← Book details Sauyin Lamari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 12

Sashe 10

Sauyin Lamari Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Damuwa tayi mata yawa taci buri da alwashi inhar ta fito sai taga bayan Jadwah da Moha da suka jefata cikin wannan hali ,saidai bataje ko ina ba ta fara wani irn ciwon mara. Da fari ta dauka abun wasa ne saida taji gabanta na wani irin zafi da rad'ad'i kaman ana zuba mata barkono. A wahalce tayi kan masansu dake cikin dakin tana k'ok'arin cire wando. Tana cirewa kuwa wani irin wari da ruwa ya biyo kafuwan ta shar kaman mai yoyon fitsari. Ihu ta saki saboda wata irin azaba da taji kaman ana zare mata rai. Abu taji tsananin cinyoyinta ya yawi ta kai hannu jiki na rawa ta duba saiga wasu katun-katun tsotsi. Wani irin gigitaccen ihu ta saka daya ja hankali masu tsaron cell d'in suka nufoshi da guje daidai tana zubewa k'asa a sume. Abokiyar zaman cell d'in nata tayi kanta tana salati.

46-50

Not edited.

Sati d'aya kenan da fara zuwan Jadwah jami'ar Oxford. Cikin d'an k'ank'anin lokaci ta saba da mutane musamman yanda take da kwakwalwa. Dukkanin wani miss da tayi na semester d'in ta tarar dasu. Kaman koda yaushe yanda ya saba kawota yauma fakin ya yi harabar makaranta dake cike da dalibai suna tai kawo. Da yawan su had'addiyar motar taja hankalin su suka zuba mata ido harda masu d'aukan hoton ta. Wani irin kallo yakewa Jadwah da yasa matsanancin kunya ya kamata tayi saurin kauda kai tana kallon mutanen dake ta yawo a gurin. Numfashi ya fesar a hankali ya yi d'an murmushi mai sauti yace

"Har yanzu baki ce komai ba. Na baki suprise gobe zamuje kiga Gwagwo da Baba da ake sa ran sallaman sa this week. "

Baki ta d'an turo a shagwaɓe tace "to ai kai ne"

"Ni ne me?"

Yace wana wani murmushi ya k'ara matsowa kusa da ita. "Hmm"

Baki ta k'ara turowa tace " ba kaine ba kane sai na baka wani abu"

"Yes Baby. Nothing comes on a silver plate. Dole ki bani reward"

K'ara turo baki tayi tana d'an k'unk'uni da sakin murmushi. Idan ta cigaba da biye masa a nan zasuyi ta zama kuma tana da test. Kunya ta cire ta juyo ta kalleshi kaman yanda ya zuba mata mayun idonsa. Ganin yanda fuskar ke gabda tata ta d'anja baya tana kallonsa. Murmushi ta k'arayi ta matso da sauri ta sumbaci bakinsa. Ido ya zuba mata yana kallonta da gira a d'age.

"Me ke nan?"

Zumbura baki tayi " reward naka mana"

Dariya ya yi " No. Baki isa ba. I need to feel your mouth. All of it"

Numfashi ta fesar a hankali ta kalli waje inda ta hango Ava da Kate tsaye suna jiranta. Juyowa tayi ta kalli Moha daya d'aga mata gira. Hannu ta miƙa ta kama fuskarsa tana matso da tata. Sannu a hankali ta hade bakin su da wani irin deep french kiss. Tuni notin kan Moha ya kwance sai jinsa kawai tayi a kanta ya mata rumfa yana wani irin tsotsan bakinta kaman zai cinye. Tsawon minti biyar suka d'auka a haka kafin ta kwace bakinta jin hannun sa da tayi cikin rigar ta ya kama k'irjin ta. Ido ta d'an zaro tana kallon yanda nashi suka chanza launi.

"Ka manta inda muke ne? A waje fa muke."

Numfashi yaja murya a tsarke yace " and so what? Su meya dame su. I tell you they will be very pleased to watch us. "
Kai ta jinjina tana k'ok'arin tureshi a jikin sunkuyo ya yi ya k'ara bata quick kiss kafin ya koma kujerar sa ya zauna yana kallonta da murmushi kan fuskar. Shi Sam baya gajiya. Yau kusan awa uku cur ya yi a kanta tun asuba saida garin Allah ya waye, amma yanzu ma wani yake nema. Har yanzu ta kasa sabawa da girman sa. Tana jin yanda yake poking kafafuwanta alamun yana neman abinci. Bata kalleshi ba ta kama murfin motar ta fice tana jin idon. Kai tsaye tayi wajen su Ava dake ta jiranta d'an kunya ya kamata ganin sunayi mata knowing look.

"Oh My God"

Taji muryar Kate tayi saurin kallon taga yanda ta zare ido tana kallon bayan ta. A hankali ta juya ta kalli Moha dake jikin motar ya kafeta da manyan Blue eye's nashi. Ai tuni mata suka fara tura k'irji ana jefansa da wani flirtatious kallo. Kishi ya rufe Jadwah ta koma da sauri inda yake tsaye fuska a had'e tace

"Tsayuwar me ka ke kuma? Ka tafi mana"

Ido ya zuba mata yana murmushi. Wani irin farin ciki na ratsa shi saboda kishin da yake gani kwayar idon ta. Matsawa ya yi daga jikin motar ya matso gabanta inda ta harde hannu sai zuna harara take duk inda idanta ya fad'a. Ita kanta bata san tana hakan ba. Sunkuyawa ya yi daidai saitin fuskar ta ya sumbaci goshinta da kuncin tare da furta

"I love you"

Murmushi tayi cike da y'ar kunya ta tura shi ya tafi yana murmushi ranshi fes. Saida taga yabar cikin makaranta sannan ta sauke numfashi wata matsananciyar kunya ta rufeta jin idanuwan mutane a kanta. Ihun Ava da Kate taji da sukayo kanta a guje suka rungume suna ihu.

