Sashe 6
Wayafi K'aunata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai da sauri suka aje mai damen kud'i suka d'au maganin da kawai sai dai suka ganshi a gabansu, suka kama hanyar barin jejin cike da murna da samun cikar burinsu................✍️
ZAHRA ROYAL STAR CE
SHARE FISABILILLAHI🥰🙏
*👩❤️👨💞 WAYAFI K'AUNATA 👩❤️👨💞*
(Love Story)
PAID BOOK #500
MALLAKIN
*©ZAHRA ROYAL STAR*
*Littafin kud'i ne wadda ya shirya yin tafiyar dashi zai iya turo kud'insa, ko katin MTN ko hoton katin saika turo shaidar biya #500 ne kacal*
8130479973
*FATIMA RABI'U OPAY BANKA*
Zaka turo shaidar biyanka ko hoton katin ta wannan number d'in,
(08130479973.08035023054)
*from this PAGE's freebies are over guys, hurry up and pay for your trip*
*END OF FREE PAGE'S*
Free Page 9-10
بسم الله الرحمن الرحيم العالم
A kwana a tashi har candy mu ya matso sosai, inda y'an gidanmu nata shirye-shiryen gama makaranta.
Muna gaf mu gama yin candy Ummah tazo gari ba k'aramar murna nayi ba da zuwanta, inda ina mak'ale jikinta, muna zaune can saita kalle Iya ta ce "Iya dama nazo ne domin na tafi da Maryam can inda nake aure domin ta cigaba da karatun ta" shuru Iya tayi tana kallo na yadda nima jikina yayi mugun sanyi duk da murnar dake cina hakan baisa na fasa yin fargaba ba, saboda tuno maganar mu da mukai da Iya.
Iya ta gyara zama itama cike da farin ciki ta ce "Umman Maryam nima gaskiya zanso haka amma ki bari magabatan ta suzo tukun kinsan nima ban isa yanke hukunci a kanta ba".
Tun daga nan Umma ta ta d'an bari zuwa kwana biyu taji mi ake ciki, sai dai amma kwatsam sai muku tsinto maganar Kawu Mamman wai zancen aurar damu ake miye na sai na wuce karatu, gaba d'ayanmu suke shirin aurar damu, ba wata maganar wucewa karatu, wai d'an-d'an Hakimin garin mu shine yake son aure na, sosai na shiga tashin hankali tunda bansan dashi ba, kuka kawai nake kwana biyun nan sosai nayi bak'in cikin hakan amma babu yadda na iya dan Ummata tana gaf tafiya ta ce bazata iya zama tana ganina cikin damuwa ba, zaune nake akan cinyarta ina kuka d'agoni tayi tana cewa "Maryama kalle ni nan" d'agowa nayi ina kallonta idona cike tab da hawaye ta ce "nasan Kakarki ta baki tarbiyya yadda ya kamata banyi nadamar barinki a wajansu ba, kuma dama sunfi ni iko dake, naji za'a kira ki domin tabbayarki, Maryam karki cuci kanki ki fito ki sanar dasu idan baki son wannan yaron d'an gidan Hakimi, ina Yayanki Hafiz mi yasa bazaki zab'e shi ba?, na tabbatar zai kula min dake, shawara na baki a matsayi na na mahaifiyarki nasan kuna da jituwa dashi Yayanki Hafiz na tabbata shima yana sonki, tunda nazo gidan nan na lura hankalinsa shima ba kwance yake ba saboda yaji labarin anzo neman auranki, ya kasa fad'a ma manya ne saboda uwarsa tayi mai mugun gargad'i a kanki, amma ai ba a nan gidan zaku zauna ba, again ba a kanta zaku zauna ba, karki duba rashin jituwar ku da ita ki cuci kanki ki fito fili ki fad'a masu abinda kike so dan sunce baza su yi miki auran dole ba, kina jina?", tashi nayi a jikinta ina share hawaye tabbas naji dad'in maganarta, ko banza Ya Hafiz yafi min wannan D'an gidan Hakimin gara na auri Ya Hafiz duk da bana jin sonshi shima a raina kwata-kwata.
Amsa mata nayi da "insha Allah Ummah zanyi anfani da abinda kika ce" tunda daga nan Ummah ta wuce birni inda take aure bayan tafiyarta da kwana biyu, ashe shima Ya Abbas nata shirye-shiryen tafiya k'aro karatu k'asar waje inda school d'in su da yake karatu an zab'esa cikin masu zuwa k'asar waje dan cigaban karatun su, dama yana karantar likita ne ta b'angaran mata ta b'angaran lalurar su.
Shima Ya Hafiz ashe ya kasa hakuri sosai yake ta rokon alfarma gurin Iyayenmu maza dan ganin sun amince masa da kudirin aurena, har lokacin ina cikin matsananciyar damuwa har yanzu bazan ce bana son Ya Hafiz ba, sai dai shid'in bai damu da rayuwar birni ba, duk da cewa shid'in kyakkyawa ne kamarsu d'aya da Ya Abbas amma Ya Abbas yafi shi komai nesa ba kusa ba, kuma ko a nan cikin garin namu shid'in dan gayo ne wayayye, sai dai shifa ba ruwansa da harkar birni shine kawai matsalar sa, Kawu Iro da Kawu Mamman sune suka kirani domin tabbaya ta fisabilillahi ina son Hamza d'an gidan Hakimi dan basa so suyi min dole.
