Sashe 6
Sauyin Lamari Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ya tura k'ofar d'akin ya shiga. Can kan gadon ya hango ta kundune sai sharar barci take hankali kwance. Murmushi ya yi ya nufi gefen gadon ya zauna kusa da kanta yana k'arewa kyakkyawar fuskar ta kallo. Gata so innocent. Hannu ya mik'a a hankali ya tattare gashin kanta daya zubo mata gefen fuska ya rufe. Murmushi ya k'arayi ya miƙe tsaye. Farar rigar dake jikin sa ya cire ya haye gadon daga shi sai dogon wando dake jikinsa. D'aukan ta ya yi chak ya d'ura kan faffaɗan k'irjinsa ya matse yana shafa dogon gashinta zuwa gadon bayanta. Sannu a hankali barci ya fara fisgar sa yana shak'ar masifaffen kamshi da kanta yake mai shegen dad'i.
Jadwah bata san meke wakana kusa da ita. Saboda gajiya da yanda take jinta kan wani abu mai tsananin laushi da kamshi yasa ta k'ara shige masa ta cigaba da barcinta hankali kwance ya k'ara matseta yana murmushi. Basu suka farka ba sai wajen azahar. Shiya fara farkawa saboda jin muryar Ammi daga can bakin k'ofa tana kwala masa kira. Murmushi ya yi yana kallon k'ofar duk da cewa a buɗe take amma bata shigo. Motsin Jadwah da yaji a jikinsa ya maida hankali kanta tana k'ok'arin buɗe ido. A hankali t buɗe su kan k'irjin Moha da take kwance. Wani irin zare ido tayi da d'ago da kanta idanta ya fad'a cikin nashi. Bata san sanda tayi wani wuntsule ba ta dire gefe tana kallon da zararrun ido k'irjin ta na matsanancin bugawa. Garin ya hakan ta kasance bata sani ba. Hannunsa yasa ya talleb'e k'eyarsa yana mata wani irin kallo tun daga sama har k'asa. A firgice ta juya k'ofa da taji Ammi na kwala masa kira tana cewa zata shigo.
Ganin yanda duk ta rude yasa saki wani d'an murmushi ya miƙe ya d'auki rigarsa yasa yana kallonta. Matsowa kusa da ita ya yi tayi saurin ja da baya. Ya k'ara wani murmushin ya wuce ya buɗe k'ofar ya fice. Aikuwa yana fitowa yaci karo da Ammi dake jiransa. Kunnensa ta kama kaman yanda larabawa suke tana masa fad'a. Shida banda dariya babu abunda yake har da cire d'an takarmi ta kwad'a masa ya fisge a guje ya yi k'asa yana mata dariya harda gwalo. Kai Ammi ta jinjina tana murmushi ta tura k'ofar d'akin ta shiga. A tsaye taga Jadwah tayi tsuru-tsuru da ita. Gadon ta kalla taga babu abuda ya yi ta mayarda kallonta kan Jadwah taga itama kayanta ne a jikin. Saida ta k'ara k'are mata kallo ta tabbatar babu abunda ya faru tsakanin su taja y'ar ajiyar zuciya ta k'arasa shigow tana wa Jadwah murmushi. Yanzuma da kanta ta had'a mata ruwa tace taje tayi wanka. Kafin ta fito ta k'ara gyara d'akin ta kunna turaren wuta. Ammi badai tsabta ba. Ita ta shirya Jadwah bayan ta idar da sallan cikin wata had'addiyar abaya ashe da aka yiwa ado da wasu had'addun dutsawa kama daimon sai sheki suke. Hoda kawai ta shafa mata da d'an lipgloss ta yi mata irin nad'in su da suke na larabawa. Zo kaga kyan da Jadwah tayi sai kallon kanta take tana murmushi, Ammi na fesheta da turaruruka kala-kala masu sanyin kamshi. Hannun ta kama suka fito falon suka iska Daddy da Moha da suka shigo yanzu daga masallacin zaune kan Dinner suna jiran Ammi. Wani irin kallo Moha yabi Jadwah dashi harda lashe baki. Matsanancin kunya yasa ta sunkuyar da kai k'asa tana k'ara mamakin rashin kunyar sa. Kaman wanda ke gaban abokansa ba iyayen sa ba. Dariya Daddy kawai ya yi baice komai sai Ammi ce tayi masa dakuwa ya d'an turo baki yana k'unk'uni. Abinci sukaci mai rai da lafiya irin nasu na larabawa. Jadwah taci abincin babu laifi duk irin matsanancin kunya da takeji. Bayan sun gama ta kira Gwagwo sun jima suna waya har Ammi ta bawa suka dinga waya da Gwagwo kaman wanda suka shekara da sanin juna. Ita dai Jadwah na zaune kan kujera tana murmushi tana jin idan Moha dake zaune kujerar dake fuskantar a kanta. Daddy zaune kusa dashi suna maganan siyaya.
