← Book details Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 13

Sashe 9

Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadeek ne ya amsa da yanzu ma idan kin shirya sai muyi ai tunda ba wani aiki bane me wahala".

Cikin jin nauyinsa kasancewarsa babba akanta ya sa ta ce "a,a kabari sai kunshirya sannan yanzu da ga tashin ku sai inkama saka ku aiki".

Tab Anty Samha da ma kinyi shiru dan tunda Yaya Sadeek ya ce zaiyi aikin to ai yayi kinsan yana son aiki sosai nima shi ne ke tayani gyara nawa ɗakin idan na tashi gyarawa."

Aiki su ka shiga yi babu kama hannun yaro Sadeek ya ɗauke manyan kujerun da ke shimfiɗe a parlon Salma ta share sai Samhad tayi mopping.

Basu jima ba suka gama aikin tsaf Salma ta ɗauko room freshner aka sanya, sosai ɗakin yayi kyau dan juya kayan ciki sukayi su ka canza musu waje.

DAGA ALKALAMIN✍️✍️
MARYAM STAR⭐⭐⭐.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GvoBXao9nFdFA7W4DO42f1

🌹RAYUWAR SAMHAD🌹(Abar tausayi ce😭)

DAGA ALKALAMIN ✍️✍️ MARYAM STAR⭐⭐

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GvoBXao9nFdFA7W4DO42f1
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=A&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

____________________________________________________________________________________________________

PAGE 3️⃣4️⃣

بسم الله الرحمن الرحيم.

Zama sukayi suna sauke ajiyar zuciya dukda aikin ba wani mai yawa bane sukayi.

Samhad ce ta haɗo musu orange juice mai sanyi sosai wanda ke tashin ƙamshin genger da clove, sosai Salma da Sadeek suka ji daɗin juice ɗin suna ta santi.

Tsokanarta Sadeek yayi wai wannan lemon ne da ta haɗa ya ɓoye yayansu ya hanashi fitowa ba wani rashin lafiya, sosai Sadeek ya saki jiki da Samhad har yana ta tsokanrta.

Samhad ta ji daɗin zuwansu dan sun ɗebe mata kewa dan Samhad ta na son abokan labari tun ta na gidansu kawaide rashin lokaci ne da kuma rashin sabo ita da ƴan uwanta.

Cikin dabara Samhad ta je bed room ɗinsu dan ta dubo ko Mubeen ya tashi da ga barcin da yake.

Zuwanta yayi daidai da fitowarshi da ga wanka daga shi sai ƙaramin towel ɗaure a ƙugu yana goge ruwan jikinsa da wani towek ɗin ganinta yasa ya nufeta ya miƙa mata towel ɗin tare da janyo hannunta ya zauna gaban miro akan stol ya miƙa mata jƙaƙiyar sumar kansa wai ta goge masa.

Ba tare da musu ba ta shiga tsane ruwan kan nasa da towel ɗin, bayan ta tsane ya jona dryer ya miƙo mata.

Amsa tayi tare da fara busar da baƙin lallausar sumar tashi, bayan ta gama ya shiga miƙo mata maya-mayan gashi ta na shafa masa.

Bayan ta gama grama masa gashin ya miƙo ma ta man shafa wai ta shafa masa, kallosa ta tsaya yi baki sake tana jinjina lamarin a ranta.

ganin bata amsa ba ya sakashi juyowa ya kafa mata kaifafan idnuwansa masu kwarjini.

Ƙasa tayi da kai tana tamƙe tafukan hannayenta tare da yunƙurawa zata matsa ganin yanda ya juyo yana kallonta.

Murmushi yayi tareda janyo ta ya zaunar akan cinyarsa ya tallabo fuskarta da ta sunkuyar tana matse manyan idanuwanta.

Kallonta yayi da kyau kamin ya kai bakinsa akan idon nata ya sumbata ya hura musu iskar bakinsa mai sanyi.

Tsikar jikinta ce ta soma mimmiƙewa ruwan zufa na tsatstafowa a kowane gurbin dake da gashi a jikin ta, motsa baki take alamar ta na son yin magana amma ta kasa furtakomai.

Wani sassanya numfashi ya fesa mata a fuska kamin ya yoga mata jiƙaƙen lips ɗinsa akan nata da bai bar kyarma ba.

