Sashe 6
Rijiya Gaba Dubu Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Gimbiya Shumaira na zaune a cikin turakar ta sai ga Gimbiya lamirat ta shigo, Koda ta dago kai suka yi arba da juna sai Shumaira ta Mike zumbur! ta ruga gareta cikin tsananin farin ciki suka rungume juna,Shumaira ta janye jikinta daga cikin nata suka fuskanci juna sannan tace,Ai tun jiya nake zuba ido naga kun iso amma sai naji shiru tunda dai shekara ta zagayo, Lamirat tayi murmushi tace Ai mun kara kwana daya ne akan lokacin da muka saba tasowa, saboda wannan karon mun taho da wani gagarumin jarumi, wanda za a samu kudade da yawa a dalilin sa,Koda jin wannan batu sai mamaki ya Kama Gimbiya Shumaira tace, Haba ya ke kawata yanzu Ashe har za a iya samun wani jarumi wanda zai burge mutane a wannan nahiyar tamu sama da mahaifina ki?Lamirat tayi murmushi tace,Ai bana nufin yafi mahaifina JARUMTA, amma dai zai taka muhimmiyar rawa a wannan gasa da za ayi ta bana,kuma ina tabbatar miki da cewar inba mahaifin nawa ba babu wanda zai iya kaishi kasa a wannan gasa, Shumaira ta girgiza kai tace Yake kawata kin sani cewa ban taba zuwa kallon wannan gasa ba saboda ko kadan bana son naga jini yana zuba, bana son naga ana kashe mutane a aikin banza, amma wannan karon naji zuciyata tana son taga wannan bakon jarumi wanda kika zo mini da labarin sa don haka indai zai yi wasa gobe zan fita filin gasar na kalle shi don kawai naga iyakar jarumtakar tasa da kike kodawa, Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Gimbiya lamirat saboda ta dade tana son ta dinga Jan Shumaira suna fita kallon wannan gasa tare amma taki tsawon shekara da shekaru, Tabbas lamirat tayi mamaki da taji Yau dare daya Shumaira ta amince zata fita kallon wannan gasa.
to jama'a sai na huta zan Dora
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 19
A daren wannan rana kuwa aka yi ta shela birni da kauye cewar sarki gurzalu yazo da wani sabon gwarzon jarumi kuma ansa cacar kudi akan sa cewar duk jarumin da ya kai shi kasa za a bashi dinare miliyan daya,kuma sannan zai yi wasan farko a gobe da safe tare da sadauki Darwaz na birnin misra, Koda wannan labari ya bazu sai gari ya rude da kace nace ana mamaki, attajirai kuwa suka yi ta shirya cacar kudi a tsananin su kowa na zabar gwaninsa a tsananin jarumi Imhal da sadauki Darwaz, Jama'ar gari kuwa mata da maza yara da manya kowa ya dinga dokin gari ya waye yaje ya biya kudin shiga filin gasa domin ya ga irin gumurzun da za ayi tsananin wadannan manyan jarumai.
Kai! tun kafin ma gari ya waye filin gasar ya cika makil ya zamana cewar har akan katanga mutane ne a zaune, duk inda mutum ya duba baya ganin komai sai kawunan bil'adama, babu wani guri da yayi saura sai na sarakuna da manyan attajirai, sune kadai basu iso ba,sai kuma jaruman da za suyi gasar, wato jarumi Imhal da sadauki Darwaz.
Sadauki Darwaz wani narkeken katon mutum ne mai girman gaske wato mai kirar mutanen farko, Darwaz ya kasance shahararren gwarzon mayaki mai tarwatsa maza a filin daga,A ranar da suka fara yin gasar kambun JARUMTA shi da sarki gurzalu, dakyar shi sarki gurzalu ya samu nasarar kaishi kasa,don har sai da ya yanki sarki gurzalu sau biyu bayan sun shafe sa a daya da rabi suna bakin yamutsi, daga wannan lokaci basu sake haduwa ba kawo I yanzu, kuma har gobe ta ciki na ciki, domin kowannensu yayi matukar bakin ciki bisa yadda gumurzun nasu ya kasance saboda sun Sha bakar wuya sun zubar da jini, wannan karon da sadauki Darwaz yaji cewar jarumin da zai kafsa dashi, sarki gurzalu ne yazo dashi sai yaci mugun burin daukar fansa a kansa ya kudurce a ransa cewar a gaban sarki gurzalu zai yiwa jarumin kisan gillah.
