Sashe 4
Yar Tsakar Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hayaniyar su ce ta balle nan kika ga yara da iyayen su sun taso sun fi talatin ,babu mai ba Ikilima Gaskiya sai dai bakin ta da Kwace ta ,don ita akwai iya sababi tasan ya ake tijara bata da hakuri ko kadan ,sai dai akwai ta da tausayi . Cike da jin takaicin ta Baba Zuwai tace " Shegiya yar banza akan Yar zina ce zaki kama Dukan jinin ki ?. Gaskiya baki da Ɗabi'a Ikilima . Mama Ko me zaku ce sai dai kuce , ba zan bari ina gani a zalunci karamar yarinya ba , Idan Zulai jina ce itama Amrah jina ce , Baba ne ya haife ta . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una tabbas akwai Hauka a kwakwalwar ki Ikilima . Cewan Zulai tana Kallon Ikilima ido cikin ido . Murmushi Ikilima tayi na tijara kana tace " ba zaki fahimci akwai Hauka a kaina ba Wallahi sai ranan da kika yi kuskuren kara taɓa Amrah ,mugaye Azzalumai .
Fito Sarari ki zage mu , yar na isa..! Jummai tayi maganan tana kallon Ikilima , Wanda baba Zuwai ta amshe tana cewa " To ai Shikenan ku barta , Ikilima daga yau ki zama uwan ta uban ta don Allah kinji, idan zaki koma makarantar kwanan ki tafi da ita tun da jinin ki ce . Daukar Amrah Ikilima tayi tana Wuce su ba tare da ta kuma tanka masu ba. Ɗakin baba Zuwai ta nufa da ita tana shiga ne tayi ido biyu Da fida na tara cike da koko . Kallon Amrah tayi Wanda a yanzu tayi shiru tayi lakwam a hannun ta . Amrah Zaki sha koko ko na saya Miki Awara .? Tayi maganan tana kallon agogon dakin da ke nuna mata karfe biyu da rabi na Rana . Da ido Amrah tabi ta don bata magana ba ta iya ba sam . Durkusawa tayi tana ɗaukar Kokon tare da zama gyefen tabarman ɗakin tana fara ba Amrah kokon wanda cikin sauri yarinyar ke masa shan Ruwa saboda Yunwa . Sai da ta kusa shanye babban fidan sannan ta dakata tana kwantawa a jikin Ikilima , Ƙwallah ne ya ciko idanun Ikilima tana kallon Amrah tare da tuno da mahaifin su . Muskutawa tayi don debo ruwa ta bata ko zata sha ,amma nan taga yarinya ta bungure Alamun barci ya dauke ta . Wannan yasa Ikilima samun zani tana Goya ta a gadon bayan ta .
Caɓe Baki baba Zuwai tayi wacce take shigowa kamin tace " Don Allah Ikilima dauke ta ki tafi Dakin kwanan ki ku tafi can , wallahi kuma indai kin zabi haka ne a cikin gidan nan to zaki wahala . Juyawa Ikilima tayi a hankali tana faɗin " Mama Wannan Fa Marainiya ce duk gidan babu Maraya kaman ta , Baba ya rasu .....ke da Allah yi mun shiru, Ahir din ki.! Daina alakanta mun miji da yar zina , fita kar raina ya ɓaci . ? Humm Numfasawa Ikilima tayi tana ficewa da Amrah.
A wannan Rana Amrah kukan rashin uwa kadan tayi Ikilima itace sayan mata Wara itace biscuit komai da yaro ke bukata kaman ta take bata , haka wuraren La'asar ta fita da ita tare da shuga gidan kawanta anan makotan su . Bata dawo Gida ba sai bayan Magriba don ko da aka kawo mata Tuwon dare ,cewa tayi ta koshi don taci a gidan Kawanta Hajara . Don acan ta cika cikin ta dana Amrah . Ganin Ana juya da Tuwon ne tace ke kawo mun nan da safe Maci da Amrah . Amsan Tuwon tayi tana Rufewa gyefe tare da dawowa kan Katifan ta tana rungume Amrah wacce tayi nisa a barcin ta. To yanzu Idan na koma makaranta wa zai kula da Amrah , ina jin tausayin yarinyar nan ,don kuwa Su Matan Gidan basa da imani ka kadan . Haska fuskar Amrah tayi da fitilan Nokia din ta kamin tace " Tabbas akwai Wani abu a ƙasa ,amma Amrah ba da kowa tayi kama ba Fache Baban mu , manyan idanun ta yanayin shatin Giranta duk wanda yasan Baba ya kuma ga Amrah yasan jinin sa ce...! Dole zan Haƙura da makaranta ko na shekara daya ne Don na bata kula ta kara Wayau daga bisani sai na tafi .
A haka yau da gobe babu lokaci na tafiya kullum babu dadi Rayuwar Amrah a cikin gidan . Gaba daya Ikilima ta kashe karatun ta na tsawon shekaru biyu , baba Adamu shine cin Amra da shan ta ..kulawan ta kuwa Ikilima ce . A haka har Amrah ta kai shekaru uku a cikin gidan . A wannan lokacin ne Ikilima ta koma makaranta , don duk wani maraici Amrah ta gama sanin shi . Yarinya ce hakurarriya bata da magana sam . Abun dake bata Ran Ikilima shine rashin zuwan Amrah Makaranta tayi magana har ta gaji . A haka Amrah takai shekaru Bakwai babu Makarantar boko sai na Allo da take zuwa . A dai dai Wannan lokacin Wahalar duniya a cikin gidan Amrah keyi ,itace tallahn Gyaɗa da Safe zuwa karfe biyu da La'asar ta tafi Tallahn Awara . Sam bata hutawa haka Abinci sai ta kwana bata ci ba .
