Sashe 1
Rijiya Gaba Dubu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 1
Da isar saiyaru cikin gidan kurkukun bayan ya wuce kofofi goma sha daya sai ya wuce kai tsaye izuwa dakin tuhuma yana ta murmushin mugunta,da isar sa kofar dakin sai masu gadin dakin suka rusuna suka gaishe shi,ko kallon su bai yi ba ya daka musu tsawa yace Maza ku budemini kofar da sauri na shiga,cikin hanzari daya daga cikin masu gadin yasa kuba ya bude kofar ya kunna kai,ashe wadannan masu gadin duk na bogi ne acikin shigar kayan dakaru suna daga cikin dakaru guda ashirin din da Imhal suka zaba domin su taimaka musu wajen samun nasarar guduwa daga kurkukun.Da shigar saiyaru cikin dakin sai yayi arba da Zauwadu zaune akan kujerar da aka saba dora masu laifi an daure hannayensa da kafafunsa da sarkoki ga badakare daya a tsaye akansa yana dukansa da kulki har ya fasa masa baki da hanci jini na suba.koda ganin haka sai saiyaru ya bushe da dariyar mugunta sannan ya dubi badakaren yace dakata haka yanzu kuma nine zanyi masa tawa azabar,ya kai Zauwadu kayi sani cewa yau ne ajalinka zai tabbata a hannnuna tunda har ka karya dokata ka sake haddasa fada tsakanin fursunoni,hakika yau gawrka rabon kifayen dake cikin teku ne.yana gama fadin haka sai ya daga kulkinsa ya nufi Zauwadu da nufin ya buga masa a kansa,ba zato ba tsammani sai kawai wannan badakaren dake tsaye ya shammaci saiyaru ya maka masa kulki akan kunnensa na hagu,take saiyaru ya sulalae kasa sumamme.Koda saiyaru ya farfado sai ya tsinci kansa a zaune akan kujera wacce ake dora fursunoni idan za a yi musu azaba an daure hannayensa da kafafunsa ta baya,Imhal da Zauwadu na tsaye akansa sanye da kayan dakaru,shi dai Zauwadu kayan saiyaru ya sanya sannan ya sanyawa saiyaru nasa na fursunoni.Koda saiyaru yaga haka sai ya tuntsire da dariyar mugunta kuma ya turbune fuska yace kun bata lokacinku a banza domin baku isa ku iya guduwa daga cikin gidan nan ba,nan gidan mutuwa ne gidan da babu wani fursuna da ya isa ya tsira da rayuwarsa koda kun gudu sai an kamo ku an dawo daku idan ma sanyin teku da halittun cikinsa basu hallaka ku ba.Koda gama fadin haka sai saiyaru yaci gaba da kyalkyala dariyar mugunta,cikin fushi Zauwadu ya daga katon kulkin nan na saiyaru ya maka masa shi a ka,take kan saiyaru ya fashe har kwakwalwarsa tayi fallatsi,koda suka ga saiyaru ya mutu sai Imhal ya dubi Zauwadu yace to fa yanzu duk nasarar mu tana hannunka duk yadda za a yi kada ka kuskura ka bari a gane cewa kai ba saiyaru banen,hatta muryarka sai ka karyar da ita irin ta saiyaru tunda daman can kuna kama da juna a fuska da yanayin jiki.Zauwadu ya risina ga Imhal yace yakai abokina kuma shugabana a wannan gida na darul maut,ina mai tabbatar maka cewa baza a taba samun wata matsala ba daga gareni sai dai daga sauran yan'uwanmu fursunoni guda ashirin wadanda muka janyo cikin wannan aiki,ni dai alkawari daya nakeso kayi mini,koda jin haka sai mamaki ya kama Imhal yace wane alkawari kakeso nayi maka?koda jin wannan tambaya sai Zauwadu ya sanya hannu acikin aljihunsa ya dauko wata sarka ta dinare ya damkawa Imhal a hannunsa yace,Wannan sarka ce ta matata wacce muke tsananin son juna fiye da hangen mai hange,a ranar da aka daura aurenmu da ita acikin birnin kisra dakarun sarki Gurzalu suka zo su dubu uku suka rufeni da masifaffen duka har sai da suka sumar dani,ina ji ina