← Book details Shukra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 53

Sashe 8

Shukra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nasani but jamaan gari fah? Kiyi tunani akai shuairat"
Ya sauketa a gida yayi tafiyarsa ckn bacin rai, shuairat kuwa tunanin maganganun Mahmud take tana Neman mafita.

Hmmmmmm......akwai ~work~
Muje xuwa
Taku a kullum *Reefat*😘😘😘
[2/21, 2:37 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*18*
By *Reefat yahya*

Mr President ya koma gida a gajiye yake likis ga ciwon kai sabida hayaniyar da sukayi da jamaa a meeting nasu ya cire babbar rigarsa ya xauna a kan gado ya buga wani uban tagumi.
Umaima CE ta shigo tare da sallama ckn sanyin jiki ta xauna kusa da mahaifin nata ta sunkuyar da kai hawaye ne ya fara sauka
"Dad don Allah ka rabu da yarinyar nan kana sauke girma da darjarka too much"
Ta nuna masa sababbin hotunan da aka tura yau , kunya ne ya kama shi don ganin yanayin hotunan sun kurawa juna ido shi da shuairat umaima CE ta katse masa tunani

"Dad pls promise me"
"Don't worry my baby babu abunda yake tsakaninmu kinji? Ki kwantar da hankalinki hakan bazata sake faruwa bah"

"Promise?
"Yes promise" wani murmushn dadi tayi daga nan Suka fara hira sannan ta koma bangarenta ckn wani irin farin ciki.
A hanya Suka hadu da bash yana waya bai lura da ita ba sauran kadan suyi karo ta ja gefe ta bashi hanya ya juya kenan Suka hada ido ya kashe wayar ya sunkuyar da kai alamar girmamawa
Murmushi ta sakar masa tace
"Dama ina son magana da kai"
Mamaki ne a fuskarsa sabida yasanta da shegen girman kai ta gane hakan tace
"Kana mamaki koh? Don't wory wasu yan tMbayoyi ne zan maka"
Nan Suka zauna bayan ta bashi ixinin xama a harabar gidan ne akan wasu kujeru kyawawa.

"Na dade ina ganinka tare da mahaifina kuma nasan kai kana daya daga ckn mutanen da Suka fi kusa da mahaifina, don haka nake son sanin wani Abu dangane dashi da wannan yarinyar"

"Ranki ya dade ni bansan komi game da maganar ba , kawai nasan babu soyayya a tsakaninsu kuma babu wata alaka mai karfi a tsakaninsu"

"Toh kana nufin mahaifina yana bin matan banxa kenan?
"Subhanallah! Ya daga idonsa Suka fada ckn nata

"Yes! Idan babu soyayya ko wata alaka a tsakaninsu toh me hadinsu?
Ran bash ya baci sosai yace
"Ita wannan yarinyar ba karuwa bace"

"Who knows" umaima ta fada ckn kwanciyar hnkli idanun bash sun canza xuwa ja yace

"Kina xargin mahaifinki da aikata xina?

"Ya zanyi? Duk laifinsa ne shi ya jawowa kansa ana ta zaginsa a gari"nan ta fashe da kuka me ban tausayi tabbas abun akwai daure kai ynxu haka ake zargin Ya'r uwarsa? Kai baxai yiwu bah dole ya dau mataki.
A hnkli ya fara rarrashin umaima tmkar yace ta kara, bash dama yana da tausayi nan ya fara bata baki bayan ya cire handkerchief ya mika mata ta karba a hnkli tana share hawayen se kuma ta tuna hoton dad nata yana sharewa wata hawaye nan ta sake fashewa da sabon kuka.
Bash yayi shiru yana kallonta ya rasa me zai gaya mata
"Sorry pls is ok ki daina kuka ni na tsani ganin hawayen mace pls"
ta share hawayrn a hnkli ta daga kanta tana kallonsa shi ita yake kallo
"Tnk u"
"U ar welcom"
Ya fada yana murmushi sunyi shiru can ta tashi tace
"Zan koma ciki but pls ina bukatar num wayarka"
Babu gardama ya rubuta mata tana murmushi ta daga masa hannu sannan ta koma ckn gida shi kuwa yana mamakin chanjin halin nata.