Satin Jadwah biyu a Dubai. Ammi ta kasa ta tsare Moha kad'ai cewa da ita. Don sosai take yiwa Jadwah wani mahaukacin gyara irin nasu na larabawa. Moha ya cika fam kaman zaiyi bindiga. Saboda yanza Ammi ta kasa ta tsare ya daina zama sosai a gidan. Ga kuma yanayin zabe dake k'ara gabatowa. Yau asabar garin Dubai ya d'auka da murna da farin cikin samun nasarar hawa kujera da Daddy ya yi. Duk inda ka wuce za kaga ana murna da celebration. B'angaren Moha da Daddy kuwa abun ba'a cewa komai ranan mutane da sukayi cincirindo a gidan abun sai wanda ya gani. Y'an uwa da abokan Arziƙi kaf babu wanda bai hallara ba. Moha takanas yasa aka d'auko Gwagwo. Sai wayar gari Jadwah tayi da Gwagwo a gidan. Murna da farin ciki abun ba'a cewa komai. Gwagwo da Ammi suka k'ara d'inkewa. Kwanan Gwagwo biyu suka rankawaya gaba d'aya Saudi har Gwagwo do sauke farali. Addu'a sosai sukayi kan wannan Mulki da Daddy ya hau. Allah ya bashi ikon sauke hakkin daya rataya a wuyansa ya bashi ikon Adalci. Saida sukayi sati a Saudi sannan suka wuce ENGLAND wajen Baba. Kai ranan duk wani masoyin Jadwah da Gwagwo saida ya zubar musu da hawaye. Haka suka rungume Baba da suka tarar idonsa biyu suna ta kuka shima saida ya zubda hawaye. Farin ciki ya yi masa yawa ya sake ganin Jadwah da Gwagwo bayan wasu y'an lukata. Kwana biyu sukayo wajen Baba kaman zasu had'iye shi. Sosai suke bashi kulawa bayan wadda likitoci suke masa. Ranan da suka cika kwana uku Daddy ya koma Dubai su kuma sai washegari Gwagwo da Ammi suka wace Dubai d'in. Dan Ammi tace k'afarta k'afar Gwagwo. Nan suka bar Jadwah da Moha sukaci gaba da bashi kulawa. Saida sukayi sati guda Cur Moha ya shirya musu wuce UK.
