← Book details Wayafi K'aunata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 7

Sashe 1

Wayafi K'aunata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*👩‍❤️‍👨💞 WAYAFI K'AUNATA 👩‍❤️‍👨💞*
(Love Story)

PAID BOOK #500

MALLAKIN
*©ZAHRA ROYAL STAR*

*Littafin kud'i ne wadda ya shirya yin tafiyar dashi zai iya turo kud'insa, ko katin MTN ko hoton katin saika turo shaidar biya #500 ne kacal*

8130479973
*FATIMA RABI'U OPAY BANKA*

Zaka turo shaidar biyanka ko hoton katin ta wannan number d'in,
(08130479973.08035023054)

Free Page 1-2

بسم الله الرحمن الرحيم العالم

Gombe state Kauyen AKKO, Babban kauye ne kusan ma kamar Local Government ne Amma ba a bashi LGA ba, garine na fulanin asali kana Shiga ba sai an fada maka ba,

Maryam Muhammad Amadu mai Shano shine cikakken sunana na tasu cikin Babban gida mai d'auke da sassa daban-daban Amadu mai Shano shine asalin mai gidan yana da matarsa guda d'aya mai suna Kubura wacce muke kira da Iya, da y'ay'a biyar Baffah na Muhammad, sai Kawu Sule shine mai bima Baffa na sai Kawu Iro sanan sai Kawu Mamman sai autar su Gwaggo Fati, dukan su mazan a cikin gidan suka yanki fili ko wanne da shashinsa dukan su suna da aure Kawu Sule yana da mata Rabi da y'ay'a biyar Abbas shine Babba sai Mansur Hafiz sai Gaje da Hajara itace auta , sai Kawu Iro yana da mata mai suna Hindatu da yara uku Naja'atu Sa'ida sai dan auta Ismail, Kawu Mamman shima yana da mata da yara guda biyu, Khamis, sai Zeena, takan bar y'arta Zeena ta kula dani, tun sadda na taso na taso na tarar da kaina a cikin gidan Baffah na ya rasu tun ina k'arama, Umma na kuma ta fita daga cikin gidan Amadu mai Shano tayi wani auran, ta barni wajan dangin Baffa na tun tasowata gidan mu hud'u ne sa'anin juna ni sai Naja'atu sai Hajara da Sa'ida sannan Zeena tun farko na kasance rikon kaka dan haka na taso ba kyara ko tsangwama a gidan bani da matsala da kowa sai Inna Rabi wato matar Kawu Sule ta tsaneni a gidan a cewarta wai na tare wa y'an uwana jin d'umin Kakarsu Iya dan haka nakan d'an jima ban lek'a sashin Kawu Sule ba, duk da kasancewar shid'in da yaransa suna matuk'a sona idan aka cire mutum d'aya Ya Abbas ya tsane ni kamar mi baya ma son gani na nima na taso da tsananin tsoronsa mugune nak'in k'ari a cewarsa na fiye shagwab'a da son jiki dan haka sam tamu batazo d'aya dashi ba, a duk sanda yazo garin hutu da yake yana karatu ne can cikin birni, nakan sha jinin jikina har sai ya koma nake samu na sake bani kad'ai bama duk yaran gidan tsoronsa suke, sai Ya Hafiz shi yana matuk'ar kulawa dani sosai duk sadda zai fita ya dawo da kalar tsaraba da zaiyi min duk sadda zai shigo sashin Iya da murna nake tarbarshi, tunda Inna Rabi ta nuna bata son duk wani d'anta ya nuna min kulawa, sai ya rink'a cewa Iya yayiwa tsaraba, amma duk haka tana ankare da yadda Ya Hafiz yake nuna tsananin kulawa a kaina tayi fad'an harta gaji kullum idan tana mai fad'a ta rink'a cewa Ya Abbas ne kawai shine ya d'akko halinta dan gani take yasan abinda take so yasan abinda bata so, shi ko a duk sanda tace haka basarwa yake abunda ta kasa ganewa ga yaron nata shid'in sawun keke ne, baka gane gabansa bare bayansa, sanan ya kasance miskili ne ba kowa yake ganin dariyarsa ba a duk yaran gidan amma kuma ni a yadda nake gani duk yafi tsana ta akan kowa, Gwaggo Fati dake aure a can cikin birni a wajanta yake zaune yana karatunsa,sauran mazan gidan duk anan sukai karatun nasu, shi yasa nafi zuwa sashin Kawu Mamman a kullum can nake yini matarsa bata da matsala ta d'auke ni kamar ita ce ta haife ni, dan haka shi yasa nafi sakewa da ita, Kakata Iya Mai dogon zango tana k'ara sona ita ko Inna Rabi tana k'ara tsanata da d'anta Abbas yayin da Ya Hafiz ke nuna min tsantsar kulawa a gefe guda wasu har sun fara zargin ko sona yake, ga K'awaye na kuma y'an uwana abokan wasana suna d'ebe min kewa,

