taga sawun
yatsun Momy guda biyar kwance a kumatunta.
Gashi tariga ta 'kwallafa rai ga zuwa birthday d'in
class mate d'insu akeyi kuma itace best friend
d'insa tare ma zasu yanka cake, to idan batayi
wannan shigar ba wace shiga momy keso tayi,
sotake tasaka atamfa ko less idan taje a
d'auketa bush girl, wasu zafafan hawaye suka
'kara zubowa a fuskarta tasa hannu ta goge.
Wayarta tashiga 'kara alamar 'kira na shigowa,
kobata dubaba tasan Leena ce dan tasan tana
Bakin get tana jiran fitowarta su wuce.
Bata ko kalli inda wayar takeba har tayi ringing
ta tsinke, kira ya 'kara shigowa karo na biyu,
sannan tasa hannu ta d'auka ta danna 'ok'
sannan takara a kunne cikin muryar kuka take
Sanar da Leena abinda Momy tayimata, wani irin
haushin momy yakama Leena, shiyasama koda
tazo bata shiga gidanba dan tasan data ganta da
ahigar dake jikinta yanzu tafara yimata wata
nasiha marar kai, wacce idan zata shekara tanayi
bazatayi amfani da itaba.
Leena tace "kiyi ha'kuri kitashi ki saka wasu
kayan saiki sako wannan a jaka idan mukaje can
saiki canja,
Haka kuwa akayi wata jallabiya me adon
duwatsu ilham ta saka sannan tayi rolling da
gyalen jallabiyar wancan kayan kuma ta zubasu a
site bag d'inta, sannan ta d'an gyara face d'inta
tafito, bata ko kalli inda Momy takeba tasa kai
tafice, cike da takaici Momy tace "Allah dai ya
shirya.
Dan duk abinda ilham keyi dadyntane yake bata
go a head, yanzuma wannan abin datayima ilham
d'in dayana gidan da sai rayuka sun 6aci, dan
Momy tarasa wane irin so yakema ilham, momy
ta girgiza kai tace addu'a kawai zan dage dan
Al'amarin ilham da dadynta sai du'a'i......
Love u all
Zee Elkaseem
Yarinyar Baba
[04:38 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page*41-50
suna Isa gidan da za'ayi birthday d'in sukayi
parking motor d'insu sannan suka fito, shigar da
Leena tayi bazaka ta6a cewa tanajin yaren
Hausa ba.
tun 'kofar gida sukejiyo sautin kid'a na tashi jikin
ilham har tsuma yake dajin tashin kid'an,
A cikin gidan kuwa duk wanda yakamata ya
halacci birthday din ya halarta mutum biyu kawai
ake jira ilham da leena, in ran Hakeem yayi dubu
ya 6aci sai cika yake yana batsewa gashi sai
kiran wayarta yakeyi taki d'agawa, Hakeem ya
kalli big boy yace "gskiya ilham bata kyautamin
ba, ace duk taron nan ita kawai ake jira......
Big boy yace "nima inata try no Leena ya'ki
Shiga......
Kafin yarufe baki yaga shigowarsu da sauri
yataso ranshi 6ace yace haba ilham tun d'azu
ake jiranki amma sai yanzu kikazo, kuma ji.....ji
dan Allah wata shiga da kikayi miye wannan?
Yafad'a yana nuna kayan jikinta.
Tace sorry my wlh Momy ce tayi west time
d'inmu ka duba kaga face dina, yakai dubanshi
ga fuskarta yaga sawun yatsu biyar kwance
akumatunta take yaji tausayinta yakamashi yace
sorry my dear, Yakama hannunta suka nufi wani
d'aki a can ta canja kayan jikinta zuwa Wanda ta
taho dasu a jaka, Hakeem yashiga rarrashinta
har yasamu ta saki ranta, yayi murmushi yace
yauwa my dear ga wannan ki saka a bakinki
sweet ya mi'ka mata ba musu ta kar6a ta 6are
ta jefa a bakinta, shima wani ya 6are yasa a
baki.
Ilham kuwa tunda tasha wannan sweet d'in da
hakeem yabata sai taji duk wani 'kunci da
damuwa da 6acin ran da Momy tasata duk sun
gushe.
Sun shiga gun birthday d'in mutane na zazzaune,
suma sun samu guri zun zauna sannan aka fara
gabatar da shagalin, ga kida sai tashi yake, ilham
da Hakeem suka yanka cake mutanen gurin suka
d'auki tafi, Hakeem ya yanko yasmata a baki,
itama haka tayimashi,
Bayan wannan aka shiga shagali anata ciye-ciye
da lashe-lashe, bayan angama kowa yakama
harkar gabanshi wasu sun shiga fagen rawa wasu
kuma sun kama friend d'insu sunata fira,
A da duk inda ilham taje magrib nayi idan
hankalinta yayi dubu tashi yake, kuma kome take
saita koma gida, amma yau sai taji duk wannan
tsoron yafita daga zuciyarta, soyayya sosai
sukasha a ranar itada Hakeem, Leena kuma
itada big boy,
kada kuyi mamaki idan nacemaku duka gurin
birthday d'in ba wanda ya haurama shekara
ishirin, dan duk class mate d'insu ilham d'inne.
