Sashe 5
Rijiya Gaba Dubu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda Sarki Gurzalu yazo nan a zancen sa sai hankalin Gimbiya lamirat da mahaifiyarta ya dugunzuma ainun suka rasa abinda yake musu dadi,cikin alamun tsananin damuwa lamirat tace,Ai kuwa tunda haka ne yanzun nan zan he kurkukun Darul maut na kashe jarumi Imhal da hannu na in ba haka ba ina cikin zulumi da fargaba tunda nace Ka kashe makashinka karfin ya samu damar kashe ka,Koda gama fadin haka sai Gimbiya lamirat ta mike tsaye da nufin ta fice daga cikin turakar amma sai Sarki Gurzalu yayi wuf ya ruko hannun ta yana murmushi ya dubeta yace,Haba yake 'yata ai kin sani cewa duk irin kiyayyarki da Imhal bata kai tawa ba amma sai gashi nayi hakuri ina jiran lokaci ya cika Wanda ya dace da zan kashe wannan yaro, kin sani cewa dake zanyi wannan tafiya izuwa birnin misra a gabanki zan kashe wannan yaro, abinda nake so dake shine, lallai ki danne kiyayyarki ga Imhal a yayin wannan tafiya tamu, kada ki kuskura ki sanar dashi cewa nine na kashe mahaifinsa da dukkan zuri'arsa domin idan ya gano hakan burina na kashe shi a filin gasar JARUMTA ba zai cika ba,Koda Sarki Gurzalu yazo nan a zancen sa sai zuciyar Gimbiya lamirat tayi Dan sanyi ta dube shi tace ,shikenan ya kai Abbana zan cigaba da hakuri har izuwa wannan rana amma fa ka sani cewa ba zan iya danne zuciya ta ba akan nunawa Imhal kiyayya gami da cin zarafin sa da azabtar dashi kafin mu isa birnin misra, Sarki Gurzalu yace A a bana son ki taba lafiyarsa domin ina so ya murmure kafin mu isa can din ramar dake jikin sa ta bace kuma ya samu isasshiyar lafiya don kada mutane suga cewar da nakasasshe zanyi wannan gasa, Koda jin wannan batu sai Gimbiya lamirat ta ciza yatsanta cikin tsananin takaici domin ba haka taso ba,tabbas taci buri ta kara azabtar da Imhal ainun bayan da ma ya Sha azabar RIJIYA GABA DUBU. wannan shine abinda ya faru a gidan Sarki Gurzalu kafin cikar kwanaki goma Sha hudun da za a fito da Imhal daga cikin kurkukun Darul maut.
To jama'a ayi min afuwa zan cigaba idan na dawo,jiya na dawo gida amma gobe zan sake komawa ina fatan za ayi min uzuri.
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 16
Al'amarin Jarumi Imhal kuwa bayan Angama yi masa wannan azaba ta kwanaki goma Sha hudu da kayan masifun dake cikin RIJIYA GABA DUBU an fito dashi an kai shi gidan sarautar sarki Gurzalu a matukar galabaice kuma a daddaure cikin sarka sai aka watsar da shi a cikin rana yayi ta gasuwa a cikin harabar gidan sarautar har tsawon kimanin sa'a guda sannan sarki Gurzalu tare da 'yarsa Gimbiya LAMIRAT suka fito Daga cikin gidan sarautar a cikin gagarumar shigar yaki gami da kimtsawar tafiya, tun daga nesa Gimbiya LAMIRAT ta kurawa Jarumi Imhal idanu Wanda ke kwance a kasa magashiyan ya jike sharkaf da gumi yana faman nishi kamar Wanda ransa zai fita. duka da cewar Imhal ya rame matuka amma surar jikinsa irin ta manyan sadaukai tana nan kuma babu abinda ya taba lafiyar kyakkyawar fuskarsa, koda tayi arba dashi a karon farko sai taji zuciyar ta ta buga da karfin gaske kuma ta kasa sanin dalilin haka, Yayin da sarki Gurzalu da Gimbiya lamirat suka iso akan jarumi Imhal suka tsaya sai sarki gurzalu ya sa kafarsa ya dunguri wani ciwo dake hakarkarin Imhal,Imhal yayi Dan ihu sakamakon mugun zafin da ya ji, shi kuma sarki gurzalu sai ya dube shi ya bushe da dariya yace Ya kai yaro, ka sani masu iya magana suna cewa, Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya,Yau gashi ranar yin gasar mu ta JARUMTA ta so kamar yadda na shaida maka, ko da gama fadin haka sai sarki ya kirawo wadansu hadimansa yace, Ku dauki wannan fursunan kuje kuyi masa wanka kuma a kirawo likita na yayi masa magani sannan a bashi kayan yaki yasa azo dashi bakin kafar gari inda za muyi wannan tafiya tare dashi, Koda gama fadin haka sai wadannan hadimai suka ciccibi Imhal suka tafi dashi dakaru kimanin guda dubu na kewaye da su don tabbatar da tsaro, saboda kar Imhal yayi yunkurin guduwa duk da cewar yana daure cikin sarkoki, Bayan an tafi da jarumi Imhal ne sarki gurzalu ya juyo ya dubi Gimbiya Lamirat yace, amma fa kin bani mamaki, wai shin duk ina zafin zuciyar taki ya tafi ne alhalin ga babban makiyin namu a gabanki amma ko dukan sa ba kiyi ba bare kiyi masa azaba ko wulakancin da kike furucin za kiyi masa, koda jin wannan batu sai lamirat tayi dan guntun murmushi tace,ya kai Abbana na sani cewa bana cin zalina ba ramamme ko nakasasshe, na fison na zalunci lafiyayyen mutum Wanda ko yaya na taba shi zai ji mugun ciwo amma ba ragowar mutuwa ba,Koda jin haka sai sarki gurzalu ya bushe da dariyar farin ciki yace Dakyau 'yata hakika barewa bata gudu danta yayi rarrafe, lallai yanzu na gamsu cewar kin gaje ni kuma ko a bayan raina nasan zaki iya tafiyar da mulki kamar yadda nake tafiyar da shi. to jama'a idan na huta zan cigaba.
