← Book details Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 13

Sashe 12

Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali Mubeen ke buɗe idonsa mai cike da barci dan sam barcin da yayi ba wani mai yawa bane, tar ya buɗe rinannun idanuwansa akan kyakkyawar fuskar Samhad da ke barci cikin kwanciyar hankali, lumshe ido yayi tare da sake buɗesu a kanta sake janyeta yayi da ga jikinsa ya na ƙare mata kallo ya na tuno moment ɗinsu na jiya, wani sanyi ne da ya haɗe da sanyin iskar asuba ya shiga feso masa wanda ya ke ƙara rura wutar buƙatuwar son kusanci da abokiyar halittarsa, rumgume Samhad yayi tsam a jikinsa ya na sauke zazzafan numfashi ya na kokowa da zuciyarsa da ke tunzurashi akan cimma muradisa a wannan lokacin, ɗayar zuciyarsa kuma na tunatar da shi falalar tashi yayi ibada a wannan lokacin.

Da kyar yayi yaƙi da gangar jikinsa da zuciyarsa ya rabu da Samhad da ke barcinta cikin kwanciyar hankali, wanka yayo haɗe da alwla yazo ya fara gabatar da sallah cikin nutsuwar da Allah ya hallicesa da ita.

Ya daɗe yana ibada kafin lokacin sallar asuba ya shiga, tada Samha yayi ya a gurguje ya fito dan so ya ke ya leƙa Daddy kafin ya wuce massalaci.

Fito yayi harbar gidan cak ya tsaya yana kallon abinda ya sakashi sakin sassanyan hawaye, Daddyne da Sadeek riƙe da hannun juna suna tafiya gwanin birgewa, sai da suka ƙurewa ganinsa sannan ya share hawayen fuskarsa ya bi bayansu zuwa masallacin.

Samhad tunda ya tadata ta tashi ta yo alwala bayan ta gama sallah tayi azkar tare da tilawa ganin shiru har gari yayi haske Mubeen bai shigoba ya saka ta tashi ta fita parlo ta nufi kitchen ta na tunanin yaushe Salma ta tafi bayan nan ta barta jiya da daddare.

Dube-duben abinda za ta sarrafa musu ta fara ganin akwai komai a wadace ya saka ta yanke shawarar yi musu pancake.

Flour ta auna ta ɗauko kwai, sugar, kwakwa, da sauran kayan haɗi, kayan shayi ta fara haɗawa a tukunya ta ɗaura akan gas sannan ta fara kaɗa kwai da madara sugar da butter bayan ta gama ta zuba flour a ciki tana juyawa a hankali tana miksing har ya haɗe sannan ta zuba baking powder da flavor sai bushashiyar kwakwa da busheshen inibi wanda ta gani a cikin wani ɗan basket, bayan ta gama juyawa ta sauke ruwan tea da ya tafaso ya nata tashin ƙamshi ta juye a flask a daura pan akan gas ta shafeshi da butter ta dinga ɗubar door ɗin tana zubawa a kai.

Ta ɗauki dan lokaci kafin ta gama dan sam jikinta babu ƙarfi sosai ƙarfin hali kawai ta ke dan ba ƙaramin dagula mata lissafi salon Mubeen yayi ba na jiya.

Bayan ta gama ta gyara wajen tare da saka pancake ɗin a cikin kyakkyawan vowle mai ɗaukar ido, wani vowle ɗin ta ɗauko ta sake zuba tare da zuba ruwan tea acikin wani flask ta saka a basket ta aje ta fice zuwa parlo.

Sama-sama ta gyara parlon dan baiyi komaiba sai abinda ba'a rasa ba, room freshner ta balala da turaren wuta sai ta kunna AC ta wuce bed room, shikan sosai tayi gyara dan saida suka maida gadon kamar wanda akayi wasan kokowa akai.

Bayan ta gama wanka ta shiga tayo ta shirya cikin doguwar riga kalar blue mai haske wacce ta zauna zam a jikinta kamar dan ita akayi rigar, kwalli kawai ta shafa sai man baki da ya saka pink lips ɗinta sheƙi suna ɗaukar ido.

Motsin shigowar Mubeen taji ɗaga kai tayi ta kalli rantsetsiyar agogon da ke manne jikin bango ƙarfe 08:40 sauke kanta tayi ta dire idanuwanta a tsakiyar nasa shanyayun idanuwan wanda suke cike da barci dan har lumshewa suke da kansu, takowa yayi a hankali ya zuwa inda ta ke zaune ta na linke kaya, zaunawa yayi a kan gadon ya kwantar da jikinsa akan bayanta ya na sake lumshe ido.

