Sashe 13
Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Hawaye ya share ya jin tsananin tausayin halin maraicin da Samhad ta shiga lokacin da ta ke gidanshi yasha kamata ta na kallo photon mahaifiyarta ta na kuka tana faɗi mata halin da take ciki na damuwa.
Ganin kukan babu inda zai kaishi ya sakashi yi mata addu'ar zaman lafiya madawwami da rayuwar farin ciki a gidanta na aure.
Mamy tun lokacin da ta faɗi ƙafarta tayi wata ƙara da ƙyar da jan ƙafa ta koma ɗakinta ta na jin duniyar gaba ɗaya ta mata zafi ji ta ke kamar za tayi ɗan ƙaramin hauka ita abinda ya fi damunta shine wai har sauran asirin da ta ɗauki shekaru ta na danƙarawa Alhaji Muhammad sai sun karye idan aka taka dokar bokan.
Janyo wayarta tayi ta sake kiran number Hajiya turai wannan karon tayi sa,a an ɗauka cikin tashin hankali ta labartawa Turai duk abubuwan da suka faru, jinjina kai Hajiya Turai tayi a ranta fal farin ciki sai dai a zahiri ta nuna tashin hankali da damuwa sosai musamman da yanzun darene kusan ƙarfe ɗaya da wani abu.
Rarrashin Mamy Hajiya Turai tayi tare da kwantar mata da hankali akan babu damuwa zatasan abinyi komi kenan zuwa gobe zasuyi magana akai.
Hankalin Mamy sam bai kwanta ba kawaide taji sanyi ne da ta labartawa aminiyar tata amma sam batada walwala ga zugin da ƙafarta ke mata yaƙi raguwa saima ƙaruwa da yake a haka ta lallaɓa tai barci har gari ya waye ba ta farka ba.
Bayan tafiyar Mubeen daga sashen Daddy shima Sadeek ya koma nasu sashen ya kwanta, tashi Daddy yayi ya shiga kaiwa da komowa akan shawarar da su Mubeen suka bashi akan sakawa Mamy ido akan lamurranta dan akwai abinda tayi wanda Sadeek yabi diddigi ya gane itace sosai ya shiga shock akan lamarin dan wasu maƙudan kuɗaɗene aka sata cikin hikima a campany.
Ya jima yana saƙawa da kwancewa gafin...
DAGA ALKALAMIN✍️
Maryam star ⭐⭐⭐(Ƴar baiwar jajirtattu💪🌹).