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 17
Koda gama fadin hakan sai sarki ya kama hannun Gimbiya lamirat ya na ta suka tafi izuwa can kofar gidan sarautar inda aka ajiye keken dokin da za su hau don tafiya birnin Misra kuma ga dakaru masu yawan gaske sun kewaye keken dokin gaba da baya, kuibi-kuibi, wadanda zasu yi musu rakiya, kamar yadda sarki gurzalu ya bayar da umarni haka akayi, wato sai da aka yiwa Imhal wanka aka sa masa magani a jikin raunikansa sannan aka kawo abinci mai rai da lafiya aka bashi yaci yasha ya koshi,daga nan kuma aka sanya masa kayan yaki a jikinsa, amma maimakon a dama masa makami sai aka sake zuba masa sarkoki aka daure shi aka kawo shi cikin tawagar sarki da zata tafi birnin misra, nan take aka sanya Imhal acikin wani akurki Wanda dawakai ke Jansa aka kulleshi a ciki, sannan aka dunguma gaba daya aka fice daga cikin birnin gaba daya.
Tsakanin birnin kisra da misra tafiya ce ta sa'a bakwai don haka fun safe aka fara wannan tafiya ba a iso birnin kisra ba sai da rana ta take, kai tsaye tawagar sarki gurzalu ta nufi gidan sarautar sarki Taiyara don haka sai ya shirya ya fito ya tare su cikin tsananin murna, nan take aka shigar da Gimbiya lamirat da mahaifiyarta izuwa inda iyalan sarki Taiyara suke, shi kuwa jarumi Imhal sai aka kai shi cikin wani daki mai kama da kurkuku aka kulleshi, Sarki gurzalu da sarki Taiyara kuwa sai suka shige izuwa turakar sarki Taiyara inda suka zauna aka kawo musu abinci da aka Sha har da giya suka ci suka Sha suka yi tatul suna ta kyalkyala dariya, daga can sai sarki Taiyara ya numfasa ya dubi sarki gurzalu yace, Ya kai tsohon abokina jarumin jarumai na wannan nahiyar, wai shin bana da wanne guzuri kazo mana da shi ne?ka sani cewa duk shekara Kaine kake lashe gasar nan don haka babu sabon wani al'amari Wanda zai sa mu samu kudade masu yawa tunda kowa ya San cewa kaine zakaran gasar, yayin da sarki taryan yazo nan a zancen sa sai sarki gurzalu ya bushe da dariya sannan yace, Kwantar da hankalin ka ya kai abokina kayi sani cewar nazo mana da wani gwarzon jarumi wanda zai burge yan kallo kuma nine kadai zan iya gamawa da shi, kafin na kara dashi zan bashi dama yayi wasa kamar sau shida, ina mai tabbatar maka da cewar a ranar da yayi wasan farko labarinsa zai bazu a ko ina, kuma kashegarin da zai sake wasa sai filin gasar ya cika ya batse da yan kallo don haka kafin ranar da zamu kafsa ni da shi ba kananan kudin shiga zamu samu ba.
to zan cigaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 18
Wannan karon har dukkanin sarakunan da ke nahiyar nan sai sun zo sun kalli wasan karshe, domin suga yadda zata kaya, Yau baza ayi wasa ko guda daya ba sai gobe saboda ina son jarumin nawa ya huta sosai ya samu karfin jikinsa, Koda sarki gurzalu yazo nan a zancen sa sai sarki taryan ya bushe da dariya sannan yace, Ya kai abokina nifa duk wannan labarin da na bani naji sane kamar tatsuniya, duk da cewar banga wannan jarumi ba da kazo dashi nasan nawa jarumin sadauki Darwaz ya fishi komai da komai, don haka a goben da safe ina son Darwaz da jarumin naka su kara.Koda jin wannan batu sai sarki gurzalu ya sake bushewa da dariya yace Ai shikenan, dama masu salon magana sun ce sai an gwada akan San na kwarai.
Sarki Taryan yana da 'ya' guda daya wata kyakkyawar budurwa ta kwatance mai suna Shumaira, Shumaira da Lamirat sun kasance kawayen juna tun suna yara kanana saboda abotar dake tsananin iyayensu, don haka suma sun shaku ainun, Wani abin mamaki shine, ko kadan ra'ayinsu baizo daya ba,domin ita Gimbiya Shumaira tana da tsananin tausayi, sabanin lamirat wadda ta kasance Mara imani ga zalunci, hakan bata sa sun kasa shakuwa da kaunar juna ba,amma suna yawan samun sabani domin ako yaushe Shumaira tana matsawa lamirat akan ta daina zaluntar talakawa da masu rauni, wani lokacin ma idan suka samu sabani, sai su kwana uku basa magana da juna,kuma su daina kwana a waje daya da con abinci tare.