Sai da gari yayi haske sosai sannan jama'a suka ji anfara buga tambura ana busa algaita da sarewa alamar cewa sarakuna zasu fito daga cikin gidan sarautar, nan take gaba daya jama'ar dake filin gasar suka mimmike tsaye don girmamawa, Fadawan sarki taryan da manyan attajiran kasar suka fara shigowa cikin filin gasar, sannan sai ga sarki taryan, sarki gurzalu, Gimbiya lamirat da gimbiya Shumaira sun shigo,dakaru da kuyangi na take musu baya har suka iso wajen da aka tanadar musu mai dauke da kujeru na alfarma,Koda jama'ar gari suka ga Gimbiya Shumaira ta fito kallon wannan gasa sai suka cika da matukar mamaki, nan dai su sarki taryan da su Shumaira suka isa mazauninsu suka zazzauna.
Al'amarin jarumi Imhal kuwa, tun a jiya bayan anyi masa wanka, ansa masa magani ajikin raunikan jikinsa, kuma an bashi abinci na alfarma ya cika cikin sa sai ya nutsu sosai ya dawo cikin hayyacinsa inda ya fada cikin kogin tunanin abubuwan da suka faru a baya.
to jama'a zan cigaba idan na huta.
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 20
Babu abinda ya fara fado masa a rai face irin tsananin azabar da aka gana masa a bakin RIJIYA GABA DUBU ta tsawon kwana goma Sha hudu, A tsawon kwanakin azabar gobe tafi ta jiya, haka akai ta azabtar dashi babu sassauci, azabar farko itace wadda kunamun nan suka fito suka yi ta cizon sa,kashegari kuwa macizai ne suka fito suka yi ta saran sa,haka abin ya cigaba da wakana, wata ran ya ga dodanni suyi ta dukansa suna tamola dashi.
Koda jarumi Imhal ya gama tuno wannan masifaffiyar wahala da ya Sha acikin RIJIYA GABA DUBU wacce ke cikin kurkukun darul maut, sai ya takarkare ya kwarara uban ihu,Ihun nasa ya cika gidan sarautar gaba daya, har sai da dakaru masu yawa suka rugo izuwa kofar dakin da yake,Koda suka leka suka gan shi a kwance a kasa kuma a daure ga kofar dakin a kulle sai hankalin su ya kwanta, sabo da dama can an gargade su matuka akan cewar kada su kuskura su bari ya tsere, idan kuwa ya gudu a bakacin ransu su duka.
Gama tunani ke da wuya sai ya kamu da tsananin bakin ciki ya fashe da matsanancin kuka, A karshe ya kudiri aniyar cewa komai rintsi da tsanani sai ya jure duk irin bala in dake gaban sa domin ya tsira da rayuwarsa, ya koma gidan kurkukun darul maut ya ruguje shi kuma ya kone wannan RIJIYA ta gaba dubu domin a daina azabtar da al umma,Bayan nan kuma yayi alkawarin cewar sai ya koma gidan Likiciya Zumaira domin ya dauke tsoho imzanu su gudu izuwa wata nahiyar daban inda da sannu zai cigaba da bincike domin ya gano asalin iyayensa da danginsa, haka dai Imhal yayi ta sakar zuci har dare ya raba bai sani ba sannan bacci ya kawo masa mamayar ba zato,
Kashe gari kuwa da safe aka sake kawo masa abinci da abin Sha mai rai da lafiya ya kimtsa cikin sa,sai bayan ya huta sosai sannan aka zo aka bude dakin aka fito dashi a daure cikin sarkoki, aka nufi filin gasar JARUMTA dashi.
koda aka iso filin gasar da jarumi Imhal a daddaure cikin sarka, da jama'a suka yi arba dashi sai filin gaba daya ya rude da shewa gami da tafi.
zan cigaba
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 21
Gimbiya lamirat da Shumaira na hango shi sai su duka suka mike tsaye, suka kura masa idanu domin a wannan rana kyawunsa da siffar jarumtakarsa sun bayyana a fili muraran,ita dai Gimbiya Shumaira nan take taji ta kamu da tsananin kaunar sa,bata ma San sanda ta kama yin murmushi ba a gareshi, ita kuwa Gimbiya lamirat sai kawai taji zuciyar ta taci gaba da bugawa da karfi, bugawar da bata San dalilin ta ba,shin kiyayya ce ko soyayya ta janyo hakan? amsar da ta kasa baiwa Kanta kenan.
