← Book details Silar Waya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 9

Sashe 8

Silar Waya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwace take a kan gado littafi take duba wa kira ne ya shigo wayar ta share wa tayi bata ɗaga ba katse wa tayi sake kira aka ƙara katse shi ta ƙara yi sake kira aka yi a zafafe ta ɗaga wayar "ka kira ɗaya ba'a ɗaga ba kayi na biyu an katse ba sai ka hakura ba mtwsssss" ta katse kiran cibiga da kira aka yi daga karshe ta ɗaga "Kai maye ne? ka ishe Ni da kira fa" "Yi hakuri sunana Habib nine Wanda kika bawa number ɗazu" "Na baka number kamar ya na baka? A ina?" ta watsa masa tambayar "A Instagram mana ko kin manta "okay na tina, sai anjima" ta kashe wayar ta.
Kiran Huda tayi bata ɗaga ba ta sake kira sannan ta ɗaga "Wannan da kika bawa number ta ya kira"

"Wow Dan Allah, ai na zata ba zai kira ba shi yasa na bashi"

"Zan tura masa number ki ni kar ya dame ni gaskiya"

"Kar ki sake ai ke ya gani bani ba, please Kar ki bani kunya ki kula shi"

"Kin san bana son haka Koh"

"Karki ce komai please kawai ki kula shi Ni banga wani abu ba"

"Shi kenan ai" ta kashe wayar ta

✰✰✰✰✰

Tun daga lokacin yake kiran ta tun bata kula shi har ta fara gaba ɗaya ta maida waya abokiyar rayuwar ta ƙawancen su da Raudah yaja baya ba kamar da ba kullum Cikin jure mata kunne suke suna cewa Raudah ba ƙaunar ta take ba......

Bayan wani lokaci sunyi matuƙar sabo da shi har sun rabu tayi sabon saurayi Bashir tayi mugun yarda da shi tana ganin zai Aure ta saboda shi ta guji Aasim kullum cikin wulakanta shi take tana ganin ta samu miji ga zugar su Huda na aiki. Raudah tana faɗa mata gaskiya wani lokacin ta ji wani lokacin ta ki dauka.

Aasim kullum yana ganin zata daina kuruciya ce ke da mun ta amma kullum abin gaba yake mai makon yayi baya.

Wannan shine labarin su shine silar ƙaddarar ta

*Allah ya Gafarta mana🤲*

Mu Hadu a next page

Please Share🙏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[2/2, 6:32 PM] Fatima Zahra Intisar (CEO ZAAHRAH GRAPHICS DESIGN): https://chat.whatsapp.com/Kb1rRqrLAda8A1JJtEO4HU

*รเɭคг ฬคץค📱😢🖤*

𝑨 𝑻𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝑯𝒆𝒂𝒓𝒕 ❤️ 𝑺𝒕𝒐𝒓𝒚

𝔹𝕐 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ

🅟🅐🅖🅔 ❶❻

★★★★★
Tunda abin ya faru ta zama silent ko fita bata yi kullum tana gida daga ɗaki sai palour Ummi kullum nuna mata take kowa da ƙaddarar sa haka Tata taso tayi hakuri amma ta kasa fita gani take kowa ya san abinda ya faru da ita.

★★★★★
Kwance take akan Kujera tayi nisa a tunanin da take sallama ake tayi shirun da ta ji ba'a amsa ba shi yasa ta tura kofar ta shigo taɓa ta tayi zumbur ta tashi "Ummi har kin dawo"

"huumm har yanzu dai ba zaki yi hakuri ba Koh, to ba ita ba ce Ni ce, bata nan ne"

"Take gidan Uncle bata dawo ba"

"Ke kuma sai ki ka kwanta sana'ar ki Koh"

"Kyale Ni kawai, Tun ina trying number sa har na daina ga shima Yaya Aasim ɗin ya daina kira maybe ma ya hakura"

"kiyi hakuri kinji, dama ya zai kira kefa kika kore shi, kin ce karya ƙara kira to ya za'ayi ya kira, ai sai dai ki kira shi"

"In kira in ce masa me, kin san yadda muka yi da shi ne? baki san Rashin mutuncin da na yi masa ba"

"Ai wayar ki zaki ɗauka ki kira ki bashi hakuri"

"Kai inaa, salan yace dan naga ya samu aiki kuma ga kaddarar data same ni, yace tallan kai na nake masa har abada"

"Ai ba cewa zaki yi ya zo ba, Nima baza goyi bayan haka ba hakuri zaki bashi ko zai sauko"

"A'a ki canja shawara, banda wannan inya zo dan kansa shikenan amma bazan kira shi in ce yazo ba"

"Tohm ai shikenan" suka cigaba da hirar su har Ummi ta dawo Sannan ta tafi.

