← Book details Sauyin Lamari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 12

Sashe 7

Sauyin Lamari Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gama fad'in haka ta wuce fuu ta bar gidan rai a matuƙar b'ace. Hannu Asiya ta d'ura a ka tana wani irin kuka. Bazata bar gidannan ba dole tasan yanda tayi Moha ya yi hak'uri ya zauna da ita. Yaushe zata bar wannan dukiya. Juyawa tayi zata koma ciki sai wuff taga wasi manya sojoji da suka shigo gidan yanzu sun tare k'ofar. Tanaji taja gani suka hanata shiga bare ta d'auko ko wayarta ne. Daga bisani sukayi mata korar k'are. Umarnin da Moha ya basu kenan.

Tunda suka fice daga gidan Jadwah ke zubda hawaye a hankali. Duk sai taji tausayin Mohan ya kamata. Gaba d'aya tunda suka shiva motar yake sauke wata irin ajiyar zuciya ta tsananin b'acin rai. Ace mata har biyu amma babu wacce ka samu nutsuwa da kwanciyar hankali da ita. Tana kallon yanda ya koma ya jingina jikin kujera ya lumshe manyan idonsa yana sauke wani wahalallen numfashi. Wani had'edd'en gidan suka shiga daya ci uwar wanda suka baro. Da sauri ya fice ya zagayo ya buɗe mota motar ta fito a hankali tana kallan sa. Hannun ta ya kama suka shiga. Kamshi da sanyi ya ratsa ta har saida ta lumshe ido. Suna shiga k'aton falon da aka k'awata ya juyo da sauri ya rungume ta tsam cikin k'irjin sa. Numfashi ta sauke a hankali ta d'aga hannu ta d'ura bayansa tana d'an bugawa kaman yanda akewa yara idan suna kuka. K'ara matse ta ya yi cikin k'irjin sa yana jin wata irin nutsuwana ratsa shi. Sun jima a tsaye kafin ya janye daga jikin ta ya sureta chak ya haura saman had'edd'en glass stairs dake falon. Wani had'edd'en d'aki ya shiga da komai nasi fari ne tas. Kan makeken gadon ya kwantar da ita da aka kewaye da labule tsakiyar sa harda fitila mai masifar kyau. Koma shima ya yi ya kwanta k'irjinta gaba d'aya ya sakar mata nauyinsa. A tare suka sauke ajiyar zuciya ita ta wahala shita samun nutsuwa sa ya yi. Babu wanda ke tattare da yunwa cikin su don sunci sunyi nak.

Babu abunda ka ke ji a d'akin sai sautin bugun zuciyoyin su da dake tashi cikin d'akin. Na Jadwah yafi k'arfi don ita harda tsoro da nauyin sa gaba d'aya daya sake mata. Sun jima a haka taji numfashin sa ya fara sauka a hankali alamun ya samu barci. Sai alokacin ta iya sauke doguwar ajiyar zuciya tana d'an k'ok'arin tureshi. Ai wani iri k'ara matseta ya yi ya k'ara tura kai tsakiyar k'irjin ta . Numfashi kawai ta sauke tana kallon sa da yanda yake wani abu sak na shagwaɓabbu. Kai kawai ta jinjina barci ya fara fisgar. Addu'a tayi musu ya shafa musu haka tayi barci a wahalce.

Ina Balaraba?. Tunda labarin cin zaban Daddy ya riske ta take ta rusa kuka kaman wacce aka aikowa da sakon mutuwarta. Sosai tayi nadaman abubuwan data aikata tana inama ace ana dawo da hannun agogo baya. Suwaiba ta daina jinta ko labarin ta bataji. Ita dai batayi sa'ar haihuwa ba. Daga Asiya har Isma'il babu wanda ya lek'o ta. Shi Isma'il ma da yake nan kusa da ita. Yana can d'akin yan matansa a kwana ana cin mace da Shaye-shaye wanda yanzu harta fara tab'a masa kwakwalwa ya zama kaman mara hankali-hankali. Wata k'ila da tayi hak'uri ta zauna da Daddy da zuciya d'aya tasan da ,da ita za'a samu wannan cigaba. Bata da kowa sai Allah yanzu. Tasan kuma a halin da take yanzu na musaka babu k'afafu babu lallai Daddy ya cigaba da zama da ita. Duk da cewa yaba bata kulawa yanda ya dace amma rabon data sashi a ido tun fitar da ita da ya yi aka yanke k'afar ka dawo da ita.

