← Book details Wayafi K'aunata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 7

Sashe 2

Wayafi K'aunata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ramadan kuwa zaro ido yayi yana mai-maita Halima badai Halima d'iyar Kharima ba k'awar Hajiya ba wadda bai san Kharima da bin bokaye da Malaman tsubbu ba, yanzu irin wannan matar take so ya aura idonsu ya rufe basa ganin gaskiya.

Cike da tashin hankali yake kallon Munnira dake tahowa tana zama kusa dashi taci kuka kamar ba gobe idonta sunyi matsifar ja, d'an kwantawa tayi jikinsa cike da tausayi ya k'ara rungumeta zai bud'e baki yayi magana ta tari lumfashinsa ta ce "mijina basai kace komai ba na sani ba laifinka bane sana kayi biyayya ga abunda Hajiya ke so shine zaka ga dai-dai bazan tab'a iya hanaka kabi umarnin iyayenka ba " ta idasa maganar hawaye na zuba a cikin idonta, shima kansa idonsa ya kad'a yayi jawur, cike da rauni ta fad'a jikin mijin tana, fashewa da kuka tayi, ta kasa rik'e kukan zuciyarta sai zugi take mata..............✍️

ZAHRA ROYAL STAR CE

SHARE FISABILILLAHI 🥰🙏

*👩‍❤️‍👨💞 WAYAFI K'AUNATA 👩‍❤️‍👨💞*
(Love Story)

PAID BOOK #500

MALLAKIN
*©ZAHRA ROYAL STAR*

*Littafin kud'i ne wadda ya shirya yin tafiyar dashi zai iya turo kud'insa, ko katin MTN ko hoton katin saika turo shaidar biya #500 ne kacal*

8130479973
*FATIMA RABI'U OPAY BANKA*

Zaka turo shaidar biyanka ko hoton katin ta wannan number d'in,
(08130479973.08035023054)

Free Page 3-4

بسم الله الرحمن الرحيم العالم

D'akina na shiga ina mita a zuciyata harna gama cin abincin ina k'unk'uni da takaicin Ya Abbas shi dai idan bai k'untata min ba, baya jin dad'i.

Iya ce ta shigo tana kallo na ta ce "nikam Maryam kin shiga wajan Kawunki Mamman Zeena ba lafiya ki gano ta?" d'an tashi nayi da sauri ina cewa "ayya Iya ai ban sani ba, da kamin ma na shigo nan saina lek'a na gano ta" Iya dake zaune kusa dani ta ce "eh ya kamata dai kije yanzu daga nan ki wuce shigon d'an lami mai kanwa ki sayo min, zanyi ma wancan mai bak'ar zuciyar d'an wake".

Tashi nayi ina b'ata rai tunda naji ta ce d'an wake nasan dama shi zatai mawa amsa nayi ina cewa "Allah danke zanje amma indan halinsa ne baza ka mai komai ba, nikam duk yau banga Ya Hafiz ba?" na idasa maganar ina kallon Iya, tafiya na farayi naji maganar Iya tana cewa "dan Allah karki dad'e Hafiz kuma zaki gansa k'ila dakin fita ai uwarsa ce mai bak'in hali itama inaga ita ta hanasa shigowa".

Nidai idasa ficewa nayi ina jin Iya ta fara masifa danmi zasubi su takura min, mina tare musu ne?, haka kawai sun taso ni gaba, ina tunani na idasa sashin Kawu Mamman, da fara'a matarsa ta tarbeni kamar yadda muka saba, sai da na duba Zeena da jiki har tana jana wai dodo na ya dawo, dariya nayi na ce "dodon kuwa dai, Allah bawan Allah nan ko a hanya banso mu had'u, kinga fa daga dawowarsa sai da yayi min masifar tasa" na idasa maganar ina jan tsaki har cikin raina nima nake jin na tsani Ya, Abbas kamar yadda ya tsaneni, dariya tayi min tana cewa "hmm bari Maryam nima nan tsoro yake bani jiki na har kyarma yake idan muka had'u ko a hanya, bare in ni kad'ai ce, wai amma a haka Sa'ida ke sonsa har wani yanga take idan ta gansa k'arfin halinta mamaki yake ban" tashi nayi ina cewa "uhm ita taji zata iya wahala, Zeena yoni ko mazan duniya sun k'are ai bazan tab'a zab'ar Ya Abbas ba, kinga bari na tashi na tafi aiki na fa Iya tayi".

Tashi tayi tana d'an b'ata fuska ta ce "kai Maryam daga zuwa sai tafiya kinga daga zuwanki har ji nayi na warke ma" dariya nayi mata na ce "kinsan halin Iya dama ta ce karna dad'e tasan idan na shigo sashin nan har mantawa nake lokaci ya ja", daga bayanmu mukaji muryar Aunty (mamar Zeena kenan haka muke ce mata), tana cewa "a'a duk zaman nan dama harda aike akai miki maza to tashi kije kar taga kin dad'e, idan kuna labarin nan naku ai bakwa ji baku gani".

Dariya mukai gaba d'ayanmu Zeena na niyar raka ni da sauri na ce "la kiyi zamanki kinji ki da k'arfin hali keda baki da lafiya, bari yanzu zan dawo wancan mugun wai Iya zatai ma d'an wake" na idasa maganar ina ficewa daga sashin.