Irin wannan rayuwar ke gudana a ahalin Amadu mai Shano wannan kenan mu shiga cikin labarin kai tsaye.

Tafiya muke gaba d'aya y'an matan gidanmu tasowar kenan daga islamiya, cike da farin ciki muka shiga cikin gidan namu sai dai, fara'ar tamu ce ta rage shigarmu gidan jin yaran gidan na cewa wai Ya Abbas ya zo yau, wani irin miyau na had'iye dan nasan had'uwar bata dad'i, ko wanne b'angaransu ya nufa daka kallemu kowa ya k'ara shiga taitayinsa jin Boss ya iso gari Allah ya gani har bamu so yazo garin saboda bak'in halinsa.

Kai tsaye sashin Kakata na, nufa tun waje nake faman kiranta ina faman cewa "Iya ta na dawo kina ina ne", wani tsaki naji anja daga baya na da sauri na waiga ido na ne yayi min tozali dashi, dake zaune kan tabarma, alama gaida Iya yazo yi, bud'e baki yayi cike da miskilancinsa ya ce "wai ke yaushe zakiyi hankali ne kullum kina girma amma ba hankali, yanzu da kike kwala mata kira muryarki na tashi kamar ba mace ba, baki iya bari ki k'ara so gaki ga ita kina abu sai kace mahaukaciya" zunb'uro baki nayi ina k'unk'uni Allah ya gani da nasan yana wajan Iya da bazanyi ganganci shigowa ina kwala mata kira ba,

Iya dake fitowa duk taji mi yake cewa tana sababi tana cewa "wai ni kam Abbas miye wannan yarinyar ta tare maka ne kasa yarinya a gaba ka hanata rawar gaban hantsi, bana son irin haka fa, idan takurata kazo kayi tashi-tashi bana son gaisuwar, haka kawai abi a takurama marainiyar Allah", tashi yayi ya fice yana murmushi dan ya saba da matsifar Iya indai aka tab'a wannan yarinyar Maryam,

Niko cike da farin ciki Iya ta shigar min na rungume ta cike da shagwab'a na ce "Iya tun d'azo nake d'okin ganinki shine fa dama na sanar dake ashe wannan Ya Abbas d'in yazo ni banso zuwansa ba wallahi", na idasa maganar ina kwab'e fuska, dariya tayi tana saki na ce "keni sake ni uwar son jiki kamar mage kuma ki rage shiga harkarsa kinsan abun kad'an yake jira dama ya had'a ku", zunb'uro baki nayi ina bubbuga k'afa na ce "amma Iya ai kinsan bana shiga harkarsa shine ma yake shiga tawa kifa duba tunda na shigo ko lura banyi dashi ba amma ya fara zazzaga min matsifa sai kace jirana yake", "jiran naki yake mana kinga ki wuce ki cire kayan islamiyar nan ga abinci can ki wuce kici ki manta da al'amarinsa fad'anku ai baya k'arewa na rasa mi yasa hakan", cewar Iya.