36/40

Ina Amina?
Tunda Jild'e suka tsinci ta suke bata taimakon gaggawa na jike-jiken su da turaruruka. Amina bata farka ba sai washegari. Lokacin data farka bata iya cewa komai sai aikin kuka kaman ranta zai fita. Nadama da dana sani ta rufeta ta ko kuna. Tsananin tashin hankali da damuwar da take ciki lokaci guda duk ta fice hayyacin ta. Jild'e da matarsa Barira sosai suke iya bakin k'ok'arin su wajen ganin ta samu lfy. Kwanan Amina biyu a rugarsu Jild'e. Gana d'aya hankalin ta da nutsuwar ta ya yi gida ne . Ko ansan ta b'ata yanzu. Moha ya sani. Idan takoma me zatace musu?. Saudat na raye ko sun kasheta?. Ranan da tayi kwana uku ta tambayi Barira ina take inda take ce mata ai an fita daga Bauchi. Hankalin Amina ya k'ara tashi. Tana kuka ta dinga rokonsu su barta ta koma gida wajen y'an uwanta. Tasan yanzu hankali duk ya tashi babu wanda yasan inda take. Babu musu Jild'e ya tattara y'an kuɗin sa na noma shka rako Amina har tasha da zata koma cikin Bauchi. Sosai Amina ke musu Addu'a da godiyar taimako da sukayi mata gashi babu yanda zatayi ta saka musu. Jild'e ya yi murmushi yace

"Na taimake ki ne saboda Allah badan ki sakamin da wani abu ba. Allah ya k'ara kiyaye gana ya sauke ki lfy"

Jikin Amina ya k'ara sanyi hawaye suka cigaba da gudu kan fuskar ta. Tayi nadama, tayi nadam. Jild'e da matarsa suj k'ara sa mata wani irin tsoron Allah. Ji take idan ta koma gida babu abunda zata b'oye na munannan aiyukan data aikata. Wata k'ila idan tayi hakan ta samu sassaucin halin data shiga. Wajen azahar lis dan sahu ya sauke Amina k'ofar gidan su. Daidai Huzaifa na fito da Mahaifin su da wani d'an sanda gefen su. Turus suka tsaya suna kallon Amina da duk ta fice hayyacin ta. Wani irin kuka ta fashe dashi tayi kan mahaifin ta ta rungume tana kuka sosai. Huzaifa shiya sallami d'an sahun yaja ya tafi. Ciki suka shiga da Amina ,Hajiya Fati dake zaune falo da Yayyan mata biyu cikin matsanancin tashin hankali. Batan Amina ya riske su jiya da suka je gidan babu kowa. Maigadi yace ai sun fita ida da Saudat tun ranan da aka kawo ta gidan. Abun kaman wasa aka nemi Amina ko sama ko k'asa an rasa. Ga duka wayoyin su a kashe ita da Saudat. Hankula suka fara tashi mahaifin Amina tuni suka garzaya police station don bada sallahon b'atan Amina. Huzaifa ya d'aga waya zai kira Moha mahaifin su yace a dakata tukun sai an samo Amina koma mene sai yaji daga baya.

Shigowar Amina da mahaifin nasu yaja hankalin su suka miƙe suna salati. A guje Amina ta zube jikin Hajiya Fati tana wani irin kuka.

"Innalilllahi Amina. Meya same ki haka?"

