← Book details Silar Waya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 9

Sashe 7

Silar Waya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Insha Allah nan da five minutes zan gama in fito"

"Shikenan sai kin fito ɗin" fice wa yayi daga ɗakin ita kuma ta cigaba da shiya kayan

**************
Zaune suke a palour ita da Maman ta "Yanzu ke dole sai yazo yaye ba zaki iya yaye shi da kanki ba ne? ko ke da zan yaye ki na kaiki gida"

"Tausayin sa nake ji shiyasa nace gwara in kawo shi nan a yaye shi in Yana gurina bazan iya ba"

"Gwara ki koya kowa da haka ya saba, yanzu da babu Ni wa zaki kaiwa? Allah yasa ya zauna tunda bai taɓa kwana a ko ina ba"

"Insha Allah ma zai zauna"

Bayan magariba yazo suka tafi da wayo ta fice daga gidan kar ya ganta....

************
ᴺ ᴵ ᴺ ᴱ ⁹ ʸ ᴱ ᴬ ᴿ ˢ ᴸ ᴬ ᵀ ᴱ ᴿ

*Allah ya Gafarta mana🤲*

Mu Hadu a next page

Please Share🙏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[1/24, 10:40 AM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/Kb1rRqrLAda8A1JJtEO4HU

*รเɭคг ฬคץค📱😢🖤*

𝑨 𝑻𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝑯𝒆𝒂𝒓𝒕 ❤️ 𝑺𝒕𝒐𝒓𝒚

𝔹𝕐 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ

🅟🅐🅖🅔 ❶❷

************
ᴺ ᴵ ᴺ ᴱ ⁹ ʸ ᴱ ᴬ ᴿ ˢ ᴸ ᴬ ᵀ ᴱ ᴿ
Allah ya amsa Addu'ar su Umma ita ma Allah ya azurtata da samun cikin har ta kusa Haihuwa. Zaune suke ita da Abdallah tana koya masa assignment da yanzu yake kiran ta Ummi Masha Allah yaron ya zama saurayi shekarar sa gurin Goma "Alhamdulillah mun gama, ka rufe books din kasa a jaka"

"Tohm Ummi, zan iya zuwa wasa" Shafa kanshi tayi tace

"zaka iya zuwa yaron Kirki ai ka gama aikin" cikin murna da zumuɗi ya kai jakar gurin ajiye ta sannan ya dawo

"Ummi na tafi" ya fice

"Allah ya tsare kayi a hankali kar kayi nisa" tohm yace ya fita a guje

"Har yanzu jinsa yake yaro Allah ya tsare" Ta tashi da kyar da shige kitchen Girkin da ta ɗora ta ke so ta gama kafin ya dawo ta san yana hanya.
Cabinet ɗin kitchen ta dafa Innalillahi wainnaillaihir-rajiun tace dur kushe wa tayi a gurin Na kuɗa take yi tun ɗazu amma yanzu tafi tashi ƙara koƙar ta wa tayi ko zata iya cigaba da aikin amma ina ta kasa addu'a kawai ta cigaba da yi Allah ya shigo da Abdallah ya kira mata shi....

Shigowar sa kenan cikin layin ya haɗu da shi a bakin masallaci "Daga ina kake Abdallah"

"Abi sannu da zuwa wasa na tafi dana dawo kuma naje masallaci"

"Shigo mu ƙara sa gidan kasan bana son kana zuwa wasan nan Koh"

"Gidan su Auwwal naje fa, daga nan ban ƙara zuwa ko ina ba"

"Toh ka kiyaye yawo daga nan kar ka tinda zuwa ko ina"

"Tohm Abi" Fita yayi daga motar ya buɗe gate ya dawo ya tashi motar suka shiga gidan parking yayi sannan suka fito ya koma ya rufe suka shiga ciki.

Da sallama suka shiga shiru suka ji ba'a amsa ba ƙara sallamar yayi shiru nan ma Abdallah ya kalla "Ina Ummin taka taje, ko ta fita ne"

"Lokacin dana tafi Wasa a palour na barta tana zaune"

"Ko bacci take, amma i Yanzu bata bacci ai, Zauna a nan in duba ɗaki"
Tohm yace shi kuma ya wuce ciki duba bedroom din su yayi bata nan har toilet fito wa yayi ya duba ɗakin Abdallah nan ma bata nan palour ya dawo gurin Shi
"Bata ce maka zata je wani gurin ba?"

