← Book details Ƴar Tsakar Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Ƴar Tsakar Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

12:01pm.
Nigeria Airport
Jirgin Su Nurain ne ya sauka , Wanda tun tsayuwar su yake jin Wani irin sanyi na Ratsa ko ina na zuciyar sa . A hankali yake shaƙar iskar Ƙasar nasa Wanda ya barshi tsawon shekaru goma sha bai dawo ba sai a yau. Lumshe sexxy eyes din sa yayi yana tunano da kyaƙyƙyawar fuskar ta wanda har Abada ba zai taɓa mantawa da shi ba a rayuwar sa. Ɗan murmushi ya saki mai nuni da jin dadin Dawowan sa . Fara sauka yayi daga Stairs din Jirgin data dauko su daga America . Wani irin girma yayi da cikar kamala ,wanda idan ka ganshi sai ka kara kare masa kallo zaka fahimci shine dai Wancen Nurain din ba wani ba . Yanda fatan jikin sa yake ko na wata hadaddiyar macen Albarka luku² tamkar wanda bai taɓa fitowa rana ba . Idanun sa sanye cikin baƙar space ( maganin ido) wanda ya kara daukar Hankalin ƴammatan wurin . Kowa da ya gansa yasan Dawowan Nigerian yau ne . Sanye yake cikin shigar Track suit Mai haske kalon Ruwan samaniya light blue . Yayin da ƙafarsa ke cin boot fari ...a hankali yake saukowa yayin da Gaba ɗaya masu take masa baya (Securities) din sa suka rufa masa . A inda motocin su suke ya tsaya yana kallon Daya daga ciki kamin yace ma drivern ya basa key din moton . Cike da natsuwan nan nasa ga Dan Miskilanci da na gani a fuskar sa wanda a da baya ban san shi dashi ba . Zaku iya tafiya ,zan taho daga baya . Ok sir . Suka yi maganan suna saurin Buɗe masa moton ba tare da sun san inda zashi ba .

**
A hankali take Ware idanun ta Tana kallon Gyefen ta inda taga Wayoyin Zaid da laptop ɗin sa amma baya wurin . Saurin kokarin tashi tayi dai dai tana jin Hannun Mom Cruzita na dakatar da ita tare da cewa " Sannu da Jiki Amrah , Ai ban san baki da lafiya ba , Oga ya faɗa mun yanzu bayan sun gama baki kula da sauran nurses . Kallon Mom Cruzita tayi tana son tambayar ta mene yace mata? Sannan ciwon mene take yi kuma?. Wata Nurse ce dake Gyefe ta kalli Amrah tana cewa " yanzu zamuje kiyi Brush idan kin fito ga Abinci nan da kayan motsa baki Doctor ya aiko Miki dashi . Gyaɗa mata kai tayi a hankali tana Miƙewa don kayan karin ruwan a gyede ta gansu da'alama har sun kare ne an cire su . Kamata Nurse din tayi tana nufa da ita Toilet .
**
Ɓangaren Nurain Kuwa Bulayi yayi tayi amma ya kasa gane Hanyar ko ina , Wanda daga karshe makarantar Jennylyna ya nufa inda suka yi . A dai dai bakin makarantar yayi parking moton shi yana fitowa tare da kallon Gyefen Hanyar wanda ya Bisa babu iyaka . Kallon Wani hanya yayi inda suke yin yanke shi da Amrah duk idan zasu koma gida , a hankali ya furta " Kina Ina Amrah a yanzu.? Kin yi Aure ? ,Ko kin manta dani?. Rufe Murfin Moton yayi yana tsallaka wa bakin Hanyar tare da bin layin nan da ya kasa mance dashi a memory din sa . Bin hanyar yake yi wanda a yanzu yaga yayi faɗa , ga mutane sun yawaita a layin kaman a da wurin ba kaman Daji yake ba . Lumshe idanun sa yayi yana tuno da rana na farko da suka fara biyo layin , yana dauke da ita a keken sa . Realy Miss You Amrah ... Idanun sa ne suka hau Rawa cikin sauri ya zare Bakar gilashin idanun sa ,. Wannan wurin mai tsiren da suke zama ya gani ,ya koma wani babban Wurin sayar da nama ,an gyara Wurin har da yi masa Adon fitilu. Saurin ƙarikawa yayi Wurin wanda a yanzu ma babu mai sayar da naman ,da'alama har yanzu da yammaci suke fitowa . Rumfan ya shiga yana tsayawa yana kallon Gyefen sa tare da tuno maganan Amrah da take kuka tana cewa " Shikenan Kaja mun na tsime , da kayana zan Kwana Kuma Baba Zuwai zata bugeni...." . Ƙaran Kiran Wayar sa yasa shi daukar kiran a sanyaye musamman Ganin kiran Mom Sa'adah ce . Nurain mene ya faru baka biyo Excouts din naka ba.? . Cike da danne damuwar sa yace " Mom na tsaya dubawa ne ko zan gane gidan su Amrah amma har yanzu Ban gane ba . Shiru Mommy tayi tana kallon Gyefen ta inda Dad da Su Naana ke zaune . Kara danna wayar tayi a saman kunnen ta yanda ba zasu ji me yake fadi ba tana kwantar da muryar ta cike da rarrashin da ta saba yi masa a kullum tace " Ka dawo Gida yanzu kaji Nurain?. Ok mom . Murmushi tayi tana Datse kiran tare da kallon Su Naana tana cewa" Yanzu zai Dawo. Cike da nuna farin ciki Nusaiba tace " Yauwa Mommy ina Cook dinnan ta rannan ita ya kamata tayi ma my boo Duk abun da yake buƙata ,Cox ta iya komai gaskiya, ka mata ma yayi ta zama masa personal maid din shi mai kula da shi da koman sa .

