Sashe 11
Ƴar Tsakar Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Me hoto ta gani a tsakiyar falon , yayin da Nurain ta kalle ta yana cewa " Amrah today I'm + 1 . Wow Happy birthday Nurry . Murmushi yayi yana rike hannun ta tare da furta " Thank you Amrah . Cake din da Mama Nanny ta kawo masu ne Amrah ta kallah kamin ta tsinkayi Muryar sa yana cewa " Mama Shigo Mai Photograph yana jira a dauke mu duka . Rungume Nurain Amrah tayi a tare suka dau hoton wanda yawan su yafi talatin fiye da Ashirin suna tare daga ita sai shi suka yi shi . A wannan rana sun wuni cikin nishaɗi har wuraren yammaci . A farfajiyar Gidan ne ta kalli Nurain tana cewa " Nurry ina keken ka yake.? Juyawa Nurain yayi yana kallon Can Gyefen Garden kamin yace muje can ki gani . Kai tsaye suka nufa Garden din Nurain na fiddo da keken sa Taho ki hau . Yayi maganan yana kallon Amrah don yasan Abun da take so kenan . Kallon sa Amrah ta tana masa dariya tare da cewa " yeeee tana saurin hayewa ta gaban shi yana fara juyi da ita a keken suna kaiwa da komowa a tare . Su kan su basu san mintunan da suka ɗiba a hakan Amrah ..... Taji Muryar sa ya kira sunan ta. Ɗaga idanun ta Tayi tana kallon sa fuskar ta cikin matsanancin fara'a ,Kiyi Haƙuri kinji..." Uhmm mene kayi mun Noory.? Murmushi taga yayi mata yana Girgiza kan sa tare da cewa " ba komai . Kallon sa Tayi tana jin akwai wani Abu kamin tayi masa magana Muryar Mama Nanny ya katse su tana faɗin " Dare fa ya fara yi , Amrah ta tafi Gida haka . Sauka Amrah tayi daga keken tana kallon Sa tare da daga masa hannu tana faɗin " Sai da safe. Ba zan jira ka ba gobe makaranta xan tafi ,idan ina jiran ka Zango daya ke wuce ku kullum . Idan kazo school ma haɗu . Juyawa tayi da gudu tana barin Wurin . A hankali Nurain ke sauke Numfashi don ji yake tamkar zuciyar sa zata tarwatse. Idanun sa na fidda Hawaye masu zafi da raɗaɗi .
Kama hannun sa Mama Nanny tayi tana nufar palour dashi . Nurain kayi hakuri Kabi maganan iyayen ka , ko mun daɗewa wata rana zaku hadu da Amrah . Tafiya ba mutuwa bace ba . Mama yanzu ba yanda za'a yi Amrah tabi Ni mu tafi America,ko na roƙi Baba Adamu ?. Cikin Sauri Mama Nanny tace " A'a Ba zai yiwu ba ,ko itama Amrah ba zata bika ba . Rintse idanun sa yayi yana cewa " ki haɗa mun kayan da zan tafi dasu . Gyada masa kai Mama tayi kurum tana gani ya wuce ciki ,a zuciyar ta hamdala take yi daya amince da tafiyar nasa do mun kuwa bakaramun fada ta sha ba a gurin mahaifin sa , a cewan sa tayaya ta bari har Wata mu'amala ta shiga tsakanin sa da yar talaka...?
**
Zama yayi a kasan tiles din yana bin gift din Amrah da sakamakon jarabawar nata da kallo . A hankali ya kankafe yana yo kasa dasu tare don yaba Mama ta sanya masa a jakar tafiyan sa .
Safiyar Alhamis .
Zaune Amrah take a cikin Ajin suna fira da ƙawayen ta . Kaman Ance ta juya idanun ta ya sauka akan Naana dake mata wani irin Dariya . Humm sauke Numfashi tayi a hankali tana Cigaba da Rubutun ta a haka har aka Tashi break . Marian ina zuwa ko zaki rakani Secondary Section . Hahaha....Uban me zakiyi a secondary section din.? Muryar Naana ya katse ta , takowa tayi gaban Amrah tana faɗin " Nasan Wurin Nurain Zaki je ? Shin baki da labarin Nurain ya koma America da zama. ? Kirjin Amrah ne ya buga daaam . Ai ba zaki ƙara ganin Nurain ba ya Miki nisa nisan da ba zaki taba iya cimmasa ba . Kallon Naana Amrah tayi kawai sai ta juya da Gudu tana nufar Section din su . Voting ta tadda Sunayi na sabon Headboy wanda Ganin haka yasa Zuciyar ta kare karyewa . Juyawa tayi tana ware ware tare da kallon Yan Class din nasu . Amrah ...! Taji Muryar saif ya katse ta . Cikin sauri ta Juyo tana kallon saif tare da cewa " Ina Nurry yake ? Don Allah ka faɗa mun yana ina..? .