Ina gaf ficewa daga zauran gidan namu kawai naji munyi karo da mutum kamin nayi wani yunk'uri naji an hankad'eni ana d'auke ni da mari tasssss dafe kumatu nayi hawaye na zubo min, nasan ba kowa bane sai Ya Abbas shi d'in ne kuwa jin saukar maganarsa a kaina kaina, na k'asa sai da na d'ako ba shiri jin wata uwar tsawa daya daka min yana cewa "wai ke dabbar ina ce kwata-kwata ba kiyin abu cikin hankali kina tafiya buguzun-buguzun sai kace ba mace ba gidan ubanwa ma zaki?, da yammar nan dare ya kusa" wasu irin hawaye ne naji sun k'ara zubo min zuciya na tuk'ukin bakin ciki naji zafin maganarsa ta farko daya kira ni da dabba, ko kallo bai ishe ni ba, na k'ara jin saukar maganarsa a kaina "ba magana nake miki ba ko sai na tattakaki a nan wajan shashasha kawai", bud'e baki zanyi domin yin magana kawai kuka ya k'ufce min.

Maganar Ya Hafiz ce ta katse mu gaba d'aya cike da kulawa ya matso kusa dani kama hannu na yayi yana bin Abbas da kallo tsaki Abbas yaja "Mtswww" yana barin wajan, kallo na Ya Hafiz yayi yana sa hannunsa ya sharemin hawayen dake sintiri akan kumatu na ya ce "shittt kayi shuru haka nan idan kina mai kuka a koda yaushe to kullum zai rink'a saki kukan ne, kiyi hakuri kinji inda sabo yaci ace kin saba da halinsa, muje na raka ki, mi zaki sayo ne?" murmushi na d'anyi ina jin zuciyata na yin sanyi dan ganin Ya Hafiz d'in na bud'e baki na ce "kanwa zan sayo kuma mugun fa shi Iya zatai ma abinci" da sauri yasa hannunsa mai taushi ya toshe min baki ya ce "Ohh my Maryam bana hana ki kiransa da mugu ba ki daina ba kyau kinji Yayanki ne shi", zunb'uro baki nayi cike da shagwab'ar da ta zame min jiki na ce "to amma Ya Hafiz ai mugunne shi" Ya Hafiz dake murmushi yana kallo na wannan shagwab'ar tawa tana matuk'ar birgesa ya ce "kashh bana hana ki fad'a ba?" dariya nayi yadda ya kwaikwayi muryata yayi maganar yasa na tushe baki na ina dariya na ce "na daina Ya Hafiz",

Haka muka idasa har shagon muka sayo muka dawo, muna wasa da dariya dashi, yana ta gaya min kalamai masu dad'i har yasa na manta da wani wai shi Ya Abbas, harda abunda ya had'ani dashi, sai dai muna shigowa harabar gidan muka iske Inna Rabi tsakar gida tunda muka shigo take binmu da hararara daga ni har Ya Hafiz, da sauri naja jiki na daga garesa ina matsawa gefe shima kansa yasan wallahi ku za'a yanka ta sai tayi maganar da ta saba yi, ai ko kamin ya gama tunani a zuciyarsa muka ji saukar maganarta akanmu cike da masifa tana cewa........

*KADUNA* POV

Washe gari haka Munnira ta tashi duk jikinta a sanyaye ganin mijin nata shima duk zuciyarsa ba dad'i yasa duk ta kori wata damuwa dake d'awainiya da ita ta fuskanci mijinta.

Tashinsa kenan daga bacci yana zaune yana kallon silin d'in d'akin yayi zurfi cikin tunani yasa da sauri Munnira ta zauna akan cinyarsa ta d'an kwantar da kanta a k'irjinsa tasa hannunta tana d'an shafa faffad'an k'irjin nasa mai cike da gargasa a hankali ta ce "mijina tunanin mi kake?, pls tunanin ya isa haka nan, na had'ama ruwan wanka", ta idasa maganar tana kamo hannunsa murmushi yayi shima lokaci guda ta mantar dashi wata damuwa da kanta ta taya shi yin wankan cike da jan hankalin mijin nata.

Sanye take da wata riga ta shan iska iya cibiya sai d'an k'aramin wando iya gwaiwa mijinta yafi son yaga mace kullum da k'ananun kaya, shi yasa kullum itama tana k'ok'arin ganin ta faranta masa rai, parlo suka fito sai da ta ciyar dashi abincin safe sana suka dawo parlo suka zauna suna fira jefi-jefi har lokaci ya d'anja, d'agowa tayi tana binsa da kallo cike da sonsa tasa hannu tana shafo fuskarsa ta ce "ya kamata my kaje yau wajan Hajiya tunda ta ce cikin satin nan take son ganinka ya kamata kaje yau kawai" kallon matar tasa yake cike da so, ya sakar mata murmushi ya ce "insha Allahu yanzo dana fita sallah zan wuce unguwar tamu" ya idasa maganar zuciyarsa na d'an bugawa, lumshe ido tayi cike da jan hankali ta ce "to yau mi kake so na dafa ma da rana uhum?" murmurshi yayi ya ce "komi kika dafa zanci ai bari na tashi naji an fara kiran sallah", tashi tayi daga jikinsa, yana gaf ficewa ta kira sunansa tsayawa yayi, k'arasowa tayi kusa dashi kamar yadda ta saba ta had'e bakinsu waje d'aya wani irin kiss ta aika mai dashi ai ko yaji sakon har tsakiyar kansa, ya lumshi idonsa yana k'ara rik'eta sun dad'e a haka sana ta sake shi tana cewa "mijina Allah ya kare min kai ya dawo min da kai lafiya ya kareka da dukkannin sharri ya dawo min da kai cikin aminci", sosai yaji addu'ar tata, duk da ta saba mai haka amma koda yaushe da kalar addu'ar da zata mai shi yasa kullum sonta k'aruwa yake bawai raguwa ba.

Haka suka rabo zuciyoyinsu cike da begin juna,

Yana fita ta d'an tsaya tana cewa "to mi zan dafa mai?," can kuma saita d'an girgiza kai tana murmushi.
Chapter 2 · 0% Book details