Bash ya koma gida ya sami labarin cewa baba na nemansa a chan mubi saboda sa ranan aurensa don haka ya nemi ixini daga wajen aikinsa.
Shuairat tana kwance a falo tayi nisa ckn tunani wayarta ya hau ruri shukrah CE

"Kawata ya akayi"
"Uhmm...gani nan dai
"Baba yaxo Neman aure fah...

"Auren wa? Shuairat ta fada tana dariya
"Munafuka dama nasan kin San xe xo amma baki taba gaya min bah"

"Ya ake ciki "
"Oho! Nima bansani bah
"Gulma koh! Ana so ana kaiwa kasuwa kinsan yaya na mai tsada ne yarinya

"Kya ji dashi munafuka
"Ehh din, nasan ana son yaya na dai ana wani nokewa xamu gani ai"
Haka Suka cigaba da hira har na tsawon wani lokaci.
Bash yana kwance a falonsa ya kurawa wayarsa ido lambar shukrah CE kullum yana son kiranta Amma ya kasa, ga kwanakin se matsowa yake amma har yau be taba kiranta bah yau dai yayi ta maza ya danna kira yayi ringing har ya kusan katsewa sannan ta daga ckn wani irin murya mai dadin sauraro tayi sallama ya amsa se kuma yayi shiru

"Hello! Wa ke magana don Allah

"Yayanki ne
"Eyya..wanne daga cki
"Yaya bash
Nan taji wani irin kunya ta rufe ido tmkar yana ganinta dakyar tace

" ina yini yaya
"Lfy ya kike ya gida"
"Lfy alhamdulillh ya su mama"
"Lfynsu lau"
Nan Suka sake yin shiru chan ya fara magana
" kiyi hkri ban taba kiranki ba wllhi aikine ya rikeni"

"Ba matsala Allah ya taimaka"
" ameen nagode" nan ma shiru Suka yi bayan minti5 tace
"Hello!
" ina jinki"
" kayi shiru
"Ehh..kema ai shirun kika yi Kiban labari toh
" ba komi fah
"Ke baki da surutu ba kamar kawarki bah
Haka Suka Dan taba hira sannan sukayi sallama bayan ya sanar da ita gobe xai kama hanya da yardan ubangiji.

😘😘😘
...............muje xuwa
[2/21, 2:37 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*19*
By *Reefat yahya*

Bayan bash ya nemi ixini a ofishin shugabankasa aka bashi kwana3 nan yabi jirgin 12 ya sauka a *yola international airport* daga nan ya shiga motar xuwa mubi.
Karfe 4:00pm ya sauka daga ckn adaidaita a kofar gidansu daga shi sai akwati, baba yana xaune yana lazimi bash ya shigo tare da sallama bayan sun gaisa yayi salla sannan ya watsa ruwa nan ya shaidawa baba zai je gun shukrah.

A kofar gidan ya tura a kirata yaron ya dawo ance ya shiga cki, a wani daki aka saukeshi babu komi a ciki sai tabarma da kuma wata ya'r darmuma.
Kannenta ne Suka shigo da kwanikan abinci bayan sun gaisa Suka bashi waje bayan kankanin lokaci ta shigo tare da sallama wani uban qamshin turare ne ya buga hancinsa habawa ya daga kai Suka hada ido tayi kyau sosai ckn atamfar Sheraton dama tana da Dan jiki dinkin yayi mata kyau sosai.
Bash ya kasa cire idanunsa a kanta ita kuma kunyarsa take ji

" ina yini" ta fada ckn siririyar murya murmushi yayi ya fara kwaikwayon muryarta
gaba daya Suka fashe da dariya
" na sameku lfy
"Lfy alhamdulillh ya hanya
"Lfy lau
" ka sha ruwa se ka ci abinci nasan ka gaji sosai

Bata jira amsar sa ba ta bude kulolin abincin rice n stew ne se kuma danwake yasha hadi har da kwai da cabbage se kuma farfesun kayan ciki..