Hajiya Fati tace tana duban Amina da duk ta fice hayyacin ta. D'an sand'an da suka tare da Mahaifin su ya matso yana cewa

"Hajiya Amina ko zaki iya gaya mana abunda ya faru don muyi bincike?"

Jikin Amina ya fara rawa. Zamewa tayi ta durkusa tana gursheken kuka. Yau dubunta ya cika. Jiki na rawa ta fara zayyano abunda ya ru tiryan-tiryan tin farko zuwanta wajen Jalli. Da yanda ta samu Moha harta aure shi, da yanda suka tafi ita da Saudat don k'ara had'a wani tuggun da iri mummunan k'addara data same sh. Bata gama rufe baki ba taji wani irin mahaukacin duka ta ko ina da waya. Ihu take sosai tana bawa mahaifin nata hak'uri. Daga Hajiya Fati har yayyenta dake d'akin babu wanda ya yi yunƙurin hanashi saima kuka da suke suna mamakin wannan rayuwa da y'ar tasu ta fad'a. Saida ya yi mata lilis d'an sanda yana k'ok'arin hanashi Huzaifa zai tare shi. Kallon Huzaifa ya yi yana huci yace

"D'auko min ita Huzaifa "

Babu musu ya ciccibi Amina dake numfashi da kyar ya yi waje da ita. Mota ya sata suka bar gidan. Can wani kauye kayau suka kaita ya bawa wani babban mutum ita yace ya ajiye masa ita har sau ta koyi hankali. A bata dukkanin wani aiki na wahala ta dinga yi. Amina tayi kuka tayi kuka kaman zata shid'e . Tana kallo Huzaifa da Mahaifin ta suka tafi suka barta a nan. B'angaren y'an sanda sunyi nasarar bin hanyar da Amina tace sun kuma samo gidan. Sun jima suna misayar wuta da y'an indiganan nan da suka addabi rayuwar al'umma. Saida suka kashe kusan rabinsu Allah ya basu nasara suka kame ragowar harda ogan su. Nan suka iske Saudat da babu yanda take. Bayan sun fuskanci bata mutu ba suka dawo da ita suna yin yanda sukaga dama ta ita. Taimakon gaggawa aka bawa Saudat bayan kaita asibiti da akayi. Y'an uwata suka zo cikin matsanancin tashin hankali da jamamin abunda ke faruwa. Saudat kwanan ta uku a asibiti tace ga garinku nan. Allah yasa mu cika da imani.

Mahaifin Amina na dawowa ko takan Hajiya Fati da yayyenta baibi bare ya gaya musu inda ya kai Amina. Ya dai ce musu

"Na kaita inda zata k'ara koyar hankali. Tunda har ta bari son zuciya da sharrin shed'an ya yi galaba a kanta. Dole ta girbi abunda ta shuka. Zan kira yaron na gaya masa dukkanin abunda tayi. Idan yaga zai iya zama da ita cikin wannan yanayin da irin mugun kullin da tayi masa harya aureta falillahilhamdu. Idan bazai iya zama da ita ba sai ya sake ta. Ai ba kanta aka fara zawarci ba"

Yana gama fad'in haka ya wuce su fuu cikin matsanancin b'acin rai. H Fati ta cigaba da kuka sosai. Wannan wace irin kaddara ce?. Ace daga yin aure ko sati ba'a yi ba ,aure ya mutu. Kai Amina bata kyauta wa kanta ba da ta bari rayuwar ta ta lalace da kuruciyar ta.

UK

18+

Sanyin asuba da kiranda wayarta yake yasa ta farka. A hankali ta buɗe idonta tana kallon fitilar dake tsakiyar gadon dake kawo haske kala-kala. Nauyin da taji a kanta ya k'ara tabbatar mata har yanzu Moha na kwance kanta. Wnai gauren numfashi ta sauke a wahalce tace.

"Ya Moha"

Murmushi kawai ya yi don ya dad'e da farkawa. Manyan idonsa ya buɗe ya d'an d'ago yana kallon ta. A wahalce ta k'arasa cewa
Chapter 7 · 0% Book details