Sake ɗaukar kyarma jikinta yayi ga kuma zufa da ta shiga ɓarko mata, cikin sanyin yanayi da na harshe yayi mata magana a kunne yace "pleaseeeeeeeeee ki taimaka wa ɗan marayan mijinki manahhhhh" sa ke jan maanar yayi a cikin kunnenta akaro na biyu saida ya tsotsi fatar kunnen nata kamin ya furta "iya mai kaɗai nace ki shafamin ba wani abu ba, please manah".

Ganin yanda ta rikici ya sanya ya tashi da ita ya zaunar akan kadon tare da yi mata rumfa ya saka hannunsa ya na shafa fuskarta ya nasakin murmushi, haka kawai idan suna atare ya ke jin kanshi cikin nishaɗi da walwala.

Zuwa yayi ya shirya tsaf sannan ya dawo inda ta ke a kwance tayi lamo kamar me barci, Ehemmm yayi gyaran murya ganin ko motsi ba ta yi ba ya sanya ya zauna a kusa da ita yana bubbuga siririn hannunta.

Wuƙi-wuƙi ta dinga yi da idanuwa kamar wata munafuka ko marar gaskiya dariya ta bashi amma ya waske baiyi ba ya ci gaba da tsareta da mayun idanuwansa da sukayi haske ba kamar shekaran jiya ba kasanewar kwana biyu bai yi shaye-shayeba.

A taƙaice ya ce muje idan kinyi break fast ki bani yunwa nake ji sosai" ya ƙarashe maganar ya na shafa lafaffen cikinshi.

Zuro ƙafafuwanta tayi ƙasa tare da sauka ta nufi hanyar fita har zata fice sai kuma ta tuna da su Sadeek da ke jiranta saurin juyowa tayi ta ce "lahhh wallahi na manta Salma da Yaya Sadeek suna jiranka sundaɗe anan wallahi na manta ne shaf".

Miƙewa kawai yayi ya nufota dan bazai iya doguwar magana ba saboda yunwar ta fara cin ƙarinsa.

Ficewa suka yi a tare suka nufi parlon wanda ke tashin ƙamshi, jinjina ƙarfin halin Samhad Mubeen keyi a ransa dan ya lura da uban aikin gyaran da ta keyi a part ɗin nasa.

Farin cikin ganin yanda Yayan nasu ya fito ya saka Salma miƙewa ta je gabansu ganin yanda Yayan nata ya fito cikin burgewa, rungumesu tayi shida Samhad ta na sakin kukan farin cikin ganinsu a haka.

Sadeek ma hawaye ya share ganin yanda Yayanshi abin ƙaunarshi ya fito a kamule da shi....

Daga alkalamin✍️
Maryam. Star⭐⭐⭐

🌹𝑹𝑨𝒀𝑼𝑾𝑨𝑹 𝑺𝑨𝑴𝑯𝑨𝑫🌹(𝑨𝒃𝒂𝒓 𝒕𝒂𝒖𝒔𝒂𝒚𝒊 𝒄𝒆😭)

𝑫𝑨𝑮𝑨 𝑨𝑳𝑲𝑨𝑳𝑨𝑴𝑰𝑵✍️
𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹⭐⭐⭐

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GvoBXao9nFdFA7W4DO42f1
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

PAGE 3️⃣5️⃣🌹3️⃣6️⃣

___________________________________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.

Wata irin karayar zuciya ta zo wa Mubeen ganin yanda Salma ta rungumesu ta na jero kalaman godiya ga Allah tare da wiya Yayan nata addu'oin shiriya.

Sadeek ma share hawayen da suka zubo mashi yayi tare da zuwa bayan Salma ya saka hannu ya rumgomesu su duka.

Shi kanshi Mubeen sai da kwalla ta taru a cikin idonshi kasancewarshi mai dauriaya ya saka bai bari ta zuboba.

Samhad ko biye musu tayi dan sosi zuciyarta ta taɓu jin labarin yanda sukayi rayuwa cikin maraicin uwa da makircin matar uba.

Jin kukan Samhad yake har cikin jinin jikinshi, ganin ba barin kukan zatayi ba yasa ya janye Sadeek tare da bubbuga bayanshi alamar rarrashi.