gani aka Rabani da amaryata SUHAILA aka sa mini sarka a wuyana,hannayena da kafafuna aka tafi dani suhaila tana kuka da ihu.Wannan shine asalin rabuwata da suhaila yau tsawon shekaru ashirin da bakwai kenan,suhaila na raye ko ta mutu ban saniba.ina son duk sanda ka dawo cikin birnin kisra komai dadewa ka nemi suhaila a unguwar Sharkas ka bata wannan sarka idan har na rasa rayuwata a kokarin guduwarmu daga nan,idan kuma na tsira da rayuwata to zan karbi sarkata domin nayiwa suhaila alkawarin cewar indai ina raye komai daren dadewa sai na dawo gareta ,amma idan ta ga an kawo mata sarkarta to bana raye.Koda Zauwadu yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa,Al'amarin da ya karya zuciyar Imhal kenan shima yaji ya kamu da tausayin Zauwadu har kwalla t acika masa idanu,nan take dai suka fito daga cikin dakin tuhuma Imhal ya sanya sarkar suhaila a cikin aljihunsa suka kullo kofar dakin ,masu gadin dakin mutum biyu suka rufa musu baya.
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 2
Duk ta inda su Zauwadu suka zo wucewa sai ka ga ana gaishe su sabo da ana zaton saiyaru ne,hatta muryar Zauwadu ta amsa gaisuwar sai ta zama iri daya sak da ta saiyaru,su kansu su Imhal sai da suka cika da tsananin mamaki bisa yadda suka ji Zauwadu ya iya mayar da muryar tasa haka,haka dai suka cigaba da tafiya har suka iso dakin da ake ajiye gawarwakin fursunonin mutum hudu da suka mutu a sanadiyyar fadan da akayi a dakin cin abinci,kawai sai Zauwadu ya bada umarni a debo gawarwakin a dora su akan amalanke domin a futar dasu gaba daya daga gidan a watsa a teku,nan take kuwa dakaru suka cika wannan umarni daya bayan daya fursunonin nan guda ashirin abokan aikin su Imhal suka dinga shigowa cikinsu suna take musu baya.dama su duka sunyi shigar dakarun gidan kurkukun,haka dai su Imhal suka cigaba da tafiya acikin kurkukun suna tura amalanken gawa ana bude musu kofofi,duk inda suka zo da zarar anga saiyaru akan gaba sai kaga anbude musu kofa da sauri har suka shige ta cikin kofofi goma sha biyu na kurkukun kuma duk kofar da suka fita sai an mai da ita an rufe.
Suna fitowa daga cikin kofa ta karshe sai suka yi arba da dandazon dakarun dake tsaron gidan kurkukun,a gefe daya kuma ga jirgin ruwa da ma'aikatan kurkukun ke shiga idan zasu je karbo abinci ko wani kaya acikin birnin kisra.Su dai masu gadin kurkukun dakaru ne kimanin guda dubu arba'in,kuma ko yaushe acikin shirin yaki suke dauke da muggan makamai,koda suka yi arba da juna tsakanin su Imhal da masu gadin sai aka tsaya ana kallon-kallo,in ba don ma shugaban dakarun ya hango saiyaru akan gaba ba da tuni ya baiwa yaran nasa umarni su afka musu.
Cikin karamar murya Imhal ya matso daf da Zauwadu yace dashi kada ka kuskura ka matsa kusa da dakarun can,domin sai shugabansu ya gane cewa kai ba saiyaru bane,daga nan zaka yi musu magana ka gaya musu cewa zamu tafi watsa gawar fursunoni ne teku.Koda jin wannan umarni sai Zauwadu ya daga murya ya dubi shugaban dakaru yace ya kai Murwatu kayi sani cewa yau an samu mutuwar fursunoni har guda hudu,sabo da haka ina son ku bani jirgi na zuba su a ciki sai na isa tsakiyar teku sannan na zubar dasu domin na tabbatar da cewa sun zama abincin kifayen ruwa.Koda jin wannan batu sai Murwatu ya turbune fuska ya dakawa saiyaru tsawa yace,Kai saiyaru sabo dame yau zaka zo mana da sauyin yanayin aiki?
