← Book details Wayafi K'aunata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 7

Sashe 7

Wayafi K'aunata Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Tana cikin tunani taji an banko k'ofar parlon, da sauri ta waiga tana kallon su yadda suke bin parlon da kallo yasa cike da fara'a ta ce "Hajiya ku shigo ina wuni" ta idasa maganar tana kaiwa har k'asa tana gaishe da Hajiya dake binta da hararara da kallon wulak'anci, Halima ce dake cin chingum tana bin ko ina na parlon da kallo tana jefama Munnira wani matsiyacin kallo ta juyo wajan Hajiya tana cewa "dama Hajiya wannan kucakar ce matar My Man ai na zata zanzo na tadda wata uwar mata a yadda kuke ikirarin wai ta mallake sa a hakan", ta idasa maganar tana nuna Munnira, tafawa sukai ita da Nawwara ta ce "hmm kema kin gani dai ya rasa uban mi yake ci tare da wannan tsohowar guzumar matar tasa kullum suna mak'ale da juna" wani irin taku Halima tayi tana matsowa kusa da Munnira tada dake tana kallonsu bak'in ciki ya cika zuciyarta amma ta dake tana son kawar da fushinta, ko kad'an idan ka kalli fuskarta baza ka ce abinda suke fad'a game da ita ya bata haushi ba, Halima dake kallonta cike da tsana da hassada saboda taga ta fita ta ko ina kyanne kyan jiki da diri da komai kawai ta fad'i hakan ne danta bak'anta mata rai sai dai tana kalli fuskarta sai taga sab'anin haka dan kuwa fuskar Munnira wani kalar annuri ma ke fita da kwarjini, ta bud'e baki ta ce "ai daga yanzu a shirya dan ba mutum shi kad'ai keda shi ba, kuma idan banda jaraba ta d'a namiji ina wani abun so da abun mak'alewa a nan", shuru Munnira tayi dan tasan shine alkhairi baza ta so tayi cece kuce a gaban sirikarta ba kuma tun kamin ma ta shigo tsayawa fad'a tana fad'a kamar zubar da mutumci ne da kima.

Shurun da tayi kuwa ba k'aramar shak'a sukai ba ta maida su mahaukata kenan cike da isa Hajiya ta zauna kujera tana d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana nunama Halima gidan ta ce "fatan dai wancan sashin yayi miki idan ma baiyi miki ba, wannan ne yayi miki zata iya kwashe kwamutsanta ta baki waje mai gurin yazo mai tabarma ai dole ya nad'e" wata dariya Halima ta saki ta jin dad'i ta ce "ai Hajiya nafi k'arfin na zauna a inda ta zauna sabon waje yayi min ina ni ina zaunawa inda ta tashi ai nafi k'arfin haka Hajiya tayi zamanta dama bakiga wajan ba duk an maida shi wani iri" Hajiya data gyara zama ta kai dubanta wajan Munnira dake tsaye ko ci kanku bata ce ba, wani banzan kallo ta watsa mata tana cewa "da alama gidanku basu iya tarbar bak'i ba ko?, kinga mutane bazaki basu abin tab'awa ba kin wani tsaya kin tsare mutane da idonki irin na munafukan farko, nazo gidan d'ana amma ko arzik'in ruwa bazan samu nasha ba, saboda baki da mutumci dama marar tarbiyya ce ke", sosai taji maganar Hajiya ta b'ata mata rai amma saita d'an k'ak'aro murmushin k'arfin hali ta ce "a'a Hajiya ba haka bane baku zauna bane na gani, kunata wasu maganganu ne wadda bai shafe ni ba, bari nayi wai ku gama idan kuka zauna saina gabatar muku da abun motsa baki" cike da mamaki suke dubanta au yanzu duk maganar nan da suka yab'a mata bata dameta ba, kam uban nan kayyasa kai rik'e baki Nawwara tayi, Halima kuwa sakin baki tayi tana duban Munnira dake shigewa kitchen, harta kawo masu ruwa da lemo suna tsaye cike da mamakinta.

Hajiya dake zaune ta cika tayi fam ai gani take kamar gayamata magana Munnira tayi, ai kuwa Halima data harbo jirgin Hajiya ta bud'e baki domin k'ara zuga tana d'aukar robar ruwa ta zuk'a tana watsa ma Munnira shi a fuska, ta ce "ai wannan maganar da tayi Hajiya gaya miki magana kawai tayi wallahi" runtse idonta Munnira tayi tana jin ciwon watsa mata ruwa da Halima tayi, Halima dake kallonta ta sake cewa "ke har kina da abunda zaki bamu mu ci?, saura muma a gama damu komi kike nufi?", Munnira dake shirrin yin magana suka ji wani irin k'arar mari tasssss tassss mai azabar k'arfe k'arar mari ta mamaye parlon su duka har rige-rigen dubawa suke waye aka zafga ma mari haka..........✍️

*To laifin dad'i aka ce k'arewa, Jama'a nima zanso inji waye aka zafga ma mari haka, mu had'u a PAID BOOK akwai k'ura fa, shin yaya rayuwar Maryam zata kasance a gidan Ya Hafiz ne?' shi kuma Ya Abbas wai miye yake nufi ne da Maryam?, akwai cakwakiya a wanga littafi, ta b'angaran su Munnira ma fa yanzu wasan zai fara yanzu aka soma tafiyar*......

ZAHRA ROYAL STAR CE

SHARE FISABILILLAHI🥰🙏
Chapter 7 · 0% Book details