"A'a bata ce ba, a palour na barta fa"

"Bari in duba kitchen ko tana ciki, amma in tana ciki ai da tini ta fito tun shigowar mu"
kitchen ya nufa tin bai ƙara sa ba ya jiyo ta tana addu'a sauri ya ƙara a dur ƙushe ya ganta a bakin cabinet "Baki da lafiya amma baki kira Ni ba?"

Gas din da yake ci ta shiga nuna masa tashi yayi ya kashe sannan ya dawo ya ɗauke ta mota ya Kaita ya dawo ya wuce bedroom din su kayan Haihuwar da ta haɗa jiya ya ɗauko Abdallah yace wa ya tashi su tafi ya rufe gidan suka yi asibiti...

✬✬✬✬✬✬✬✬✬

Shigar su asibitin ke da wuya nakuɗar ta kara karfi nurse's ne suka karɓe ta suka yi ciki da ita waya ya ɗauka ya kira mama sannan ya kira gidan su. Nurse ce tazo karɓar kayan haihuwa tambayar ta ya shiga yi ta sauka tace A'a ta ƙara gaba.

Ba'a jima ba sai ga Nurse din ta fito da Baby a hannu "ta sauka, ka samu baby girl" ta mika masa ƴar "Alhamdulillah" kuɗi ya ɗibo a cikin aljihun sa ya bata ta tafi tana washe baki waya kara ɗauka ya kira su ta sauka Zama yayi kusa da Abdallah yana nuna masa Baby.....

Ba'a jima ba sai ga su Mama sunzo suka karbi ƴa suna Barka "Ina take ita?" "Sun fito da ita tun ɗazu tana dakin hutu" "Masha Allah, Abdallah anyi ƙanwa an zama yaya"

*Allah ya Gafarta mana🤲*

Mu Hadu a next page

Please Share🙏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️

[1/29, 6:29 PM] Fatima Zahra Intisar (CEO ZAAHRAH GRAPHICS DESIGN): https://chat.whatsapp.com/Kb1rRqrLAda8A1JJtEO4HU

*รเɭคг ฬคץค📱😢🖤*

𝑨 𝑻𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝑯𝒆𝒂𝒓𝒕 ❤️ 𝑺𝒕𝒐𝒓𝒚

𝔹𝕐 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ

🅟🅐🅖🅔 ❶❸

★★★★★

Bayan Isha'i aka sallame su tunda lafiyar ta qalou suka tafi gida Abdallah yana maƙale da ita yaƙi zuwa ko ina

Washegari sai zuwa Barka akeyi dan haka maman ta tace su zauna anan ba sai ta koma gidan su ba za'a sami wadda zata kula da ita su Aasim tun safe suka zo yana tare da Abdallah maman sa ma ta kusa haihuwa. Kullum sai an zo Barka gidan kullum a cike yake..

𝗕ɑ𝑦ɑ𝖓 𝗞𝑤ɑ𝖓ɑ 𝘚һⅈ𝒹ɑ

Ranar suna Yarinya taci suna Khadijah an maida mata sunan ƙanwar su Zasu ringa kiran ta da ɳαʝɱαԋ Yarinya ta samu kyaututtukan mutane anyi suna lafiya an gama lafiya. Sun cigaba da kula da yarinyar su Cikin so da ƙauna ita da Yayanta. Bayan wata shida Amina ta haihu ta samu baby Boy Anyi wa Aasim Kani Ranar suna Yaro yaci suna Aliyu Haydar. A lokacin Najmah watan ta shida da Haihuwa..

