← Book details Rijiya Gaba Dubu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 6

Sashe 2

Rijiya Gaba Dubu Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kafin Zauwadu da Imhal su ankara da abinda yake faruwa tuni ya kshe musu mutane goma sha biyu ya zamana cewa saura goma kacal,koda Imhal ya juyo yaga gawarwakin jama'arsu a kasa a lokacin da gaba daya jikinsa ya rine da jinin dakarun da ya kashe sai ya kwarara uban ihu ya kara kaimi yana mai cigaba da sara da suka cikin tsananin zafin nama mara misaltuwa sai gashi yana yiwa dakarun mummunar barna.

Shima Zauwadu da yaga Imhal ya kara zage damtse sai shima yayi koyi dashi suka haukace suna ta daukar rayuka,Koda shugaban dakaru Murwatu yaga haka sai ya daka tsalle sama kamar an cilla shi daga cikin kibiya ya dira a gaban Zauwadu ya tare shi suka ruguntsume da azababben yaki.

Wohoho! idan tsagwaron karfi ya hadu da kwarewa akwai tashin hankali,kai koda ga dan kallo ma cikin firgici da tashin hankali zai iya kallon wannan gumurzun.Sai da Marwatu da Zauwadu suka shafe dakiku masu yawa suna kaiwa juna mugayen hare-hare na sara da suka basu samu nasarar komai ba.

A wannan lokaci kuwa Imhal ya samu nasarar bazar da dakaru dubu ashirin a kas,ragowar dubu ashirin din ma sun razana dashi ainun sun fara ja da baya duk da cewa wasun su ya sassare su amma sabo da naci sun ki hakura dada yi masa kawanya suke domin suyi masa rubdugu
A bangaren Marwatu da zauwadu kuwa,lokacin da suka fafata ainun suka ga babu wata nasara sai suka ja da baya sukayi cirko-cirko suna haki da kallon juna kamar wadan su zakaru,kowannensu na tunanin irin dabarar da zai sauya don ya samu nasara akan abokin yakinsa.kamar hadin baki suka zare takubbansu suka daga sama lokaci guda suka rugu izuwa kan juna suna kururuwa,koda ya rage saura bai fi taku uku ba su hadu sai kowannensu ya daka tsalle sama suka kaiwa juna mummunan hari.Cikin sa'a Murwatu ya sokawa Zauwadu takobi a kahon zuciyarsa,shi kuwa Zauwadu ya soka masa a gefen cikin sa,suka rikito kasa a matukar galabaice jini na zuba a jikin su.

Zauwadu ya baje a kasa wanwar ya kasa tashi yana aman jini da karkarwar jiki,shi kuwa Marwatu sai ya mike tsaye ya yage rigar jikinsa ya daure raunin cikin nasa don tsaida zubar jini.

TO AYI MUN AFUWA ZAN CIGABA IDAN NA HUTA
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 4
Koda ya dubi Zauwadu yaga yana kakarin mutuwa kuma ya waiga yaga shima Imhal ya fara gajiya ainun tsabar naci ne da tsananin juriya yasa yake cigaba da yakin sai ya bushe da dariyar farin ciki ya dubi zauwadu yace Ai babu yadda za ayi ku samu nasarar guduwa daga nan har ku tsira da rayuwarku,shekaru arba'in baya haka muke gadin gidan nan ku duka sai kun zama gawa,saura Imhal shi kadai a tsaye shima kuma yanzun nan zan koma na gama dashi kamar yadda na gama dakai.

Koda jin wannan batu sai hawayen bakin ciki ya zubowa zauwadu ya dubi gawarwakin 'yan uwansu fursunoni dake kwance a kasa,kawai sai ya yunkura cikin matukar karfin hali ya bushe da dariya ya dubi marwatu yace,Tabbas mutuwa zanyi amma ko ba komai na jagoranci fursunoni mun karya alkadarin gidannan tunda gashi har mun samu nasarar fitowa daga cikinsa alhali babu fursunan da ya taba fitowa,ko ba komai kai marwatu zan mutu na barka da tabon yankan takobina a cikinka.

Gama fadin haka keda wuya sai suka ji karar bude kofofin kurkukun guda goma sha biyu gami da gudun sawaye alamar cewa dakarun da ke cikin gidan sun faarga da mutuwar shugabansu saiyaru wanda aka bar gawarsa a dakin tuhuma don haka fitowa za suyi waje su kawowa su marwatu dauki.