"Damn girl. That you're husband?, why can't i found someone just like him?. Damn his to hot. He look like someone who just came out straight from Novel"

Dariya Jadwah tayi duk da kishin dake cinta. Su gama fantasies nasu Moha nata ne ita kad'ai.

Murmushi kawai yake yana hasko kishin sa dake kwance cikin kwayar idon ta. Wayarsa data hau k'ara ta katse masa tunani. Number da yaga na kiransa yasa shi cikin mamaki. Tunda ya auri Amina bai tab'a kira yaji ya take ba. Fakin motar ya yi gefen titi ya d'aga wayar cikin girmawawa. Gaisawa suka farayi da mahaifin Amina kafin ya kwashe dukkanin abubuwan da suka faru ya sanar da Moha. Wani irin shiru Moha ya yi kaman wanda ruwa ya cinye. Allah mai iko. Maganan gaskiya tunda yaji wannan abu bazai iya cigaba da zama da ita ba. Shi dama yana ta tunanin hanyar da zaibi ya yakice ta. Inhar yace zai cigaba da zama da ita to tabbas zai cutar da ita. Numfashi ya fesar a hankali yace

"Baba kayi hak'uri, amma bazan iya cigaba da zama da Amina ba. Na sake ta saki d'aya. Allah ya zaba mata mafi alkhairi "

"Babu komai Muhammadu. Duk wani uba na kwarai bazai so ka zauna da y'ar sa cikin wannan hali ba. Allah ya yi maka albarka kaji. Ka gaidamin da mahaifin naka da matar ka"

"InshaAllahu Baba"

Wani irin sauke Numfashi ya yi ji yake kaman an sauke masa dukkanin wani damuwa da yake ciki. Alhamdulillah. Abunda yake iya furtawa kenan cikin ransa. Ummi ya bata kusa sai Gwagwo ce ta d'auka. Bai b'oye mata komai ya kwashe ya gaya mata yanda sukayi da Mahaifin Amina. Sosai Gwagwo tayi mamaki dayi masa Addu'a. Kafin suyi sallama ya kashe wayar.

B'angaren Gwagwo , Ummi na fitowa tare da Daddy ta tare su da zanjen. Suma sunyi matukar mamakin jin wannan abun. Daga Daddy har Ummi babu wanda baiyi hamdala cikin ransa da Allah yasa Moha bai kusanci Amina, auren nasu yazo k'arshe tun ba'aje ko ina ba. Ga Asiya ma daya kira ya sanar dasu abunda suka iske tanayi da hukunci daya yanke mata. Tabbas Jadwah ita ce alkhairi sa. Yanzu fatansu su gansu da jikoki.

Sai yamma likis Jadwah tayi masa yawa. Tuni yana bakin makaranta ya k'arasa. A gajiye ta shiga motar tana kallon Moha dake zuja wani uban kamshi. Sanye yake da farar riga da bakin wando gashin kansa a tufke tsakiyar kansa sai yan silli-silli da suka zubo gefen fuskarsa dake d'auke da farin glass. Fad'an matsanancin kyau da ya yi abun bazai kwatantu. Ido ta zuba masa yana kasheta da blue eyes nashi. Murmushi kawai ya yi ya tashi motar suka bar cikin makarantar. Saida ya fara wucewa dasu KFC ya yi order abinci sannan ya juya suka koma gida. Sallah Jadwah ta farayi sannan taci abincin ta miƙe cikin kujera. Kwanukan ya kwashe ya kai kitchen ya wanka kafin ya dawo ya d'aga ta ya shige kujerar ya kwantar da ita kan k'irjin sa yana shafa bayanta a hankali. Ba ita ta farka ba sai magriba ta miƙe tana mik'a. Cikin kunne yace mata suje suyi salla bata musa ba ta miƙe tsaye ya tashi ya d'auke chak ya haura sama. Saida ya fara wanke tas ya naduta cikin tawul ya fito ya shafeta da turaruruka masu kamshibya saka mata y'ar k'aramar riga ta shan iska data tsaya mata iya gwiwa. Pant kawai yasa mata babu bra. Itama bata damu ba don kwana biyu sosai take damunta ga wani irin cika da k'irjin nata ya k'ara. Basu tashi daga kan dadduma ba saida akayi sallan isha suna ta tilawa da muryoyinsu mai tsananin zaki da gard'i.

Suna shafawa ya Mike ya fice. Miƙe tayi itama tana k'ok'arin hayewa gado ta kwanta tana tufke gashinta. Karar Moha taji kaman wanda ya yi wata mugun fad'uwa. Ai a guje Jadwah ta fito tana kiransa. Kafin ta kai k'afar bene taji ya rik'o ta yana y'ar dariya. Saurin juyowa tayi tana kallon. Ganinsa lafiya lau ta kai masa duka yana kaucewa yana dariya. Da bango ya had'ata yana cewa

"Baby. Haka ki ke sona?"
Chapter 10 · 0% Book details