← Book details Wayafi K'aunata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 7

Sashe 3

Wayafi K'aunata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kitchen ta shiga ta d'akko b'arzazzar shinkafa ta d'akko roba ta juyeta a ciki ta wanke ta fas, sana ta d'akko tukunyar ta zamani sitima, tasa ruwa a k'asanta, tasa hawa na d'aya, ta d'akko mai da magi fari da d'an gishiri kad'an, duka tasa a cikin b'arzazzar shinkafar nan data wanketa, tasa mai fari mai d'an dama-dama, sana tasa farin magin nan da gishiri, sai tasa ludayi ta motsa ta had'esu, sai kuma ta d'an taro ruwa kad'an tasa a ciki, sai ta d'akko tukunyarta mai hawa-hawa ta fara zubawa gida uku ne ko ina tasa sai kuma ta d'akko gyad'a wadda ta daka ta sama-sama tasa a ciki, ko wanne gida sama-sama ta barbaza ta, ta had'a su waje d'aya ta rufe saman tukunyar da marfinta, ta d'ora akan gas.

Tana gama wannan ta d'ora wata tukunyar ta d'akko d'anyan naman kaza dake cikin firiza tasa a tukunya, ta yanka al'basa a kai ta d'ora a d'ayan gas d'in, sai kuma ta d'akko tafarnuwa ta dakata da kayan k'amshi tana gama dakawa ta juye a tukunyar data d'ora naman kazarta a ciki, sai da naman kazarta ya tafasa ya fara k'amshi ta d'akko markad'ad'd'und'on kayan miyarta ta juye a ciki ta rufe, sai da miyarta ta fara dafuwa, sana ta bud'e tasa kayan d'and'ano, danda nan gidan ya fara d'omewa da k'amshin girki, sai da miyar taja sosai sana ta d'akko manja tasa a miyar ta rufe, sai kuma ta rage gudun gas d'in, ta koma ga danbun shinkafarta ta bud'e sama tasa cukali ta d'ebo, ya daho yayi wara-wara ta sauke ta juye a kula, sai da ta kai darning sana ta dawo ga miyarta, tana bud'ewa har mai ya fito sosai ta kashe gas d'in, ta juye ta itama a kula, ta kaita darning, ta dawo kitchen d'in ta gyara ko ina, sana ta bud'e firiza ta d'akko ayarta da dabino da kwakwa ta wanke su ta tsaftace su tasa a bilanda ta had'esu ta markad'e sai da ta tabbatar sunyi laushi sun markad'u, sana ta juye su, ta tace su ta d'akko wani jok mai tsawo ta juye a ciki, sai kuma ta d'akko madarar da ake yin iloka da ita, guda d'aya ta juye rabi a ciki, tasa cukali ta motsa ko ina ya had'e, saita d'akko k'ank'ara ta fasa ta ta juye a cikin kunun ayarta, ta aje gefe guda ta k'ara gyara kitchen d'in ko ina yayi kyau, sana ta fita ta aje shima kunun ayar akan darning.

D'an zaunawa tayi tana rik'e k'ugunta saboda ta gaji sosai, sai da ta d'an huta sana ta shige bathroom tayi wanka ta sake fashe jikinta da turare tasa turaran wuta tasa hijabinta ta rufe kanta dashi sai da ta tabbatar ko ina na jikinta ya d'au k'amshin turaran wutar, sana ta aje shi a gefe yana ba d'akin k'amshi, sallah tayi ganin har hud'u tayi, tana gamawa ta fito parlo ta zauna jiran mijin nata.

RAMADAN POV

Sai da ya gama sallah a masallaci sana ya shiga motarsa ya nufi unguwarsu, yana zuwa mai gadi ya wangale mai get ya shiga harabar gidan nasu yayi parking d'in motar yana kallon harabar gidan naso a cikin zuciyarsa yana tunanin da Abbansa yana raye da duk wannan matsalolin basu faru ba, sai da suka gaisa da mai gadi sana ya nufi cikin gidan naso.

A babban parlon gidan nasu ya tadda duka y'an gidan da k'annansa guda biyu sai Yayyansa guda biyu Ya Aysha ce kawai babu itama dan tayi aure su kuma Inteesar da Nawwara Auntys d'insa kenan basuyi auran ba sai k'annansa guda biyu Hasana da Usaina.

Suna ganinsa suka gaida sa shi kuma ganin Yayyan nasa mata na mai wani kallo yasa ya murtuke fuska yana gaida su badan yaso ba.

Amsawa sukai ba yabo ba fallasa Hajiya ce ke sakkowa, d'aga kai yayi yana kallonta ganin irin kallon da take aika mai dashi ne yasa yayi k'asa da kansa, tana k'arasowa har kasa ya duk'a ya kwashi gaisuwa, sai da ta zauna ta d'ora kafa d'aya kan d'aya tasha mur ta bud'e baki cike da isa ta ce "sai yanzu kaga damar zuwa ko kuma sai yanzu y'ar gwal d'in taka ta baka umarnin zuwa?" ta idasa maganar tana tsaresa da ido, shi kuwa cike da mamaki yake bin Hajiya da kallo, shikam ba duka jiya ne Ya Ayshar ta zo ta gaya mai sakon Hajiyar ba, katse mai tunani tai da cewa "koma dai minene ka sanar da ita cewa nanda wata biyu masu zuwa zaka k'ara aure, nanda sati biyu kuma zanzo har gidan naka da amarya, zata zab'i inda yayi mata koda d'akin da Munnirar take zaune ne kuwa, idan ta nuna nan ne yayi mata dole ta kwashe komatsanta taba amarya waje, kaji na gaya maka karma kace ban sanar dakai ba", wani irin kallo mai wuyar fassarawa yake bin Hajiya dashi wannan k'iyayya har ina kai jama'a ta ina zai fara ne, Hasana ce ta buga tsalle dama ba kunya ne da ita ba tana cewa "haba ai gara ta matsa taba amarya waje duk ta kanainaye komai dama... Kamin ta idasa maganar Ramadan ya tashi a zuciye yana d'auketa da wani gigitaccan mari ji kake tasss tasss, su duka sai da suka tashi tsaye, Hasana sai hawaye tana b'oyewa bayan Hajiya ganin yadda yake huce kamar zai rufeta da duka, Hajiya cike da masifa ta rufesa da fad'a tana cewa.........✍️

