← Book details Rijiya Gaba Dubu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 6

Sashe 4

Rijiya Gaba Dubu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda gama fadin haka sai aljani Sautil makatur ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba acikin dakin,nan fa Imhal yaci gaba da jin tsananin zogi da radadin Harbin da kunamun nan suke masa har ya dinga jin kamar ya yanke duk wadan nan kurajen na jikinsa wadan da suka duri ruwa, gashi kuma a wannan lokacin yunwa da kishirwa sun addabe shi sai birgima yake yi a kasa yana mutsu- mutsu,kai komai rashin tausayin mutum idan yaga Imhal acikin wannan hali dole ya tausaya masa, haka dai Imhal ya kasance acikin wannan hali har sai da dare ya raba sannan aka bude kofar dakin RIJIYA GABA DUBU aka shigo aka baiwa Imhal wani irin ruwa mai tururin zafi acikin kwarya,Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce, Wanda yake cikin ruwa ko takobi aka mika masa kamawa zai yi, domin ana mikawa Imhal wannan ruwa a lokacin da yake fama da kishi sai kawai ya karbi kwaryar ya kafa a bakinsa ya fara kwankada duk da cewar ruwan yana kona masa harshe kuma yana mugun war I sannan bashi da dadin dandano,shi dai kawai burinsa ya jika makogwaronsa ya kawar da kishirwar da ta addabe shi.

Hakika rashin Sani yafi dare duhu!

Inda Imhal yasan abinda sai biyo baya da bazai sha wannan ruwan ba,gwara ya gwammace kishirwa ta zama ajalinsa domin yana gama shan ruwan da kamar dakika daya sai cikinsa ya murde matuka ya kama ciwo yaji kamar ana daddatsa hanjin cikinsa,bai San sanda yaci gaba da birgima ba a kasa yana rusa ihu,idanunsa kuwa suka kumburo sukayi bulu-bulu kamar zasu fado kasa.

Ayi min afuwa zanci gaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 12
Kurajen dake jikinsa kuwa sai suka cigaba da tsananin zogi suna kara kumbura, Daga can kuma sai Kurajen suka dinga fashewa da Kansu suna zubar da jini gami da wani irin mugunyar ruwa mai doyi, nan take kurajen Na gama fashewa gaba daya sai ya sume, bai sake farfadowa ba sai da sanyin asuba ya buga.A sannan ne aka sake bude kofar dakin aka kawo masa abinci loma daya da ruwa mukurwa uku acikin wani Dan karamin kofin kasa, Haka dai aka cigaba da ganawa Imhal azaba kullum, daga cikin azabobin da aka tanada na cikin RIJIYA GABA DUBU, har tsawon kwana goma sha hudu ya zamana cewa ya rame matuka ya lalace kuma ko ina a jikinsa duk ciwuka ne babu kyan gani,hatta fuskarsa ma sai da tayi muni amma duk wannan tsananin azaba da yunwar da ake yi masa horo da su bash sa ya mutu ba.

A Ranar kwana na goma sha hudu ne da sassafe aka bude dakin RIJIYA GABA DUBU aka fito da jarumi Imhal a cikin matukar galabaice tamkar an dauko tsumma domin ko kadan babu kuzari a jikinsa da kyar ma yake iya taka sawayensa, da yawa daga cikin fursunonin Gidan ma da aka zo za a wuce dashi ta gabansu kasa shaida shi suka yi saboda yadda kamanninsa suka sauya da kuma yadda ya rame matuka, Koda fursunoni suka shaida shi sai suka kamu da tsananin tausayinsa harma wasu suka zubar masa da hawaye, nan dai aka fitar da Imhal daga cikin kurkukun gaba daya aka saka shi acikin jirgin ruwa a daddaure cikin sarkoki, kai kace wani katon goggon biri aka kamo, kuma suma dakaru DUBU ne suka kewaye shi acikin jirgin ruwan don kada yayi wani yunkuri na guduwa, nan take aka nufi Gidan sarautar birnin kisra da wannan jirgin ruwan,Wannan shine abinda ya faru da jarumi Imhal bayan ya gudu daga kurkukun Darul maut an kamo shi ansake dawo da shi.