Wani irin bugawa Ƙirjin Nusaiba yayi cikin sauri ta katse Nusaiba tana cewa " Aa duk Ma'aikatan Gidan nan sai itane zuwan yanzu zata yi masa.? . Kamin Nusaiba tayi magana Mommy cike da kashe zancen tace " Ai ita mai Girkin dare ne , ba anan take zama ba ,kullum zuwa take . To ai Mom kudi ake biyan ta . Yanzu dole ta kasance 24hrs a cikin gidan nan . Idan ke kina buƙatan ta to ai ba lallai Shi Nurain yana bukatar ta ba . Kin san baya ma Son takura shi , ko fa breakfast baya yi a Dinning Falon sa ake kai masa .

Kallon Naana Nusaiba tayi tana cewa " To ai shiyasa nace Miki ta zama personal maid din sa , ta rinka masa aiki shi kadai . Amma kina ji bari ya dawo idan ya nuna yana bukatar ta zama masa hakan ai kin san shi dai kaifi daya ne sai dai kiyi Haƙuri . Murmushi Mommy tayi tana dan sa yar dariya kana tace ' Kudai ba'a iya maku .
Mikewa Nusaiba tayi tana nufar ina Hadiza suke don ta sanar masu a kira Amrah don yau ita zatayi entertaining din Nurain da yake dawowa .
**
Sosai Amrah taci Abincin wannan yasata jin karfi a jikin ta . Sai daga nan ne kuma ta fara dawowa hayyacin ta , jikin ta take kallo Ganin an sauya mata kayan jikin ta zuwa Wata doguwar riga bakar Abaya . A sanyaye ta kalli su Mom Cruzita da har a lokacin take kanta tana cewa " Mom karfe nawa yanzu .? Mom Cruzita ce ta bata Amsa da " 2:30pm . Waro idanun ta tayi Waje da sauri ta miƙe tana kokarin ficewa ne Zaid ya shigo . Kallon sa tayi tana dan yin ƙasa da idanun ta a hankali ta furta " Na gode da kulawa da kayi dani . Murmushi taji yayi mai sauti kana yace " Wannan ai dama wajibi na ne . Zan tafi ina zuwa gidan Wani Aiki yanzu lokaci ya ƙure na gode . Kamin yayi mata magana tuni ta fice tana nufar Ɓangaren su ta dauki Hijab. Don tsoron abin da zai kai ya kawo take ,kar a koreta a gidan Aikin nata .
**
Lekowa Nusaiba tayi a fusace take fadin Wai ina Yarinyar ne har yanzu bata zo ba.? Eh Hajiya amma .... Assalamu alaikum . Ohh Gata nan ma . Mtswww Dan tsaki Nusaiba tayi kana tace " Ke kin ɗauki Aikin ki kuwa da muhimmanci? . Kiyi maza yanzu ki haɗa ma Yaya na kunun Aya irin wanda kikayi mana. Kece Zakiyi entertaining din sa . Wani irin danmmm Amrah taji Kirjin ta ya yanke ya fadi , Tambayan kan ta take wani yayan nata ? Badai Nurain ba .? Ficewa Nusaiba tayi yayin da Hadiza take fadin maza muje kitchen mu fara Aikin . Don kuwa ya dawo kin san baya cin abinci a Dinning sai dai a falon sa . Mutum ne yanda naji labari Miskili baya magana sai rashin mutunci baya da Kirki sam . Humm Numfasawa Amrah tayi a zuciyar ta tana cewa " A'a ba Noory bane , Shi Noory yana da Fara'a da Kirki sosai .

Mintuna Ashirin suka ɗiba suna shirye shirye . Kana su nufo Dinning ita da Hadiza . Bin ta da Kallo Naana tayi tana ganin Amrah cikin Shigar Yan Aikin gidan . Wani irin murmushi tayi duk da Zuciyar ta yaki natsuwa, amma tana da yakinin Nurain ya manta da Amrah . Cikin Sauri Mom ke fadin " Ke fine baby girl din nan zaki kai masa , sai ki tsaya idan ya kammala ki fito da komai . Tom Hajiya . Amrah tayi maganan tana ɗaukar Wani basket da suke dauke da kayan marmari da motsa baki . Cike da dan karsashi ta nufi falon da ake nuna mata yake . Ganin ta shige yasa Naana Saurin miƙewa tana kallon Mommy tare da fadin " Momy Wannan fa yarinyar itace Amrahn da Kika sani.! Kallon Ta Mom tayi cike da Rashin fahimta kamin tace " Wacce Amrahn kenan?. Idanun Naana sun sauya na tsaban Ƙiyayyar Amrah cikin dan daga murya mai nuni da takaici tace " Amrah wacce Daddy ya bar Da Nurain kasar nan saboda ita ,itace fa a yanzu kuka aika masa a matsayin Mai kula da bangaren sa cin sa da kuma shan sa. Ba Mom kadai ne ta dauke Wuta ba har Nusaiba mutuwar zaune tayi .....!
Chapter 16 · 0% Book details