Sashe 5
Wayafi K'aunata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wajajan k'arfe biyu na fito Iya na tsakar gida tana aikin danbu ina ganin yadda take murza danbun na ce "kai Iya yauma dan Ya Abbas zakiyi danbun nan na sani daya zo garin nan sai abunda yake so shi kike yi" na idasa maganar cike da jin haushinsa murmushi Iya tayi ta ce "kinga bana son kilbibi kema duk da rashin jituwar taku irin abinci d'aya kuke so keda shi kunfi son abincin gargajiya dannayi kuma sai kice danshi nayi, kinga ki wuce inda zaki nasan sashin Kawu Mamman zaki sai kin dawo".
Tafiya na farayi ina cewa "eh Iya can zani ina so mud'anyi fira da y'an uwa na nasan suna can kar ayi ba ni", ina jin maganar Iya na cewa "ai dai duk kun kusa bamu waje duk ku tafi gidan mazajan ku" nidai harna idasa barin sashin bance k'ala ba dan wani irin haushi nake ji idan akai maganar auran nan wallahi, toni wama zan aura dan gaskiya ni a cikin zuciyata har yanzu bazance ga wadda nake so ba ko Ya Hafiz kawai shak'uwa ce amma bana jin sonsa a raina.
Ina tunani na idasa sashin Kawu Mamman ai kuwa na taradda yawanci y'an matan gidan na sashin sunje duba Zeena zama nayi cikinsu dan dukkan muna samun jituwa dasu garama Sa'ida ita ce mai d'agin kai cikinmu ba wani shiga harkarta nake yi ba.
Hajara ce ta ce "Ohh ni tun jiya rabon dana ganki Maryam" d'an gyara zama nayi ina cewa "hmm ina zaku ganni Boss d'in gidan nan ya dawo shi yasa ko son fita bana yi danma karmu had'u dashi" dariya suka sa gaba d'aya can Sa'ida uwar iyayi an tab'o mata inda ke mata k'aik'ayi ta ce "hmm bari kedai ai Ya Abbas yayi wallahi matarsa ta more daga gani zata ga soyayya irinsu ne basa da sakin fuska ga jama'a, amma ga iyalansu ba'a magana irinsu idan kaga suna nunama matansu soyayya zaka sha mamaki wallahi" duka sakin baki mukai muna kallonta na ce "ke amma Sa'ida baki san wadda suka iya soyayya ba yo ni Allah na tuba mi Ya Abbas ya iya idan ba d'aure fuska ba, haka zaije yana ma matar tasa yayita firgita d'iyar mutane ko wacece ma" na idasa maganar ina rik'e baki.
Shewa suka saki gaba d'aya Zeena ta ce "ai kuwa irinsu sun iya soyayyar Maryam kuma sun iya gigita mace nanne dai zasu nuna mana jan ido", da sauri Sa'ida ta ce "yauwa kin gane kenan" tab'e baki nayi ina cewa "ku kuke ganin haka, kuda kuke da samari a hannu, ai dole kusan wadda suka iya soyayya a cikin maza" shewa suka k'ara saki, har suna had'a baki wajan cewa "kai Maryam kema fa kina soyayyar nan ina Ya Hafiz d'in kika barsa" dariya na saki ina d'an jawo kwanon da Zeena kecin waina na ce "ke ba tayi kin tasa abu gaba sai narka kike?" na fad'a dan ina so a kauda zancan da sauri ta turo min kwanon tana cewa "yanzu fa nake shirin tashi na zubo miki nasan kina sonta sadda zaki shigo duk su Hajara sun gama ci" idasa cinye ta cikin kwanon nayi ina cewa "yanzu dai tashi ki k'aro min dama yunwa nake ji yau Iya ta tsiri danbu saboda Boss har yanzu bata gama ba", tashi tayi tana d'ebo min ta kawo min sai kuma ta zauna tana kallon Sa'ida dake cewa "ya kamata fa mu fara shirye-shiryen gaba school d'inmu tunda kusan dukanmu zamu gama a tare" na cika bakina da waina na ce "nima nama Iya magana zata ban wasu kud'i zamuje shago mu sayo irin su alawa zanje a bugo min sticker kuma amma ba mai pictures ba, mai suna nake so" da sauri Hajara tayi karaf ta ce "nima gaskiya bana son mai hoto mai rubutu nafi so nima, amma ni inaga Bashir zai kawo min a ranar" dariya muka saki muna cewa "ahh kaga masu samari", bugu ta kaima Sa'ida data fi mata tsiya tana cewa "kuma fa da samarin nan naku kowacce tana dashi wallahi, shawarar da zan baku ma karku wani wahalar da kanku zaso yo muku ne su kawo muku" dariya aka saki ana shewa, dama idan muka had'u kamar zamu tada waje.
Muna cikin fira Aunty dake madafa har yanzu tana tuyar waina muka ji maganarta suna gaisawa da Ya Abbas, ai ko danda nan kowa cikin mu ta shiga hankalinta.
Lek'o d'akin yayi bayan sun gama gaisawa yana zafga mana hararara da manyan idonsa ko waccanmu sai da ta had'e wani miyau, banda ni dake cin wainata ko kallo bai isheni ba sosai na kama kaina dan bana ma son disginsa.
Cikin kakkausar muryarsa ya ce "dakuka zo kuka rarrashe nan kuna surutun banza da wofi ina islamiyar?" Sa'ida ce cike da iyayi ta ce "Ya Abbas ai yau al'hamis" tsaki yaja ba haka ya so ba, so yayi na tanka mai ya samu kafar da zai min rashin mutumci, nima shi yasa nayi kunnan uwar shegu dashi, nayi kamar bana wajan, duk da haka sai da ya samu kafar da zai tanka min, kallo na yayi yana cewa "ke kuma kici a hankali mana kina cin abinci sai kace akuya nacin abinci ke komai idan za kiyi bakya duba cewa ke macece kiyita abu na rashin dacewa da'alla" wani tuk'ukin bakin ciki ne ya rufe ni na bisa da kallo ya gama yab'a min bak'ar magana yayi gaba abinsa ko a jikinsa kamar bashi yayi ba.