A aikin tarihin gidan nan tsawon shekaru arba'in da kafuwarsa ba a taba yin hakan ba,duk fursunan da ya mutu daga nan ake jefa gawarsa cikin tekun,idan baza ku iya jefa gawarwakin ba daga nan to fa sai dai ku hakura ku koma da gawarwakin ku,duk wanda yayi wani yunkuri cikin ku kuwa zamu far masa.
Koda jin wannan batu sai hankalin su Imhal ya dugunzuma ,suka rasa abinda ke musu dadi domin ga dukkan alamu sun sha wahalar banza kenan bisa duk irin kokarin da sukayi suka samu nasarar fitowa har kofar karshe ta gidan kurkukun DARUL MAUT.
Cikin tsananin damuwa da karayar zuciya Zauwadu ya dubi Imhal yace ya kai abokina yanzu mene abin yi?Imhal yace Bamu da abin yi face mu yaki su Marwatu ko mu ko su!
Cikin firgici Zauwadu yace Baka da hankali ne,ta yaya mu ashirin da biyu zamu iya yakar dakaru dubu arba'in?
Imhal yace bamu da wani zabi wanda ya wuce hakan,ko dai mu yake su ko kuma mu jefa kanmu acikin tekun nan mu hallaka shine kadai gatan da zamu yiwa kanmu,ya kai abokina kai sani cewa faduwar gaba asarar namiji ce,yau ne za muyi yaki da dukkan karfinmu na jiki da karfin zukatanmu,ko mutuwa mukayi mun bar abin fadi.Ko kuwa ka zabi ka koma cikin darul maut a cigaba dq gana maka azaba har ka mutu tunda kasan cewa ko kadan baza ayi mana sassauci ba tunda mun kashe saiyaru?koda Zauwadu da sauran fursunonin suka ji wannan batu sai nan take suka ji dukkan tsoro ya kau daga cikin zukatan su.
AYI MIN AFUWA ZAN CI GABA
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA3
Lokaci guda su duka suka daga kulakensu,sannan suka ruga izuwa kan dandazon dakarun suna masu kurma uban ihu,ai kuwa suma wadan nan dakaru su dubu arba'in sai suka zare takubban su suka ruga gare su.ana haduwa aka kacame da azababben yaki. a kofar gidan na darul maut.Kaico hakika idan mutum yaga mutuwa muraran to fa sai inda karfinsa ya kare,duk da cewar su Imhal yan kalilan ne a cikin wadannan dakaru sai gashi suna ragargazarsu don duk inda suka sa gaban su sai dai kag maza na zubewa kasa alokacin da jini ke feshi da fantsama,kuma ihun mazaje da karafkiyar karafa ta cika dodon kunne.Koda aka samu dakika dari biyu ana wannan gumurzun sai labari ya sauya sabo da sarkin yawa yafi sarkin karfi,nan fa dakaru suka fara samun nasarar saran jikin fursunonin nan,jikinsu na darewa suna ihu amma sabo da naci gami da taurin rai sunki su fadi kasa,a hakan suke cigaba da yaki.Sai dai kaga jikin fursuna yayi kaca-kaca da sara da suka tamkar yayi wanka a kogin jini amma shima bai fasa ragargazar maza ba,wani lokaci ma har faduwa suke kasa sakamakon jiri dake dibarsu amma sai kaga suna mikewa tsaye suna cigaba da yakin.
Koda shugaban dakarun ya ga ana ta ragargazar yaransa kuma ya kasa fahimtar bangaren dake samun nasara a tsakanin mutum ashirin da biyu kacal da kuma mutum dubu arba'in sai ya fusata ainun ya kutsa cikin fursunonin nan da karfin tsiya cikin tsananin kwarewar yaki ya dinga fillewa fursunonin kawuna suna zubewa kasa matattu.