Janyo Salma yayi itama ya share mata hawayen nata tareda jan kumatunta kamar wata ƴar yarinya.

Murmushi Salma ta saki tare da sumbatar hannun Mubeen, sumbatarta yayi shima sannan ya sumbaci Sadeek ya juya wajen Samhad da ke sakin murmushi tare da hawaye a lokaci ɗaya rungumeta yayi tare da bata light kiss a kai, a hankali ya furta "sorry dear ki dai kuka bana so yana taɓamin zuciya".

Zare jikinta tayi tana ɗaga mashi kai alamar amsawa, Sadeek ne ya matso kusa da ita ya tsugunna ya na mata godiya sosai, "haƙiƙa ke alkairice a rauwarmu Anty Samha bazamu iya biyanki da komai ba sai dai zamu tsaya maki akan komai kamar yanda kika tsayawa ɗan uwanmu abun alfaharinmu na gode sosi Anty Samha."

Murmushi kawai Samhad tayi kamin ta ce "ba komai Sadeek ai kunzama ƴan uwana kuma insha Allah atare zamu fuskanci matsalolin da ke fuskanto mu".

Bayan sun gama kuka suka ɗunguma zuwa dinning dan itama Samhar yunwa ta ke ji sosai kasancewar ba ta karya ba ga shi har sha
biyu saura.

Nutsuwa sukayi suna break atare dan Sadeek cewa yayi shima zaiyi dukda sunyi shi da Salma a ɗazu, Zuba ma kowa Samhad ta yi dan dama tayi da yawa ne dan ta kai har sashen Mammy to sai ga su Salmar sunzo.

Bayan sunkammala Salma ta tayata kwashe kayan zuwa kitchen su ka wanke su tsaf sannan suka dawo parlon inda su Sadeek ke zaune suna ƴar fira sama-sama.

Wani kallon
ƙasan ido Mubeen ya bita da shi, sosai rigar ta fito da kyawunta kasancewarta kalar green mai duhuwa.

Itama satar kallon nashi ta yi a ƙasan ido ta na jin wani abu mai sanyi na narkewa a ɓargo da jijiyoyin jikinta a game dashi.

Sunjima suna fira wanda Sadeek ke sake tabbatar da Yayan nashi ya na cikin kwanciyar hankali da kyakkyawar kulawa.

Sai wajen ƙarfe ɗaya sannan suka tashi don zuwa masjid daga nan kuma zasu tafi shi da Sadeek office dan taya Mubeen aikinsa.

Bayan sunyi sallah su kakwanta barcin rana wanda basu farka ba sai gab da la,asar, sallama Salma tayi mata ta re da tafiya dan so ta ke ta yi wanka.

Samhad ta nuna damuwa da Salma ta ce za ta tafi amma daga bisani sai ta haƙura dan Salma ta ce zata dawo zuwa anjima.

Bayan sallar magrib Mamy ta saka masu aikinta suka girka abinci mai rai da lafiya da kanta da jera abincin akan dinning tare da ajiyewa kowa cup da plate a kujerar da yake zama.

Sai data tabbatar babu me ganinta sannan ta zuba maganin da Hajiya turai ta bata akan kujerar da Daddy ke zama da kuma wacce Mubeen ke yawan zama sannan ta saka a flate na gaban kujerun nasu. sai da ta gama tsaf sannan ta je sashen Alhaji Muhammad cikin salon ƙwarewa a makirci ta tayashi saka kaya harda shafa masa mai kamin daga bisani ta ce "Alhajina ya kamata ka kira yaronka yau ya zo shida ɗiyar mutane mu yi diner a tare, kaga tunda ya ɗauketa basu sa ke tako ƙafarsu a nan ba."

Bai amsa ta ba sai janyo wayarshi da yayi ya kira number Mubeen wanda sai ya shekara bai kirasa ba dan kansa sai idan Mamy ta sakashi gaba kamar yanzu.

Sai da wayar ta kusa yankewa sannan Mubeen da suke tare da Sadeek a cikin mota su na tattaunawa akan ɓatan wasu takardu na wata babbar kadarar Alhaji Muhammad.
Chapter 9 · 0% Book details