Sashe 1
Sauyin Lamari Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
𝐏𝐆 15/20.
A d'aure a riƙe amana banda share fisabilillahi🙏.
Gidan su ya fara nufa kai tsaye daga bakin gate yaci karo da Isma'il dake k'ok'arin fitowa da muto. A hanzarce ya fice da sauri ya nufi Isma'il yana kira. Da tsananin b'acin rai Isma'il yace
"Lfy zaka rufemin hanya?"
"Ina ne gidan H Suwaiba?"
"Wace Suwaiba kuma?"
Kallo Moha ya watsa masa da babu shiri ya bashi address na gidan ya juya a sukwanne ya fad'a mota Lameen ya fisge ta da sauri.
B'angaren Suwaiba tana ganin shigar Jadwah ta yi bakin k'ofar tana bugawa daga baya ta fice ta kira maigadin yazo ya balle k'ofar. Babu b'ata lokaci mai gadi ya shigo ya fara dukan k'ofar da Suwaiba tace ta rufe yarinya ne an kasa buɗewa. Gigitaccen ihu Jadwah tasa ta tashi a guje tayi toilet ta garkame k'ofar tana kuka k'ank'ame da wayarta da ta mutu babu chaji. Allah ya kawo mata d'auki ya k'ubutar da ita daga sharrin wannan mata. Saura kad'an k'ofar ta fita daga jikin hinge nata Moha ya fad'o cikin falon kaman mahaukaci yana kwalawa Jadwah kira. A firgice Suwaiba take kallon Moha da matsanancin tsoro kwance kan fuskarta. Saboda yanda hankalin sa ya yi kan Jadwah bai tsaya ta kan Suwaiba ba ya fara bincike a gidan da kiran sunan Jadwah. Lameen ya shigo daga baya yaja ya tsaya yana kallon Suwaiba tayi tsuru-tsuru da ita alamun rashin gaskiya tattare da ita. Kallo d'aya ya yi mata yasan ba mutuniyar arziƙi bace. Maigida yace
"Alhaji akwai yarinya da k'ofa ta rufe cikin d'akin nan shine muke k'ofarin buɗe ta."
Ai duka d'aya ya yiwa k'ofar sai gata a kasa ya kutsa cikin d'akin yana kwala mata kira. A firgice ta miƙe daga zaunen da take bakin k'ofa ta k'ara kasa kunne. Ila kuwa muryar Moha taji daya tunkaro k'ofar banɗakin yana kwala mata kira. A guje ta buɗe k'ofar daidai yana k'arasowa. Luu ta fad'a k'irjin sa tana sakin wani irin kuka mai tab'a zuciya. Matseta ya yi kam cikin k'irjin sa yana shafa bayanta.
" Shhh, I'm here"
Cak ya d'auke ta ya fito da ita har zuwa lokacin Suwaiba da Lameen na tsaye falon. Suna fitowa ta fara k'ok'arin sulalewa ta gudu Lameen ya tare ta. Kallo d'aya Moha ya yi mata yace da Lameen ya kira y'an sanda babu musu ya danna musu kira. Tana mak'ale a jikinsa ya shiga motar ya fisga a guje kai tsaye ya d'auki hanyar Jordan. Yana hanya ya kira Gwagwo da tun jiya hankalin ta ya tashi. Saida taji Jadwah tayi magana sannan ta kwantar da hankali ta fara k'ok'arin d'ura musu abinci tunda yace gasu nan hanya. Barci mai nauyi ya yi awon gaba da Jadwah ta k'ara lafewa kan k'irjin sa tana sauke numfashi a hankali na wahala. Karfe hudu daidai suka sauka Jordan dan gudu yake babu kakkautawa babu tsayawa. Har suka je barci take haka ya fito da ita ya shiga gida da sallama. Gwagwo na saune tsakar gida ta gama dakan sakwara da taushe dayajo naman ganda da busheshshen kifi. Da azama Gwagwo ta miƙe tana cewa
"Taheer har kun k'araso? Lfy dai take ko?"