Zaune suke a palour gaba ɗayan su Abi ne yace "Ina so na sanar miki idan Allah ya kaimu gobe Aasim zai zo in kin ga dama ki kore shi in kin ga dama ki saurare shi ku dai-dai ta juna" "Idan kin ga dama ki kore shi sai ki fitar da wani mijin kafin ƙarshen watan nan" ya tashi ya fice...

★★★★★
Tura kofar tayi ta shiga yana zaune akan kujera neman guri tayi ta zauna ajiye tray ɗin hannun ta tayi "Yaya Aasim barka da Yamma" "Barka kadai, ya gida" "Lafiya kalau" "Masha Allah" gyara zama yayi sannan yace

"Dama ba wani abu ne ya kawo Ni ba sai cewa ina son na faɗa Miki na fasa Auren ki, ya kamata ki faɗa wa su Baba tunda su suka ai ko ni"

A firgice ta dago ta kalle shi "Mai kake nufi kenan sai Dana fara Sonka zaka ce ka fasa Aure na, Haba Yaya Aasim ya zakayi min haka me nayi maka Innalillahi wa Innalillahi rajiun"

*Allah ya Gafarta mana🤲*

Mu Hadu a next page

Please Share🙏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[2/3, 6:35 PM] Fatima Zahra Intisar (CEO ZAAHRAH GRAPHICS DESIGN): https://chat.whatsapp.com/Kb1rRqrLAda8A1JJtEO4HU

*รเɭคг ฬคץค📱😢🖤*

𝑨 𝑻𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝑯𝒆𝒂𝒓𝒕 ❤️ 𝑺𝒕𝒐𝒓𝒚

𝔹𝕐 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ

🅟🅐🅖🅔 ❶❼

★★★★★

"Amma Yaya Aasim banyi xayan zaka yi min haka ba, baka duba ƴan uwan takar mu ba"

"Idan ban Miki haka ba ya zan Miki, wace ƴan uwan takar zan duba? ke baki du ba shekara na wa ina sonki amma kina girma kika ce ba kya so na, tun baki san kan ki ba nake sonki"

"Amma yanzu Insha Allah zan gyara kuskure na, kayi hakuri"

"Sai yanzu kenan zaki gyara kuskuren ki, Hakuri ma kawai zaki bani, baki san wahalar dana sha a kanki ba" "Huuuummmm Wlh Najmah da ba dan ƙaddarar data same ki ba ba abinda zai sa ki kula Ni"

Share hawayen fuskar ta tayi "Gori zaka min kenan ai bata wuce kan kowa ba, Nagode" ta tashi zata fice

"Ina zaki tsaya mu gama magana"

"Wace maganar zamu cigaba tun ba'a je ko ina ba ka fara min gori, gwara na tafi"

Ta fice da sauri, dafe kansa yayi ya fara magana shi kaɗai "oh God dana san kwabar da zan yi da banyi haka ba, gaskiya nayi kwaba bari in bi ta" "No nayi mata waya idan ta hu ce yanzu ba zata saurare Ni ba" ya fice.....

★★★★★

Da kuka ta shiga palourn Ummi ce kaɗai tana karatun Alkur'ani rufe wa tayi ta kalle ta "Ke kuma menene haka zaki shigo ko sallama babu"

"Babu komai, bari in kwanta"

"Da komai mana dawo ki Zauna, Kukan me kike" shiru tayi bata ce komai ba

"Ba da ke nake magana ba kika yi min shiru"

"Ummi ba komai"

"Da komai zaki faɗan ko sai na saɓa Miki" ta faɗa a zafafe hawayen fuskar ta goge sai tace

"Ummi dama idan ka samu wani naka sun kowa gudar ka yake?"