Ranan kwana Jadwah tayi tana kuka ita babu inda zata. Saida Baba ya yi ta lallashinta da bata baki. Jikinsa alhamdulillah an samu cigaba sosai da sosai. Dan yanzu yana iya tashi da kansa ya d'an taka ya yi sallah. Kwana ranan Jadwah tayi k'irjin Baba, Moha ya sasu a gaba da kallon su yana murmushi. Washegari k'arfe takwas daidai suka bar ENGLAND. har jirgin ya d'aga Jadwah kuka sosai. Sai matseta ya yi cikin k'irjin sa baice mata komai baya barta tana ta kuka har barci ya nauketa. Iska ya hura mata kan fuska ta d'anyi motsi a hankali ta fara buɗe idonta. Dashi taci arba yana mata murmushi. A hankali takai dubanta ta jikinta taga yanda taje zaune d'are -d'are kan cinyarsa. Wai me yasa yake son ganin ya d'urata a jikinsa ne?. Da sauri ta zame ta zauna tana kallon window. Sautin murmushin sa taji ya miƙe yana cewa
"Mun iso Baby "
Bata kalleshi ba ta miƙe a hankali tabi bayansa suka fito daga cikin jirgin. Garin duhu sosai sabanin sanda suka taso daga UK. Had'addiyar Limo dake fake gaban jirgin wajen Biyar suka shiga guda da tafi ko wacce kyau. Tunda suka shiga tak'i kallon sa duk yanda take jinsa idonsa. Jin idansa take har cikin bargon jikinta. Y'ar tafiya sukayi kaman ta minti talatin kafin su tsaya k'ofa wani had'edd'en gate dake d'auke da wai moder house mai kyan gaske. Gidan bashi da wani girma amma an kashe masa dukiya .ciki da wajensa da glass akayi. Motarsu na fakin ya buɗe da sauri ya ficeya zagaya ya buɗe mata. A hankali ta fito tana kallon kayataccen gida. Gana ya yi tana binsa a baya har k'ofar porch na gidan da akayi da glass. Tana kallo ya danna wasu password jikin k'ofar ta buɗe a hankali kafin ya juyo ya kalleta yaba murmushi yace
"Ladies first "
D'an murmushi tayi ta wuce shi a hankali ta shiga bakin ta da y'ar siririyar sallama. Mugun birki taci ta kasa k'arasa sallaman da takeyi ta zaro ido d'an k'aramin ihu da salati ya maye sallaman tata.
A hanzarce ya shigo yana cewa "Menene what happ..?"
Maganan ta mak'ale shima ya zare ido yana kallon Asiya da Jojo dake kwance tsakiyar falon haihuwar uwarsu. Ihun Jadwah yasa suka dawo daga duniyar sa suka lula hankali tashe suka miƙe suna neman suturta kansu. Hankalin Asiya ya yi masifar tashi ganin Moha da tayi unexpected gashi ya ganta cikin wannan mummunan hali ita da Jojo. Jiki na rawa suka fara saka kaya. Idon Moha da sukayi wani irin mugun jaa kaman garwashi yake kallon su dasu ransa a matuƙar bace. Wannan wace irin masifa ce. Shi wlh harga Allah ya manta da wata Asiya. Bai tab'a tunanin tana nan ba. Da yasan tana nan tana yi masa irin wannan kazantar a gida da tuni ya sa anyi mata korar kare. Jikisa har wani tsuma yake saboda b'acin rai kalma data fito bakinsa kuwa tafi komai muni.
"Na sake ki saki uku. Ki tattara barmin gida nan da minti biyu"
Wayyo wani irin ihu da kururuwa Asiya tayi ta nufoshi a guje ya watsamata wani mugun kallo taci burki taja gunjin kuka. Jadwah dake b'oye a bayansa ya ja hannun ta suka fito daga gidan sai kuka take tana tur da wannan rayuwa. Mota ya jefata shima ya shiga daidai Asiya na k'arasowa tana wani irin kuka ya fisge motar a guje ya bar gidan. Zubewa tayi a gurin tana kuka sosai ta shiga uku. Bata san cewa tana son Moha ba sai yanzu data rasashi.
Jojo dake tsaye bakin ciki kaman zai kashe ta. Mugun tsaki taja ta wuce fuu zata fice daga gidan cikin matsanancin b'acin rai. Asiya tayi saurin riƙe ta tana kuka tace
"Ina kuma zaki tafi ki barni cikin wannan halin"
Ran Jojo a matuƙar b'ace tace da turanci " bazan zama second option naki ba saboda mijinki ya rabu dake yanzu. Tuntuni nasan cewa dama ni kad'ai ke sonki. Ni kad'ai zan iya bada komai nawa saboda ke. Saboda haka na gaji ,banza cigaba da zama dake matsayin option ba"