A can gefenmu ashe Ya Hafiz na kusa na hango shi ya jingina da bango yana kallo na wani irin kalar tausayi ya bani, da sauri na girgiza kaina ina cewa "ni gaskiya Ya Hafiz nake so", da sauri Kawu Mamman ya ce "kin tabbata?", kai kawai na iya d'agawa san nan na duk'ar da kaina k'asa, shuru sukayi kafin su ce "na tashi na tafi kawai".
Tashi nayi jikina a sanyaye ina hangen Ya Hafiz dake sujjada ta godiya ga Allah ina hangen fuskarsa cike take da tsananin farin ciki, ji yake kamar ya goya ni dan murna sai jifa na yake da wani shu'umin kallo harna b'acewa ganinsa.
Bayan kwana biyu Inna Rabi da taji irin had'in da akai da yaranta inda Hajara ita da saurayinta, ita ko Zeena da Hashim d'an abokin Kawu Iro sai kuma Sa'ida da Hamza d'an gidan Hakimi ni ko tare da Ya Hafiz duk muna murna da hakan, bare ni bazan ce bana so ba, ba kuma zance bana ra'ayi ba, duk dai Sa'ida taso Ya Abbas amma ba yadda ta iya ta hak'ura.
Inda Inna Rabi ta tasa Kawu Iro gaba da masifa danmi za'ayi irin wannan had'in masifa take tana cewa "ni gaskiya an cuce ni ba'a kyauta min ba danmi za'a had'a Hafiz da waccar yarinyar mai bak'in jini" tashi yayi kanta rantsa ya d'an fara b'ace ya ce "koke keda ikon aurar dasu, idan kin isa sai ki suke auran na gani" tashi tayi itama a zuciye tana banbamin masifa tana cewa "ai dole ka ce haka mana saboda an tab'a y'ar so, kuma wallahi indai na isa da Hafiz bazai aure wannan yarinyar ba bazata sab'o ba wallahi bazan yarda ba a maida min yaro yadda aka ga dama ba a maida min shi kamar wani lusari, waye bai san uwar wannan yarinyar ba sadda take aure a nan gidan, sai da ta maida Yayan naku kamar wani bawanta", wata irin tsawa ya buga mata idonsa ya kad'a yayi jawur, ita kanta sai da ta firgita ganin yadda mijin nata ransa yayi mugun b'ace ba shiri ta rufe bakinta cike da b'acin ran dake taso mai ya ce "wallahi Rabi kika sake kika tada zancan nan wajan Hafiz ko kikai mai maganar ya fasa auran nan to kema a bakin auranki.............
*KADUNA* POV
Zaune Munnira take tun jiya gabanta yake wata irin mahaukaciyar bugawa tun tana daurewa har wasu irin hawaye suka sami nasarar zubo mata wadda bata shirya zubowarsu ba, tashi tayi ta shiga d'aki, domin Ramdan ya fita zuwa wajan aiki d'akko wayar tayi ta dawo ta zauna Yayarta ta kira mai suna Hafsa wadda suke uwa d'aya uba d'aya su kad'ai suka rage ma junan su, iyayansu sun rasu tun suna y'an yara, itama Hafsar tana aure ne a Kadunar amma ita tana auran wani d'an siyasa ne mai kud'i, suna matuk'ar son junansu.
Bayan ta d'au wayar jin an d'auka ta sauke ajiyar zuciya can cikin wayar Hafsa jin kamar y'ar uwar tata tana cikin damuwa yasa ta ce "Munnira lafiya kuwa?, na jiki kamar ma kuka kike miye yake faruwa ne?" Munnira kam bata san sadda ta fashe da kuka ba, dama damuwar ta mata yawa, ta rasa wadda zata fad'awa ta samu sauk'i a zuciyarta abinda yasa bata yawan kai kukanta wajan y'ar uwarta indai tana cikin damuwa to itama ba k'aramar damuwa take shiga ba, cike da tashin hankali Hafsa ta ce "wai miye yake faruwa ne?, Munnira karki sa na wanko k'afata yanzu nazo gidan naki minene yake faruwa ne dan Allah?", share hawayen tayi tana girgiza kai kamar tana gabanta tana cewa "a'a ba sai kinzo ba amma Hafsa zuciyata ta kasa samun natsuwa akan wannan auran da Ramadan danginsa suke so yayi, wallahi Hafsa zuciyata bugawa take" cike da tausayin y'ar uwar tata tasan kishiya a yi maka ita da ciwo bare ita danginsa basa sonta wacce suke so ita za'a auro, cike da sanyin murya da son kwantar mata da hankali ta ce "ki kwantar da hankalinki dan Allah ki daina sa damuwa a ranki idan kika ji irin haka ki rink'a mai-maita Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un, sana Munnira ki rink'a karanta Alqur'ani mai girma ki yawaita yin azzakar, insha Allahu koda da niyyar cutar dake ta shigo Allah bazai tab'a bata ikon hakan ba", sosai Munnira taji zuciyarta tayi sanyi.
Inda Hafsa ta ce zata shigo gidan zuwa gobe su k'ara tattaunawa, da haka sukai sallama.
Tana nan zaune kawai taji tsayuwar motoci a cikin harabar gidan nata ba shiri yadda zuciyarta ta buga ta tashi ta lek'a ta wundo, ganin masu fitowa a cikin motocin yasa ta d'an zare ido, da sauri ta zawo hijabinta ta sa tana cewa "to mi ya kawo Hajiyar Ramadan da Yayarsa guda d'aya Nawwara?," ta tabbayi kanta, can kuma saita tuno ai dama sunce zasu zo, addu'a take Allah yasa su gama abinda suke su tafi karma su shigo cikin sashinta dan taga sun shiga d'ayan sashin wadda tasan nanne amaryar zata tare bayan anyi auran.