Al'amarin shugaban dakarun kurkukun Darul maut kuwa, wato sadauki Marwatu, lokacin da yaga sun dawo da jarumi Imhal kurkukun cikin nasara sai ya tafi izuwa gidan Sarki Gurzalu yana mai tsananin farin ciki.
tayi min afuwa zan cigaba idan Na huta
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 13
Da Isar sa gidan sarautar kuwa aka yi masa iso a wajen Sarki, take Sarki yayi masa izini ya shiga har cikin turakarsa inda ya iske shi tare da matarsa Muzaina a zaune acikin farin ciki da nishadi suna ciye-ciye da shaye-shaye, da isowar Marwatu kusa da kujerar da su Sarki suke zaune sai ya zube kasa kamar zai yi masa sujada ya kwashi gaisuwa sannan ya dago kai da nufin yayi bayani amma sai Sarki Gurzalu ya daga masa hannu yana mai yi masa muni da yayi shiru,Sarki Gurzalu ya mike tsaye ya tako har gaban Marwatu ya kama kafadun sa ya tashe shi tsaye sannan ya dube shi fuskarsa cike da annuri yace, ya kai Marwatu kayi sani cewa a iya tsawon aikin da kake yi mini a kurkukun Darul maut baka taba yi mini aiki mai kyau ba kamar wannan na kamo jarumi Imhal, domin inda ya samu nasarar tserewa da ya karya alkadarinmu gaba daya,kuma da ya rusa tarihin da mahaifina ya kafa akan kurkukun Darul maut, tabbas sakamakon da zai biyo bayanka shine mutuwa, to amma yanzu da ka samu nasarar kamo shi na baka kyautar dinare dubu dari biyar gami da nayi mata da maza guda dubu, sannan kuma na baka gidan gona ta na birnin Saihur, Koda Marwatu yaji wannan bushara sai ya dimauce ya sake zubewa kasa yana sumbatar kafar Sarki yana mai yin godiya, Sarki Gurzalu ya bushe da dariyar murna yace, Tashi ka tafi abinka ya kai Marwatu, domin ka kamo min zakin da idan ya balle daga daji zai iya hallakani ya kawar da dukkan zuri'ata ta yanzu, Nan take Marwatu yayi sallama da Sarki ya mike tsaye da nufin ya juya ya fita,sai matar Sarki Gurzalu ta kirawo sunansa ya waigo sannan ta dube shi tace, Ya kai Marwatu kayi sani cewa nayi maka matukar farin ciki matuka da kasa aka kai wannan babban makiyi namu dakin RIJIYA GABA DUBU na kurkukun Darul maut, lallai acigaba da yi masa azabobin cikin RIJIYA GABA DUBU har tsawon kwanaki goma sha hudun nan kafin as tafi da shi birnin misra inda Sarki zai kashe shi a gaban miliyoyin jama'a a lokacin GASAR JARUMTA, Koda Muzaina tazo nan a zancen ta sai Marwatu ya risina yace,Angama ya shugabata sannan ya juya ya fice daga cikin turakar.
zan cigaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 14
Faruwar hakan ke da wuya sai ga wata tsaleliyar budurwa ta kunno kai cikin turakar, Hakika wannan budurwa ta cika dari a fagen kyau domin sau tari idan ta fito cikin gari bata wucewa tabar mutane lafiya dole sai kaga hadari na faruwa, domin Wanda ke kan jaki ko doki zai bangaje masu tafiya a kasa bai sani ba,wadanda ke dauke da kaya a Kansu zasu saki kayan su zube bash sani ba,Kai bama maza ba hatta 'yan uwanta mata idan suka yi arba da ita sai kaga sun Wangame baki suna dalalar da yawu basu sani ba,sabo da tsabar kyawunta da burgesu da take yi,Ba wata bace wannan budurwa face Gimbiya LAMIRAT 'ya guda daya JAL! a wajen Sarki Gurzalu, A duniya babu abinda Sarki Gurzalu yake so dama da Gimbiya LAMIRAT, ba don komai yake tsananin sonta ba sai saboda halayenta sun zo iri daya da NASA,wato ko kadan lamirat bata son talakawa kuma sannan bata da imani da tausayi ko kadan,Laifi kankani bawa ko baiwa za su yi mata tasa a gaba musu azaba mai tsanani ko kuma tasa a sare musu hannaye, idan ma ranta ya baci sosai da kanta zata zare takobi ta sare musu kai,Gimbiya lamirat ta gado mahaifinta Sarki Gurzalu a tsananin Mark da iya yaki sannan tana taba samun tsananta gaba akan makiyi, domin idan tasa shi a gaba sai taga bayansa, Bisa wannan dalili ne take yiwa 'ya'yan sarakai da 'ya'yan attajirai na birnin matukar kwarjini suke tsoron tunkararta da batun soyayya ko aure, Ita da Kanta Gimbiya lamirat ta dauke alkawarin baza ta auri wani namiji ba face Wanda ya fita bata,karfin damtse kuma ya cinye gasar jarumtaka ta nahiyar akan mahaifinta tunda mahaifinta shine ke rike da kambun gasar sama da shekaru ashirin ankasa samun Wanda zai karbe daga hannunsa.

Lokacin da Gimbiya LAMIRAT ta shigo cikin turakar Sarki Gurzalu ta iske shi tare da mahaifiyarta Muzainat a zaune cikin farin ciki bayan taba fitar sadauki Marwatu sai ta karasa garesu cikin tsananin murna ta fada kan kirjin Sarki Gurzalu ta rungume shi tana mai cewa, Ya kai Abbana ina mai tayaka murna da aka samu nasarar kamo wannan babban makiyin namu bayan ya gudu daga kurkukun Darul maut kayi sani cewa naso ace ka bani dama naje har Darul maut na kashe wannan makiyi namu da hannu na domin ko sunan sa bana so naji an ambata bare kuma na ganshi da idanu na".

To zan cigaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 15
Koda jin wannan batu sai Sarki Gurzalu ya bushe da dariya yana mai janye jikinsa daga cikin na LAMIRAT sannan ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar ya dubeta cikin nutsuwa yace,yake 'yata rabin jikina ki kara hakuri daga nan zuwa ranar da zamu hadu da wannan babban makiyi namu a filin gasar JARUMTA ta misra, zaki ga yadda zanyi masa kisan gillah ta hanyar yi masa mugayen sare-sare da takobi na,lallai sai na daddatsa shi kamar yadda ake daddatsa nama a mahauta, yanzu zan sanar daku wani babban sirri Wanda baku sani ba ke da mahaifiyarki, Ku sani cewa wannan jarumi Imhal Wanda nake so nayi gasar KAMBUN JARUMTA dashi ba wani bane face Dan marigayi Sarki Imhal na kasar nan Wanda na kashe shi na hau karagar mulkin da karfin tsiya,idan ban kashe wannan yaro yanzu ba nan gaba sai ya kashe ni ya karbi karagar mulkin sa,duk naga wannan al'amari ne a cikin madubin tsafi na bisa bincike da nayi a jiya da daddare.
Chapter 4 · 0% Book details