Haka sukayita bad'ala tsakanin mata da mazan
gurin, sune basu tashi birthday d'inba sai karfe
sha biyu da Minti ashirin da biyar na dare.
Hankalin ilham yayi matu'kar tashi lokacin data
lura da daren datayi bata koma gidaba, cikin
rud'ewa tafara magana "dan Allah Hakeem ka
maidani gida wallahi nasan yau sai Momy ta
6atamun rai, Hakeem yayi murmushi yace kada
ki damu babyna nina gayamaki yau Momy bazata
maki fad'aba, dama nasan bakida matsala da
dady, itadai hankalinta tashe yake tace nidai
mutafi, yace "to muje, ilham ta kalli Leena wacce
ke kwance kan cinyar big boy, yanata latsata
bako kunya, tace "Leena nizan wuce kedai nasan
ba yanzuba, Leena ta d'ago da rikitattun idanunta
wad'anda suka canja launi saboda tsabar jaraba
tace "ni gaskiya ba yanzuba sai naga abinda
yaturema buzu nad'i.
Cikin minti sha biyar Hakeem ya sauke ilham
'kofar gida, kwankwasawa tayi megadi ya bud'e
mata ta wuce, zaune ta taradda Momy da dady a
falo da Alama dawowarta suke jira,
Ganinsu zaune yasa gabanta yayi mummunar
fad'uwa sai yanzu ta tuna da kayan jikinta
Wanda Momy tahanata fita dasune......
Love u all
Zee Elkaseem
YARINYAR BABA
[04:42 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 51-60
ilham tayi matu'kar mamaki yanda momynta ta
tarbeta da fara'a ta taso tana cewa "ilham sai
yanzu kika dawo kinsa munata jiranki dadynkima
yakasa runtsawa saboda rashin ganinki, jiki na
'kyarma ilham tace "wallahi Momy abubuwane
sukayi yawa a gun birthday kuma kinsan nice
best friend d'in Hakeem dole kome dani za'ayishi
yanzuma tahowa nayi badan angamaba kawai
saboda ina tunanin kada kiyimin fad'a.
Sai lokacin dady yasa baki yace "ba damuwa
ilham _*YARINYAR BABA*_ sunanda yake kiranta
dashikenan "jeki ki kwanta ki huta, cike da
mamaki ilham tanufi d'akinta a zuciyarta tana
cewa _{yau meya faru da Momy hartakemun
magana me taushi haka, Wanda nasan duk
lokacin danayi ba dai-daiba ba wanda ya Isa
yahana tayimin fad'a idanma duka yakama ta
dokeni}_
Momy kuwa binta tayi da kallo tanason yimata
fad'a amma data kalleta sai taji wani Abu ya
dakar mata zuciya bakinta yayi nauyi takasa
furta mata wata kalma me zafi.
Tana shiga d'akinta ta cire kayan jikinta ta d'aura
wani d'an 'karamin towel tafad'a toilet ta ahe'ka
wanka sannan tafito tashafe jikinta da wani
lafiyayyen lotion me dad'in 'kamshi, sannan
tasaka kayan bacci tabi lafiyar gado ba sallah ba
salati, barantana tayi addu'a yayin kwanciya
bacci.
Kullum idan ilham zata kwanta sai momynta
tashigo d'akinta ta tambayeta tayi sallah idan
batayiba nan zata tasata gaba tayi sannan tasata
tayi addu'oi ta kwanta, amma yau Momy tana
tunkaro d'akin ilham sai taji kamar ana ri'ke mata
'kafa ana maida ita baya, sai taji bata son zuwa
d'akin ilham d'in komawa tayi d'akinta ta kwanta
wani irin bacci me nauyin gaske yayi awon gaba
da ita.
Ilham kuwa koda ta kwanta sai taji kanta
yayimata wani irin nauyi, sai juyi take kan gado
zuwa can sai taga d'akin na juyamata, lokaci
guda wani irin haya'ki ya turnu'ke d'akin wanda
idan da mutum ze shiga ciki baze iya ganin
abinda ke gabanshiba, ganin haka yasa ilham
rud'ewa wani matsanancin tsoro yashiga cikin
zuciyarta duk illahirin jikinta 'kyarma yake,
Kusan mintuna sha biyar d'akin na juyamata
sannan kome ya lafa yakoma yanda yake jitayi
anyi sama da ita, tafiya akacigaba dayi da ita
cikin sararin samaniya batare dataga Wanda ke
tafiya da itaba.......