*Washhh Allah na gaji mu had'u zuwa gobe idan Allah ya kaimu*

ZAHRA ROYAL STAR CE

SHARE FISABILILLAHI🥰🙏

*👩‍❤️‍👨💞 WAYAFI K'AUNATA 👩‍❤️‍👨💞*
(Love Story)

PAID BOOK #500

MALLAKIN
*©ZAHRA ROYAL STAR*

*Littafin kud'i ne wadda ya shirya yin tafiyar dashi zai iya turo kud'insa, ko katin MTN ko hoton katin saika turo shaidar biya #500 ne kacal*

8130479973
*FATIMA RABI'U OPAY BANKA*

Zaka turo shaidar biyanka ko hoton katin ta wannan number d'in,
(08130479973.08035023054)

Free Page 5-6

بسم الله الرحمن الرحيم العالم

Muka ji saukar maganar ta akanmu cike da masifa tana cewa "kai dai Hafiz ban san irin ka ba wallahi, shin wai mika gani wajan wannan yarinyar mai kama da aljanu?, ka wani mak'ale mata, to tun wuri bari na gaya maka idan wani abunne a zuciyarka wallahi kayi gaggawar cire shi a ranka" ta idasa maganar tana hararara ta gaida ta nayi ina cewa "Inna Rabi ina wuni" wani banzan kallo data yi min tana cewa "da ban wuni ba kin ganni uwar iyayin tsiya, kai kuma bita zai-zai sai ka ciga ba da bin bayan ta kamar wani jelar doki, ai shi yasa d'an uwanka yake birgeni ya za'ai ma ya tsaya da wannan kucakar yarinyar", ta idasa maganar tana jan wani dogon tsaki tayi gaba abinta.

Shi kuwa girgiza kai kawai yayi yana kamo hannuna ganin nayi k'asa da kaina ya ce "Maryam" ya kira sunana a hankali d'agowa nayi ina dubansa cike da sona ya sake cewa "am so sorry my Maryam... Da sauri na katse shi da cewa "kai Ya Hafiz miye na bani hakuri to?, ai itama uwata ta ce dan tayi min fad'a ba wani abu bane" murmushi ya sakar min yana k'ara kallon kyakkyawar fuskata, shi dai Allah ya sani ina matuk'ar birgesa.

Ganin lokaci naja na ce "Ya Hafiz bari na shiga daga ciki kar Iya taga na dad'e" saki na yayi yana cewa "Ohh na ma manta aiken mu fa aikai oya jeki ina nan shigowa sashin naku" da to na amsa inayin gaba.

Da sallama na shiga Iya na zaune, ta tasa fulawar da zatai d'an wake a gaba tana jira na, murmushi na saki ina zama kusa da ita, tashi tayi tana d'ebo ruwa ta zauna tana cewa "yanzu fisbilillahi Maryam tun d'azo na aike ki sai yanzu kikaga damar dawowa saura masifaffan can ya shigo duk ya damu mutane" tana maganar dai-dai ta gama kwab'a d'an waken tashi nayi ina cewa "kai Iya wallahi a hakama nayi sauri kuma harda shi ya tsayar dani yana faman min tsiyar daya saba min yanzu dai kawo na jefa d'an waken" sakar min tayi, tana zama a tabarma, dama tuni ta d'ora ruwan zafi harya tafasa, zama nayi gefen murhun na fara jefa d'an waken, Iya dake kallona ta ce "yanzu sabo da Allah shi dai duk inda ya ganki hankalinsa bazai kwanta ba saiya jaki fad'a, ni na rasa wannan k'iyayya taku keda shi, to idan Allah ya k'addara zaku zauna inuwa d'aya fa..... Kamin ta idasa maganar da sauri har ina shirin zubar da kwab'un d'an waken na ce "kai Iya wannan wane irin fata ne kike min dan Allah ki daina ma wannan maganar karma mala'iko suji su amsa ina dalili ina zankai rigimar Ya Abbas kashe ni zaiyi wallahi", dariya ta sakar min tana cewa "ke ki bimin sanwa a hankali karki zubar min da kwab'i , wasa nake miki koni bazan bari a had'a ki da wancan mai bak'ar zuciyar ba".

Tashi tayi bayan na gama jefa d'an waken na d'akko roba da ruwa a ciki ina tsamewa ina cewa "yauwa Iya ta ai nasan baza ki bari ba Allah sarki da Kakana mai shano na nan ai da mai wannan bak'ar zuciyar bazai min duk wannan abubuwan ba", Iya dake zaune cike da damuwa da kewar mijin nata yau kusan shekaru bakwai da rasuwa, ta ce "Allah dai ya jik'an Malam" da amin na amsa nima zuciyata ba dad'i Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i.

Bayan na gama Iya ta ce nasa mai nashi a kula, sai da nasa masa na aje gefe, na had'a mana nida ita muka zauna muka fara ci d'an waken yayi mun dad'i sosai saboda yaji kayan had'i an yanka su tumatur dasu albarsa harda kwai a ciki.
Chapter 3 · 0% Book details