Koda aka kawo jarumi Imhal tsakiyar filin gasar wanda sama da dakaru dubu dari ne suka kewaye shi rike da makamai don tabbatar da tsaro harma da wadanda suka dana kibiyoyi akan baka, kawai jira suke suga wani yayi ba dai dai ba yasha ruwan kibbau, aka kwancewa jarumi Imhal dukkanin sarkokin da ke jikinsa sannan aka bashi takobi da garkuwa ya rike, nan fa Imhal ya fara waige-waige da dube-dube domin ya ga abokin gwaninsa, amma bai ga kowa ba,Alokacin ne sarki taryan ya bushe da dariyar mugunta ya dubi sarki gurzalu yace,Yanzu wannan Dan jarumin ne lake tunanin zai iya karawa da gwarzo na abin alfahari na?Sarki gurzalu yace,Ai a inda babu kasa nan ake gardamar kokawa, ina naka jarumin ya fito su kara mu gani,Koda jin haka sai sarki taryan ya daga kai ya dubi wani barde,take barden ya daga wata katuwar gudumar danko ya daki wani katon bandiri, karar bandirin ta cika birnin gaba daya da amsa kuwwa, Faruwar hakan ke da wuya aka bude wata katuwar kofa, sai ga sadauki Darwaz ya fito cikin shigar yaki rike da takobi da garkuwa, Tunda Imhal yazo duniya bai taba ganin mutum mai tsananin tsawo, kauri, da murdewar jiki ba irin ta sadauki Darwaz, nan take zuciyar Imhal ta karaya ya fara tunanin cewa, ai bazai iya ba da wannan katon domin da sadauki Darwaz ya karaso ya tsaya daf da shi sai ya zama Dan mitsitsi akansa kamar an ajiye dantsako a gaban shirwa, tun kafin a bayar da umarnin a fara gasar sai Darwaz yasa hannu daya ya make Imhal, saboda karfin dukan sai da Imhal ya yi tsalle sama yaje ya gwaru da karfen da aka kewaye filin gasar ya fado kasa Tim!yana aman jini,Koda Faruwar hakan sai filin gasar ya rude da shewar jama'a, Attajiran da suka shiga cacar kudi da sadauki Darwaz suka kama murna suna ihu da tsalle domin suna ganin cewar lallai jarumin sune zai lashe gasar su kwashi tsabar kudi, shima sarki taryan sai ya kama kyalkyala dariyar mugunta, ita kuwa Gimbiya Shumaira sai hankalin ta ya dugunzuma ta rude ainun ta kamu da tsananin tausayin Imhal, har kwalla ta cika mata idanu.
Ba zato ba tsammani sai aka ga jarumi Imhal ya mike tsaye zumbur! ya ruga da gudu izuwa kan sadauki Darwaz sun ruguntsume da azababben yaki suna masu kaiwa junan su SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama da juriya da bajinta ta ban al'ajabi.
WAYE ZAI SAMU NASARAR WANNAN GASA TSAKANIN JARUMI IMHAL DA SADAUKI DARWAZ?
SHIN SARKI GURZALU ZAI SAMU NASARAR KASHE JARUMI IMHAL YA LASHE GASAR KAMBUN JARUMTA?
SHIN IMHAL ZAI CIKA BURINSA NA RUGUJE KURKUKUN DARUL MAUT DA KONE RIJIYA GABA DUBU?YAUSHE NE IMHAL ZAI KOMA BIRNIN MISRA YA SAKE SADUWA DA TSOHO IMZANU KUMA YA SAN 'YAR UWAR MAHAIFIYARSA LIKICIYA MUZAIRA?
Mu hadu a littafin RIJIYA GABA DUBU 3 don jin cigaban wannan kasaitaccen labari.
to jama'a zan Dan huta kafin Ku jini a cikin na uku