Koda Imhal ya jiyo sautin gudun dakarun daga cikin kurkukun sai ya zabura ya falfalo da azababben gudu izuwa inda su marwatu suke ya buda dakarun nasa da karfin tsiya yana saransu da banke su kai kace tamkar bai taba gajiya ba ko kuma a sannan kuma a sannanne ma ya fara yakin.

Kafin marwatu ya juya ya tari Imhal tuni Imhal ya dako tsalle a sama ya doki gadon bayansa,sabo da karfin dukan sai da marwatu yayi tsalle sama ya bar kan tsuburin gaba daya ya fada cikin tekun,koda ganin haka sai ragowar dakarun nasa gaba daya suka ruga zuwa bakin tekun domin su ceto rayuwar marwatu.

Damar da Imhal ya samu kenan ya sunkuya ya dauki zauwadu ya saba shi ae kafada ya ruga da baya izuwa inda jirgin ruwa yake ya daka tsalle ya dirga acikin jirgin ruwan ya warbar da zauwadu a ciki sannan yasa takobinsa ya sare igiyar da ta daure jirgin,aikuwa sai igiyar ruwa ta kada jirgi sai gaba.
a dai dai wannan lokaci ne dakarun cikin kurkukun suka karaso kofar gidan a guje suna da yawa kuma a sannan ne aka tsamo marwatu daga cikin tekun aka dawo dashi kan tsibirin.

Koda marwatu ya kyalla ido ya hango su Imhal acikin jirgi nesa kadan da tsibirin sai ya kwarara uban ihu yace A ruga a debo karnukan gidan,nan take kuwa aka je aka debo karnukan,Marwatu da karnukan tare da wadansu dakaru kimanin mutum dari biyu suka shiga wani jirgin dabam suka bi bayan jirgin Imhal.

TO JAMA'A AYI MIN AFUWA IDAN NA HUTA ZAN CIGABA.

RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 5
Lokacin da Imhal yaga igiyar ruwa ta kada jirginsu yayi gaba sa ya dawo inda ya warbar da Zauwadu ya iske shi yana ta kakarik mutuwa bai mutu ba,Imhal ya durkusa daf dashi ya kama hannayensa ya rike a lokacin da hawaye ya zubo masa ya dube shi yace "Haba ya kai abokina,sabo dame zaka tafi ka barni alhalin gashi mun sami nasarar guduwa daga kurkukun darul maut?" koda jin wannan batu sai Zauwadu yayi kakin jini ya tofar sannan ya dubi Imhal cikin karfin hali yace"ya kai abokina ina mai farin ciki da ya zamana cewa kai kadai ka tsira da rayuwarka daga cikin mu ba don komai ba sai don nasan cewa ka samu damar da zaka cika alkawarin dake tsakanin mu, duk ranar da ka riski matata suhailat ka bata labari irin rayuwar da mukayi a cikin kurkukun darul maut da yadda ka zama babban abokina kuma masoyina alhalin da farko mun kasance makiyan juna,ka sanar da ita yadda akayi muka samu nasarar guduwa daga wannan masifaffen kurkuku har izuwa sanda ajalina ya riskeni,ya kai Imhal idan kayimin haka ka gama yimin komai,kuma cikin kabarina zanyi bacci acikin kwanciyar hankali batare da bakin ciki ko nadamar komai ba,sabo da ko ba komai matata tasan cewa na mutu a filin daga a matsayin gwarzon jarumi,ka sani cewa ba wani laifi nayi baaka kawoni kurkukun darul maut face kawai na hana dakarun sarki Gurzalu zalunci a watavrana sanda suka shigo cikin gari suka kashe wani attajiri suka kwashe dukiyar gidansa kaf,suna shirin kashe iyalinsa ne na afka musu na ragargaje su suka gudu,nan take na taimaki iyalan attajirin na kaisu tashar jirgin ruwa suka hau jirgi suka bar garin gaba daya,tun daga wannan rana sarki Gurzalu ya dinga farauta ta ina buya har izuwa ranar da tsautsayi yasa aka zo aka kamani ranar da na auri suhaila" kodaZauwadu yazo nan a zancen sa sai yayi wa Imhal murmushin karshe sannan idanunsa suka kafe gaba daya jikinsa ya sandare ya zama gawa.Koda ganin haka sai Imhal ya kwanta akan gawar zauwadu ya rungumeta yana mai fashewa da matsanancin kukan bakin ciki kamar ba zai taba dainawa ba, sai da Imhal yayi kuka har ya gaji barci ya dauke shi bai sai ba,a lokacin da igiyar ruwa ta ci gqba da kada jirgin acikin teku yayi ta tafiya ba sassauci.
Chapter 2 · 0% Book details