"Mai ya faru kuma? mai yayi Miki"

"Ummi shima gori yake mun saboda ƙaddara ta, gani nake kowa haka zai mun tunda ɗan uwa na yayi min haka" labarta mata abin da ya faru tayi

"Ba gudar ki yake ba, ke baki kalli Abinda kika yi masa ba? Abinda nake gudar Miki kenan, bari Abi yazo in sanar masa"

"Dan Allah Ummi karki faɗa masa kawai ku kyale shi zai fi"

"Sai na sanar masa" ta tashi ta bata Guri kukan ta ta cigaba....

Da daddare bayan Abi ya dawo ta sanar masa da abin da ya faru kamar yadda Najmah ta faɗa mata Ya kira Yayan sa ya faɗa masa tun a daren yace su haɗu a gidan Hajiya gobe.

*Allah ya Gafarta mana🤲*

Mu Hadu a next page

Please Share🙏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[2/5, 10:38 AM] Fatima Zahra Intisar (CEO ZAAHRAH GRAPHICS DESIGN): https://chat.whatsapp.com/Kb1rRqrLAda8A1JJtEO4HU

*รเɭคг ฬคץค📱😢🖤*

𝑨 𝑻𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝑯𝒆𝒂𝒓𝒕 ❤️ 𝑺𝒕𝒐𝒓𝒚

𝔹𝕐 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ

🅟🅐🅖🅔 ❶❽

★★★★★
Zaune suke a tsakar gida Shida Mama kallon ta yayi "Aasim ko ya dawo"
"Ya dawo tun ɗazu ya shiga ɗaki kamar ba shi da lafiya na ganshi"

Haydar ne ya shigo gaishe su yayi "Kira min Yayan ku"
Tohm yace ya shiga ɗakin sa
Kwance ya tarar da shi Sallama yayi shiru bai amsa ba da alama yayi nisa a tunanin da yake ƙara sa shiga ɗakin yayi taɓa shi yayi "Yaya lafiya" "Lafiya kalau, baka ga ɗare yayi ba kaje ka kwanta"

"Yanzu zan kwanta dama Abba ne yake kiran ka kazo"

"Abba kuma, da daren nan" tashi yayi suka fice.

Neman guri yayi ya zauna kusa da Abban "Gani" "Ya gurin aikin" "Alhamdulillah" "Masha Allah, Ya kuka yi da ita da nace kaje" Ɗa go wa yayi ya kalle sa "Abba bamu dai-dai ta ba, mun samu matsala"
"Ko kuma kaje da matsalar ba, shine Abinda na aike ka yi kenan"

"A'a akasi aka samu, gobe Insha Allah zan koma"

"Ba ma sai ka koma ba, ai ya wuce Allah ya bata Nagari na zata kai ɗan uwanta zaka iya riƙe ta tunda kana sonta, tashi kaje sai Allah ya Kaimu safiya"

"Abba kayi hakuri, Ni ba sonta ne bana yi ba, Ina sonta kuma zan Aure ta ko baka ce ba Balle har ma kace, Kuskure ne Insha Allah zan gyara"

"Kuskure fa kace, tashi kaje zanyi shawara" tashi yayi ta tafi.

★★★★★

Zaune suke a palourn Hajiya kowa yana zaune Yaya Umar ne ya fara magana "Kamar yadda jiya muka yi waya da kai muka yi magana akan yaran nan shima Aasim na tun tuɓe shi kuma yayi nadamar abinda yayi"

"Na yanke shawarar yi wa Aasim da Najmah aure nan da Wata biyu idan Allah ya kaimu"

sai ya maida kallon sa ga Najmah dake kuka
"Najmah ba wai dan Bana sonki bane ko kuma ɗan bani na haife ki ba a'a ba haka bane. Ina ganin na isa da ke kamar su Janin sannan kuma in kin ga ba zaki iya Auren sa ba ki faɗa min ba za'a yi Miki Auren dole ba"
"A'a Abba ka isa da Ni mana, ko wani kace in Aura ba shi ba zan Aura, Allah yasa hakan ya zama Alkhairi"
"Ameen Ameen" duk suka faɗa maida kallon sa yayi ga Aasim
Chapter 8 · 0% Book details