Kallon Amrah saif yayi cike da daurewar kai yace " A'a bai faɗa Miki zai koma America da zama ba ? , Ai yanzu ma haka jirgin su ya Ɗaga nake tunan.... Kamin ya ƙarike Maganan ta juya da Gudu tana nufar Hanyar Gate . Me Gadi dai yaga yarinya ta felle ne ta gudu wannan yasa shi kiran sunan ta da Ƙarfi Amma ko waiwayowa ba tayi ba . Gudu take yi iya ƙarfin ta wanda sam bata tsaya ba sai a bakin Gate ɗin Gidan su Nurain. Baba mai Gadi ta gani a kofar gidan ,Wannan yasata ƙarisowa cikin haki take fadin " Ina Noory.? . Kallon ta ya tsaya yana yi wanda Ganin irin kallon da yake mata yasa ta fara zubda Hawaye . Da gaske ne kenan ya tafi.? . Girgiza Kai Baba mai Gadi yayi cike da Tausayin Amrah kana yace " Kiyi Haƙuri Amrah , kuskuren naki ne tun farko kin shiga jikin wanda yafi ƙarfin ki , sanadin ki mahaifin sa yasa shi don dole sai ya koma America, Saboda baya son hulda da talaka . Yaji labarin ki , kuma ko da kika ga Nurain a nan layin mahaifiyar sa ce taso hakan ,ba tare da mahaifin sa yasan a cikin talakawa yake zaune ba . A yanzu ina so ki manta da Nurain domin gidan nan ko kin shiga babu kowa cikin ta ya sallami kowa,sannan Nima yanzu ina hada kaya na ne xan koma Garin mu ta buzaye . Karan motocin da Amrah taji ne yasa ta Saurin juyawa tana kallon Wasu irin manyan motaci irin na rusau din nan . Hawayen idanun ta karuwa suka yi . Baba mai Gadi Nurain ya tafi kenan . Amrah kalli kiga wannan motocin sun zo ne don rushe Gidan nan , saboda Mahaifin sa baya son alakar ku Dawowan Nurain ba yanzu ba . Kuma ko ya dawo Nigeria ba lallai ya gane inda kike ba . Saboda rushe gidan nan za'a yi inda ya zauna ma ba zai gane ba . Idan kuwa aka rushe nan da shekaru uku Ba za'a gane komai ba ,bare kuma ya kai ga Shekaru goma . Kiyi Haƙuri ki manta da komai ,ki manta da kin san Nurain .! Ɗauke Wuta tayi tana kasa ce masa komai ya juya yana barin ta anan tsaye don baya da bakin da zai Fahimtar da ita .
A hankali take daga ƙafan ta tare da Nufar can Gyefe tana gani aka fara rushe gidan yayin da bata motsa ba har aka maida wurin flat .zama tayi a bakin hanyar tana wani irin kuka mai ban tausayi da raunana zuciya .
**
Akwana ta a tashi Wahalan nata na karuwa amma a haka take girma ,tana manta komai a rayuwar ta amma ta kasa mantawa da Nurain wanda a yanzu gidan su ya zama Wani karamin kasuwar layin don fili ne aka maida shi na Al'umma ,wannan ya tabbatar mata da cewa " Mahaifin Nurain wani babban ne a Nigeria. A yanzu sun kai Primary 5 inda a yanzu hanya ta biyo don an ce tazo da kuɗin zana jarabawar shiga Js 1 . Sannan scholarship ɗin nata ya ƙare yanzu sai dai ta biya kuɗi idan tana son tafiya Ajin gaba ko ta sauya makaranta . A Tsakar gidan taci karo da Baba Adamu wanda shima a yanzu yana jin jikin sa halin rayuwa kudin ma babu kwatakwata . Sannu da Jiki baba . Yauwa Amratu ,yayi maganan yana kokarin ficewa . Nufar dakin Baba Zuwai tayi sam ta kasa tambayar baba Adamu .
To maza a sauya kaya azo a dauki tallann Awara . Kallon Baba Zuwai tayi kana tace " Tom Baba , Baaba An Koro ni kudin jarabawa Zamiyi exam . Don Allah Baaba ki biya mun ,idan banyi ba ba Zanje Matakin gaba ba .
Wani irin Kallo Baba Zuwai tayi mata kamin tace " Alhamdulillah, Na huta da Wannan shegen karatun naki , Ni asara ta haife Ni na biya Miki kudin makaranta,koda kuwa kudi na zuba mun ai ba zan baki ba . Don haka Shikenan . Daga nan kin gama karatu har Abada kuwa. Wasu irin Zafafan ƙwallah ne suka zubo mata . A hankali take tunawa da maganan Nurain . Ki mun Alƙawari ko dani ko bani Zakiyi karatu . Me kike so ki zama for your future life.? Rintse ido tayi tana tunano da maganan tasu . Ina so na zama babban mutum kaman kai . Dallah dauki Awara ki fita ki zaga mun makota . Saurin daukar Roban awaran tayi tana ficewa daga Dakin . Tun daga nan Amratu bata ƙara karatu ba ta hakura ta aje komai da ya shafi karatu sai Wahala na cikin gidan kawai . Kamin nan kowa yasan ta a ƳAR TSAKAR GIDA.