Da kyar na had'iye wacce ke bakina Zeena na ban hakuri shuru kawai nayi, can naji muryar Hajara na cewa "ke yanzu Sa'ida a haka kike son Ya Abbas komi kayi baka iya masa ba, ga shegen miskilancin tsiya da fad'an da babu gaira babu dalili, yanzu dan Allah miye cin abincin Maryam yayi da zaice wai kamar akuya nacin abinci kai jama'a, ni a yadda nake gani ma ita da yanga take cin abincin ta, amma shi yanzu ji abinda ya ce" girgiza kaina nayi ina jin abincin ya fice min a rai tashi nayi ina wanko hannuna na wanke baki na na dawo, Sa'ida da jikinta yayi mugun sanyi wasu abubuwan da yake min ba akan idonsu bane shi yasa harta kwallafa rai a kansa, shi ya yarfa ka gaban mutane ba abu bane mai wuya a wajansa................
*KADUNA* POV
Nawwara tana gama abinda zata yi ta dannawa Halima kira ta waya, Halima dake zaune a babban parlon gidansu tare da Hjy Kharima Mahaifiyarta duk duniya Kharima Halima kad'ai ce d'iyarta shi yasa ta sangartata da yawa kuma ita ta reneta Babanta sun rabo da Kharima da tsiya ta karb'e d'iyarta, tunda baida wani k'arfi da tsiya ta amsu Halima wajanshi tasa Malamanta suka rufe mai baki bai iya cewa komai ba.
Da sauri Halima ta tashi tana cewa "kinga Momy Nawwara ke kira" da sauri Kharima ta ce "yi sauri ki d'auka inaga maganar auranku ce da Ramadan ta taso" ai da hanzari Halima ta d'au wayar tana sata a amsa kuwwa, bayan sun gaisa da Nawwara sai taba Hajiya inda Hajiya ke shaidama Halima tana so gobe zuwa jibi ta shirya tazo zasuje gidan Ramadan zata zab'i sashin da take so koda na Munnira ne idan dai har yayi mata, wani tsallan murna Halima ta saki tana cewa "insha Allahu tana nan shigowa zuwa jibi", da haka Halima ta katse wayar.
Kallon Mahaifiyarta tayi ganin yadda ta saki wani k'asaitaccan murmushi tana d'ora k'afa d'aya kan d'aya wata shegiyar dariya ta saki tana cewa "lallai Hajiya basirarki ta toshe tunda har kikayi tunanin had'a jini dani, d'an naki da kike tak'ama dashi, kike ikirarin wata ta mallake sa to yanzu ne za'a mallake sa da gasken-gaske ai naku wasa ne" tafawa sukai ita da Halima suna sakin shewa Halima ta ce "ai Momy sai nasa ma Hajiya hawan jini bana ruwa ba saina maida d'anta kamar d'an korena sai abinda nake so shi zaiyi kai saina basa umarni ma idan zaije wajanta" tafawa suka sake yi Kharima ta ce "Hajiya kin d'akko ruwan dafa kanki, shiri zamuyi babba gobe zamuje can dajin zango wajan wani boka aikinsa kamar yankan wuka tun kamin ki shiga gidan za'a gama dashi".
Nan suka zauna suna tsara yadda abun zai kasance.
Kamar yadda suka tsara tunda dugu-dugun safiya suka d'au hanyar zango sunyi tafiya mai nisan gaske sana suka fara kutsawa cikin jejin mai duhun gaske tun a bakin hanya suka aje motarsu da k'afa suka rink'a kutsawa cikin uban jijin kwata-kwata ba ko d'igon tsoro a tare dasu bare gajiyawa daka kalli yadda suke kutsa kai cikin uban duhun jejin zaka san sun saba zuwa dama, a yadda suke bin hanyar data mik'a cikin dajin, sai da sukai tafiya a k'alla takai ta minti talatin sana suka iso wani waje wadda fili ne ba alamar akwai wani rai wadda ke rayuwa a wajan, amma ga mamaki na wata bukka ce ta bayyana kamar k'iftawa da bismililla, dajin ne ya d'auke wata irin girgiza da wata irin mahaukaciyar dariya, sai wani irin gurnani dake fitowa daga cikin bukkar, tsabagen yadda guguwa ke tashi da wasu irin koke-koke yasa Kharima da Halima had'ewa waje d'aya suna zazzare ido, wata irin murya sukaji ta kewaye su mai cike da kauri da kaushi amonta ba dad'in ji tana rarrabuwa kashi-kashi, ana zayya ne musu duk abinda suke tafe dashi.
Danda nan Kharima ta ce "eh boka mai jan aiki uban la'anannu uban shaid'ano waya ce dake ba kai ba boka mai zamani mai tafiya da zamani" wata irin mahaukaciyar dariya aka kece da ita ana cewa "kware kuwa nine ubanku la'ananun Allah, ga wani magani nan gabanku ta tabbatar sai ta shiga cikin gidan a matsayi mata, ta tabbatar duk wani abun shanshi ko na wanka tana sa wannan maganin a ciki, sai wani d'aurin gashi nan shi kuma ta tabbatar sai idan zai sadu da ita zata sashi a gabanta, ta tabbatar tayi aikin yadda akace idan ba haka ba k'aik'ayi ne zai koma kan mashek'iya, ku aje kud'in ku b'ace min daga gani".