Kai kawai ya d'agawa Gwagwo ya shige d'akin da ita ya kwantar kan gado Gwagwo ta biyo shi. Saboda damuwa daya gani fuskar Gwagwo bai gaya mata abubda ya faru yace mata dai kawai gajiya ce ta sata yin barci a hanya. Saida yaci abinci ya yi nak sannan ya wuce masaukinsa ya kira Lameen dake masa bayanin an kama Suwaiba da laifin sace Jadwah da kuma niyar yin Ambani da ita . Saboda cika kudurinta yasa ta sace don Jadwah taki b'ata damar da take so. An yanke mata zaman yari shekara goma saboda miyagun aiyukon data ke yi da yara k'anana tana gurbata musu rayuwa.
B'angaren Jadwah bara farka ba sai gab da magriba. Tana ganin Gwagwo zaune kusa da ita tana shafa mata ta miƙe ta rungume ta k'ara fashewa da matsanancin kuka.
"I ishiru ya isa haka kuna kar kan ki ya yi ciwo"
Tana sheshshek'a tace " Gwagwo da gaske ne ni matar Moha ce?"
Numfashi Gwagwo ta fesar tana kallon Jadwah tace " tabbas haka ne. Mahaifin ki ya damka masa amanar ki lokacin da yake tunanin bazai rayuba kuma sai ubangiji ya yi hikimar sa. A ranan da Umar ke kwance gadon asibiti ya nemi alfarmar Moha ya riƙe masa ke da amana yana ganin kaman zaki shiga kunci na rayuwa idan har shima ki ka rasa shi. Mahaifin Muhammadu yace in har Umar zai yarda ,yana so kuma su riƙe ki amana ya bashi ke ya aura. Umar ya amce don nema miki gobe mai kyau. A rana d'aurin auren Asiya da Muhammadu aka d'aura auren ki da Muhammadu. Kiyi haƙuri haka Allah ya nufa miki inshaAllahu akwai alkhairi mai d'unbin yawa."
"Amma Gwagwo, shine ku ka bari naje auren sa da Amina? Tana kallona a matsayin mayaudariya da maci amana?"
Kai Gwagwo ta girgiza " kona ce miki kar kije baza ki ki zuwa ba saboda yanda ku ke da Amina. Gashi ai yanzu kinsan ainihin halin ta. Ke dai ki kama kanki ki zauna da mijin ki lfy"
Tana kai zancen ta miƙe ta fice daga d'akin Jadwah ta bita da ido. Anya kuwa zata iya zama da Amina da Asiya a matsayin kishiyoyi?. Kai A'a .dole ma ya sake ta gaskiya.
To b'angaren Amina . Misalin k'arfe biyar motocin d'aukan amarya suka kwashe ta zuwa gidan ango. Yanda suka shiga gidan babu kowa haka suka ajiye amarya b'angaren Moha. Kafin kowa ya watse Saudat ta bata maganin da data k'arbo mata wajan Jalli. Turare da shana. Suna tafiya ta diddike maganin ta shafe turaren lungu da sak'o kaman yanda Saudat tace da ita. Shiru-shiru ango yazo babu shi babu labarin har ta fara gyad'i daga karshe barci ya sace ta bata sani bata farka ba sai gabanin asuba. Ta tashi tana d'an dube-dube ko zata wata alama Moha ya shigo gidan, amma babu komai tsabar bak'in ciki bata san sanda ta fashe da wani irin kuka ba ranta na d'aci. Duk wannan laifin kan Jadwah ta d'ora shi.