"Wanne zaa fara xubawa
"Ni danwake kawai xan ci
"Haba ka isa?
"Y not" ya fada yana murmushi

" Allah baka isa ba sai ka cinye duka

" haba shukrah kema dai kinsan baxan Iya cinye wannan ba"

Baya CE komi ba ta diba masa danwaken dama shuairat ta gaya mata yaya bash na balain son danwake, ta ajiye a gabansa sannan ta xuba zobo a ckn Kofi ta tura masa a gefe ya daga kai Suka kalli juna yace

"Sai ki matso muci tare ai"
" a koshe nake"
" no! Ki xo mu ci"
" a'ah naci nawa tun dazu"

Murmushi kawai yYi ya hau ci a hnkli yake kominsa gwanin burgewa shukrah tana satar kallonsa guy din ya hadu😜
Carab ya kamata tana satar kallo ya murmusa yace

" ya dai"
" ba komi"
" ki fadi gaskiya"
Ta rufe fuska ckn jin kunya tace

"Zan koma ckn gida idan ka gama ka kirani a waya"

" no! Kiyi xamanki ni bana jin kunya ai kece me jin kunyana"

Tana dariya ta kawar da fuska a gefe.
Bayan ya gama cin danwaken yana santi yace

" wannan girkin inna koh? Nasan naki bare kai wannan dadi bah"

"Naji na yarda"ya shanye zobon ma yaji ya koshi yayi hamdala ya juya suna fusksntar juna sosai nan Suka fara magana ta fahimtar juna ya nemi jin raayinta game da auren nasu ita tace duk yadda sukayi ya mata daidai bata da zabi .

Haka Suka kasance har magrib sannan ya mata sallama ya tashi ya tafi kamar karsu rabu sabida dan xaman da sukayi sun fara sabawa da juna.
[2/21, 2:37 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*20*
By *Reefat yahya*

Dakin ya cika makil da jamaa daga ministoci senators members da dai sauransu mr Joshua yana xaune wato vice president kenan ga bodyguards a gefensa ta kowane bangare.
Idan ka duba wani bangare kuma yan jarida ne birjik ga maaikatan yada labarai dai daban daban ana jiran fitowar mr President , ya fito kuwa ckn manyan kaya yayi kyau sosai fuskarsa ba yabo ba fallasa yana taku ckn kasaita yana wani ji da kai tamkar sarki 😜😜( lols me banbancin)
Ya nemi kujera ya xauna nan wani mutum ya fara magana yana murmushi daga ganinsa yana jin dadin yanayin da yaga mr President a ciki....

"Mr president yau ne karo na karshe da xamu maka wannan tambayar...me hadinka da wannan yarinyar?
Shiru ba amsa ya maimaita maganar sau3 ko uffan mr President bai tanka masa bah
Nan aka fara hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa..

" muna ganinka mutumin arxiki shiyasa muka baka wannan matsayin Amma ka kunyatar damu ...
Wani dattijo ne ya fadi haka yana rike da speaker.mr president ya runtse ido yana jin wani irin radadi a ckn xuciyarsa dakyar yake furta sunayen Allah.

"Silence" wata siririyar murya ta fada da karfi sanye take ckn wani gown me kyawun gaske black da adon pink tayi rolling da pink veil ta sa lipstick pink Dan kadan tayi kyau sosai.

Wal wal hasken camera kawai kake gani anata daukanta hotuna gaba daya hnklan jamaa ya koma kanta ta karbi speaker ta fara cewa
Chapter 8 · 0% Book details