*KADUNA* POV

Zaune take akan cinyar mijinta sai zuba mai shagwab'a take k'ara rungumeta yayi, cike da tsananin sonta ya ce "Ohh my Noor kina ritani da shagwab'ar nan taki fa minene kake so", shafa d'an k'ara min sajenshi tayi tana kallon cikin idonsa cike da son mijin nata ta ce "to ai sonka ne yake azalzalar zuciya ta indai muna tare sai kayi hakuri da rigimar tawa", ta idasa maganar cike da wata shu'umar murya wacce ta kashe mai jiki da ruhi "Ohh my Noor wannan salon naki shi yasa kullum kike k'ara shiga raina", cewar Ramadan,

Tashi tayi tsaye daga ita sai wata y'ar ficiciyar riga iya gwaiwa, ta fara d'an tafiya cike da jan hankali, binta yayi da kallo kamar wani tsohon maye yana lumshe idanuwansa da suka fara canza launi.

Suna cikin wannan yanayi kamar daga sama suka tsinkayi muryar Ya Aysha cike da tsana Aysha ke bin Munnira da kallo, ganinta da wata y'ar ficiciyar riga yasa cike tsanarta ta ce "to makira ai da wa'innan y'an iskan kayan naki irin na karuwan farko kika gama da K'anina tashi ki bamu waje ina son magana dashi" ta idasa maganar tana warga ma Munnira dake tsaye hararara Munnira kuwa wani irin kuka ne take jin na shirin taso mata, da gudu tayi uwar d'aka Allah ya gani dangin mijinta basa sonta, hatta uwar mijinta, sun taso ta gaba, daga aure duka shekararsu biyun dayin auran har sun fara mata gorin haihuwa abun na mugun ci mata rai bata da matsala da mijinta amma danginsa sune babbar matsalar ga abunda ke k'ara mata fargaba suna son tusamai dole sai ya k'ara aure gani suke kamar ta asirance masu d'an uwa abunda basu sani ba tsantsar kulawa ce da take ba mijin nata, kuka ta fashe dashi tana fad'awa kan gado.

Ramadan dake zaune rantsa idan yayi dubu ya b'ace, wallahi baccin Ya Aysha Yayarsa ce da sai ya mata rashin mutum ci, kodan sunga kusan shine k'ara mi a cikin su shine zasu rink'a wulak'anta mai mata, d'aure fuska yayi tamau, zaunawa tayi kusa dashi tana tab'e baki tana cewa "ai dole ka d'aure min fuska mana an tab'a y'ar gwal to sak'on Hajiya ne ta ce a gaya maka ta baka nanda sati d'aya kaje tana son ganinka, kuma zata kawo ma matar da take so ka aura dan baza mu zuba ido mu barka da wannan shu'umar matar taka ba ehe" wani irin kallo yabi Aysha dashi cike da tsananin b'acin rai ya ce "ni gaskiya bana da niyar k'ara wani aure wai mi Munnira ta tsare muku ne ni banga wani abunda take muku na rashin dacewa ba sai ma k'ok'ari take taga ta kyautata muku, amma bakwa gani ya kuke so tayi ne wai?" ya idasa maganar cike da tausayin kansa da kuma matarsa yasan halin Hajiyarsu muddun ta tsani mutum to ya bani idan taso abu kuma sai anyi Aysha kuwa da ta tashi cike da matsifa ta ce "kaga dakata Ramadan bani ce zaka ba wannan amsar ba Hajiya zakaje ka bawa kuma da kake kare matarka uban mi take a cikin gidan nan idan ba taci ta kwanta ba Mtsww aikin banza kawai tama ji da kyau wallahi sai Halima ta shigo gidan nan" tana idasa maganar ta fice daga cikin gidan.
Chapter 1 · 0% Book details