Moha kam harga Allah ya manta da wata Amina. Hankalin sa da nutsuwar sa gaba d'aya na kan Jadwah. K'arfe takwas tayi maaa k'ofar gidansu Jadwah. Lokacin daya shigo kai tsaye falon Gwagwo ya wuce don yanzu bashi da shamaki da gidan kaman yanda Gwagwo tayi masa unarni. Zaune ya gansu suna karyawa da soyeyyen dankali da chicken pepper soup da soyayyen kwai. Gefe ga kunun madara da yaji kwakwa sai tururi yake. Guri ya samu kusa da Gwagwo dake masa sannu da zuwa ya zauna yana fuskantar Jadwah data sunkuyar da kai ta kasa cigaba da cin abincin.
Miƙewa Gwagwo tayi ta fice taba cewa bari ta kawo masa abincin ta . K'irjin Jadwah ya fara harbawa da kyar ta had'iye yawu saboda maitar kallon da yake binta dashi tace
"Ina kwana?"
Shiru bai amsa mata ba har tayi tunanin ko baiji bane ta d'ago a hankali ta kalleshi idonta ya fad'a cikin nasa tayi saurin d'auke nata idon. Kiran da Gwagwo ta kwad'a mata ne yasa ta miƙe da sauri ta fice daga d'akin kama wadda aka koro. Kitchen ta samu Gwagwo ta gama had'a abinci kan tire ta ce
"D'auki maza ki mik'a masa ya karya. Allah yasa anyi abincin da dama kaman nasan zaizo"
Bada san ran Jadwah ba ta k'arbi abincin ta koma d'akin. Gabansa ta ajiye k'irjin ta na harbawa ta matsa da sauri zata bar kusa dashi ya yi magana da muryar nan tashi mai tsananin gard'i.
"How are you feeling?"
Gaba d'aya jikin ta ya mutu murus tayi saurin ficewa bata bashi amsa ba. D'aki ta koma ta kwanta tana tunanin abubuwa da dama cikin ranta. Shikam zagewa sukayi da Gwagwo suna magana k'asa-k'asa . Gwagwo ta gaya masa zancen sanin auren sa da Jadwah da tayi. Wata y'ar b'oyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke. Finally gwanda data san da hakan dama yazo ne yau da niyar bayyana mata koshi waye a wajen ta. Abun ya fara zuwa masa da sauk'i yanzu sai ya fara cusa mata sanshi cikin ranta. Bai tashi tafiya ba sai gab da azahar yace da Gwagwo ta d'an ara masa Jadwah zata rakashi Unguwa. Lokacin da Gwagwo ta kwala mata kira har ta fara barci ta miƙe da sauri ta fito tana gyara d'ankwalin kanta daya kunce
"Na'am Gwagwo "
"Maza ki d'an gyara fuskar ki kizo zaki raka Muhammadu "
Sakato ta tsaya tana kallon Gwagwo da tayi maganan ba tare data kalle ba ta. Tana jin yanda ya bita da wannan shegen kallon nasa. Bata ce komai ta juya ta fice daga falon ranta a b'ace. Bafa zata iya zaman aure dashi. Kar yaga don har yanzu batace komai ba hakan na nufin zatayi shiru ne.
Doguwar riga ta saka k'irar Egyptians silver Ash. Ta yana mayafin ta a kanta gashinta data nad'e kaman gammo. Sai d'an flat takarmi data saka da K'aramar pose. Tana fitowa ta sameshi tsaye bakin k'ofar ya d'an jingina da bango ya hard'e hannu da k'afa yana kallon k'ofar d'akin. Sai yanzu ta lura da k'ananan kayan fake jikinsa. Farar riga mai gajeren hannu da bak'in wando. Rigar kaman ta sanyi take mai kaman ruba. Sosai tabi lafiyeyyen jikin sa ta kwanta don har Abs nashi kana gan sa suka kwanta jikin rigar. Koya ta motsa sai jijiyoyin hannun sa sun nuna. D'an firgita tayi da ganinsa tsaye bakin k'ofar ba tayi tunanin hakan ba tayi sauri komawa ciki dafe da k'irjin ta dake barazanar tarwatsewa.
Murmushi ya d'an yi mai sauti yace yana d'an d'aga murya kad'an yanda zataji.
"Let's go"