Amratu Amratu...!
Muryar Baba Adamu ya katse Amrah dake Wanke-wanken kwanukan Gidan nan baki daya , rayuka sun fi tamanin . Na'am Baba ." Tayi maganan cike da Sanyayyar Muryar ta na yara. Murmushi Baba Adamu yayi yana Fiddo da takarda yana cewa " Amratu na kin ga wannan Admission ne na Makarantar masu kudin can Sun dauki nauyin karatun marayu 10 a wannan shekaran sunan ki ya fito Amratu, zaki fara daga Aji biyu zuwa har aji shida .duka a kyauta . Yayyyyy....! Baba Ina so Baba nimm....Don Allah rufe mun baki ,wani makaranta za'a saki ? ,Tallahn gyaɗan Safen Wa zai mun .? Baba Zuwai tayi maganan tana fiddo da idanun ta na masifa waje . Jummai ne tace " Ni kuma Tallahn Waran La'asar din fa.? .
Shiru Amrah tayi yayin da Baba Adamu yace " Amrah a gobe zata fara zuwa makaranta kunga ledar nan uniform din ta ne ciki da komai da komai aka bata su hukumar makarantar . Tallahn safe ku nemi mai yi maku Tallahn rana idan ta dawo tayi . Jeki tafi ki Cigaba da aikin ki . Summ² Amrah ta wuce tana dukufa tare da Cigaba da Wanke-wanken . Da ido suka bi Baba Adamu har ya shige sasan shi . Tabdijam yanzu makarantar ya'yan masu kudi zai kaita ,mu namu yaran suna na gomnati?? . Larai tayi maganan yayin da Zuwai tace " Humm Fifiko ke abun bari ta fara zuwa zan ci uban ta ne , karatun wallahi ba zata yi ba . Yanda ta shiga Batasan komai ba haka zata fito Batasan komai ba. Shewa Jummai tasa ka da sauran mutanen tsakar gidan suna fadin " Dakyau Baba Zuwai .!
**
Safiyar litini Amrah murna take yi sosai sam ta manta da ɓacin ran cikin gidan . Sanye take cikin uniform rigar fari da Sanyi akai . Skirt ne iya gwiwa sai takalmin makarantar babu arzikin Safa bare jakan makaranta , Don Littafai biyu baba Adamu ya saya mata wanda ta zuba su a leda . Hijabin makarantar iya Kafaɗa ne wasu ma basa saka Hijabin sai hula musamman su yara . Saurin fita daga Taskar Gidan tayi don gudun Tsiya da zata sha . A wajen Gidan can nesa ta tsaya tana Jirar fitowar Baba Adamu . A hankali take bin titin layin nasu da kallo tare da kallon ƙaton gidan dake gaban ta , benen saman gidan take kallo , dai dai ana buɗe Gate ɗin gidan.
Laa kayan mu iri ɗaya ...! Tayi maganan a zuciyar ta tare da bin Dan Saurayin da ya fito daga Gidan sanye cikin uniform irin nata Amma shi da dogon Hannu ne alamu SS yake . Kallon Driver n shi yayi yana cewa " No yau a keke zan tafi ,ba sai kazo dauka na ba . Sabon keken shi ya hau tare da gyara School bag din shi yana fara Driving ɗin keken wanda daga ji kasan bana kasar nan bane . Ta gaban Amrah yazo yana kokarin wuce ta idanun Nurain ya Sauka akan Ta . Tun daga saman ta har ƙasa ya kare mata kallo idanun sa na dira akan jakar ledar Hannun ta . Nan take ya hau kyakyata dariya har yana sakin kan keken yana kecewa da Wani irin Dariya . Hi student...! Which school are you going now.? . Tsayawa Amrah tayi tana kallon sa sam ta rasa inda ya nufa , don bata ji mai yake cewa ba . Tsayawa yayi yana ɗan yin jimmm tare da kallon kyaƙyƙyawar fuskar ta dai dai tana dago da Lulun idanun ta wanda suka ciko da ƙwallah fuskar ta a dan shagwaɓe alamu tana gab da fashewa da kuka ne . Wow fine girl . Are you in primary section? . Amratu... Amratu...! Muryar Baba Adamu ya katse su inda tayi Saurin juyawa tana kokarin nufa inda Baba Adamu yake . Kallon bayan ta Nurain yayi yana bin uniform din ta da ko guga babu ta fito kaman wata bujiya yana ƙara saka dariya tare da Wuce ta .
Bayan ta karisa inda Baba Adamu yake ne ta kalle shi tana cewa " Baba wannan Shima kayan Makarantar mu iri ɗaya. murmushi baba yayi yana cewa" Eh ai shi anan yake , kin ga gidan mahaifin shi can ,su ya'yan masu kudi ne , Duk girman Gidan nan shi kadai ne a ciki iyayen sa suna Kasar Waje , acan suke rayuwa ,yanda naji wai shi yaron ne ke son yin karatu a nan kasar . Hummmm Kama hannun Baba Adamu tayi cike da Yarinta tace " Baba ya kalle ni yana mun Dariya Kuma yana wani magana banji komai da yace ba . Kallon ta Baba yayi yana cewa " Amratu kenan , Amratu baiwar Allah ...! Hau mu tafi ka kiyi latti . Ɗago ta yayi yana daurata a gaban tsohuwar keken sa yana gungurawa tare da bin gyefen hanya don kaita makarantar............
```Tallah```
Assalamu alaikum jama'a yau gaku ga buxuwa empire