✰✰✰✰✰

Aasim tun Najmah tana yarinya yake son ta ba shi da zance sai Najmah kullum yana gurin ta har aka haifa masa Kani yawanci yana gidan su gurin ta. Idan ya tafi makaranta baya dawo wa sai an gama semester tun daga lokacin shaƙuwar su taja baya
✰✰✰✰✰

Najmah ta taso cikin kulawar iyaye da yan uwa da kuma yayanta kowa nata ne amma akwai rashin ji ƙawar ta ɗaya yar makotansu ƙanwar Auwwal Amma ita bata da kiri niya kamar Najmah sun taso tare idan baka sansu ba zaka zata ƴan biyu ne makarantar su ɗaya ko ina tare zaka gansu har su ka bar Unguwar basu rabu ba suna tare har lokacin makarantar su ɗaya.
Abdallah yayi karatun sa a B.U.K ya karanci Accounting ya nemi aiki bai samu ba sai ya koma kasuwa gurin Abi kuma Allah ya buɗa musu

⁂⁂⁂⁂⁂⁂

Gidan Yaya Umar
Tunda yayi retire komai ya tsaya masa kuɗin retirement din sa shi ya juya ya fara sana'a da su Ƴaƴan sa Huɗu biyu maza biyu mata Aasim, Haydar, sai yan biyu Janin da Hanan suna zaune lafiya da kwanciyar hankali suna son junan su yana cikin kasuwancin Allah ya haɗa shi da yan damfara suka gudar masa da kuɗin gaba ɗaya..........

*Allah ya Gafarta mana🤲*

Mu Hadu a next page

Please Share🙏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[1/29, 6:30 PM] Fatima Zahra Intisar (CEO ZAAHRAH GRAPHICS DESIGN): https://chat.whatsapp.com/Kb1rRqrLAda8A1JJtEO4HU

*รเɭคг ฬคץค📱😢🖤*

𝑨 𝑻𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝑯𝒆𝒂𝒓𝒕 ❤️ 𝑺𝒕𝒐𝒓𝒚

𝔹𝕐 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ

🅟🅐🅖🅔 ❶❹

★★★★★

Aasim tunda ya gama makaranta bai samu aikin yi ba da farko zaman guda ya fara daya ga abin ba ƙare bane sai yake zuwa kasuwa har lokacin yana son Najmah Addu'ar sa kullum Allah yasa ta zama matar sa.

Shigar ta University shine abinda ya fara basa matsala duk da dama bata amshi soyayyar sa ba amma tun da ta ƙara ƙawaye wayyayu suke hure mata kunne kullum Raudah tana nuna mata ta karɓe shi amma suna hana ta

ᕯ ᕯ ᕯ

Ƴan mata uku ne Zaune a bakin theater biyu ne suke tayin hira ɗayar kuma waya ce a hannun ta tana operating "Wow Kinga wani handsome yayi following din ki" "Mugan shi"cewar Huda "Kin Ganshi Gsky ya haɗu"

"Kai Masha Allah yi Follow back mana"

"Gaskiya Najmah kina da matsala ke ko duba followers ɗin ki ba kya yi balle kiyi Follow back "

"Ni ba wani dubawa nake ba, basu dameni ba, yanzu muka fara makaranta bana son bawa su Abi Kunya gwara in dage inyi karatu"

"Gaskiyar kam bani littafin Nima in duba, Sarkin karatu ana Library"

"Nima ina ga can zan tafi ai, Huda ban wayar in tafi"

"Ki tsaya mana guy ɗin yana online har yayi magana chat muke yi ma"

"Zaki iya following din sa ai sai ku cigaba da hirar"

"Ai bani yayi following ba, Kinga ma yace in bashi number, bari in rubuta masa number ki"

"Ki bashi taki mana, da ke yake hira"

"Ai har na tura masa, please in ya kira Karki ki ɗaga wa baki gansa ba nadan zamu ci kuɗi"

"Nifa har yanzu Bana son cin kuɗin maza kin san halin su"

"Kar kiji komai in bazaki Ci ba ki bamu"inji Ahlam

"Bani waya ta na tafi gurin Habibty"

"Gata nan"ta mika mata wayar........

*Allah ya Gafarta mana🤲*

Mu Hadu a next page

Please Share🙏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[2/2, 6:31 PM] Fatima Zahra Intisar (CEO ZAAHRAH GRAPHICS DESIGN): https://chat.whatsapp.com/Kb1rRqrLAda8A1JJtEO4HU

*รเɭคг ฬคץค📱😢🖤*

𝑨 𝑻𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝑯𝒆𝒂𝒓𝒕 ❤️ 𝑺𝒕𝒐𝒓𝒚

𝔹𝕐 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ

🅟🅐🅖🅔 ❶❺

★★★★★
Chapter 7 · 0% Book details