Cikin kulawa tace "barka da safiya yah Mubeen" warrrr ya buɗe idonsa tare da jan numfashi, bai san miyasa duk sanda Samhad ta ambaci sunansa ya ke tsintar kansa a cikin wani yanayi ba.

DAGA ALƘALAMIN✍️
MARYAM STAR⭐⭐⭐(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU💪🌹).

🌹RAYUWAR SAMHAD🌹

WRITE BY MARYAM STAR⭐⭐⭐

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GhuhVAo9XfoAsdj82FOnmC

KARKI MANTA LITTAFIN RAUWAR SAMHAD NA KUƊI NE ZAKI BIYA 400 KI MALLAKI DOCUMENT CIKIN SAUƘI.

GA WADDA TA SHIRYA MALLAKAR LITTAFIN GA ACCOUN A ƘASA

9136291920
Maryam umar
Opay.

SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN
09136291920

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Typing....

Page 4️⃣2️⃣

___________________________________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.

Buɗe idonsa yayi sosai akanta ba tare da ya amsa ba ta miƙe tare da cewa "ya zakiyi da ni dan wallahi yunwa nike ji ga barci bai wadaci idona ba" yayi maganar ya na janyo hanuwanta ya miƙar da ita tare da fara tafiya zuwa hanyar parlo, bai saki hannun nata ba sai da ya isa dinning sannan ya saki hannun na ta ya na kaiwa zaune akan kujerar, dariya ce ta kama Samha ganin yanda ya zauna duk yayi huri-huri ga yunwa ga barci sai buga hamma ya ke ya na murza ido.

Yana kallon sanda Samha ke ƙunshe dariya dan ya saki wata ɓarkekiyar hamma shi kanshi ya so yayiwa kanshi dariyar yanda
ya ke jera hamma amma ya maze ya na wani tsare gida.

Sai da tayi dariya mai isarta sannan ta haɗo masa kayan break ɗin ta kawo, ko jira ta zuba mishi pancake ɗin bai yi ba ya tsiyaya ruwan shayin da ta saka zuma ya fara aikawa cikisa babu ƙaƙƙautawa, sai da ya shanye shayin tas ta kuma daɗo masa sannan yaci pancake ɗin, bai wani ci da yawa ba ya ce ta aje mishi sai ya tashi barci zai ƙarasa ci.

Rufewa tayi tare da haɗawa kanta shayin itma ta sha a yangance, shi dai Mubeen yana zaune yana sakin gyangyaɗi harta gama sannan suka tashi ganin ta ɗauki basket ya saka shi dalla mata uwar harara tare da faɗin "mi zakiyi kuma da wannan abin" marairaice fuska tayi sannan ta ce "Daddy zan kai mawa break..." bai bari ta ƙarasa ba ya janyo ta ha aje basket ɗin ya ce " haba Samhadidina ki tauayamin manah wallahi barci nikeji ke na tsaya jirafa tun ɗazu" yayi maganar cikin sigar shagwaba.

Murmushi Samhad ta yi itama cikin sigar Shagwabar ta ce "Please Yah Mubeen Daddy ne fazan kaimawa"
katse ta yayi da faɗin " ok bara inkira Sadeek sai ya ɗauka" bai jira amsarta ba ya ɗauki wayarsa ya kira Sadeek akan ya zo ya ɗauki saƙo ya kaiwa Daddy amsawa Sadeek yayi da cewa "angama babban yaya sai nazo" yanke kiran yayi tare da jan siririn hannunta suka bar wajen, direct kan gado ya nufa da ita amma saita toge juyowa yayi tare da dafe goshi cikin yanayin shagwaba da ya fara daga jiya zuwa yau yace " Hadidina mi nene kuma kika tsaya please ki daina jamin aji hakanan" murmushi tayi sanan ta ce " Yah Mubeen ba fa muyi brush ba" bai bari ta ƙarasa ba ya janyo hannunta ya haura kan gado tare da kwanciya ya janyo remode ya sauko musu rumfar labule da ta zagaye gadon.

Ƙanameta yayi sosai a jikinsa ya na sauke lumfashi dan ko minti biyu basuyi da kwanciya ba barci mai nauyi yayi awon gaba dashi dan dama baiyi wani isashen barci ba kuma a masallaci ya haɗu da Daddy da Sadeek shine da aka taso suka wuce sashen Daddyn su duka sukasha fira har sai da Daddyn ya korosa dan ya lura da yanda idanuwansa suka ƙanƙance alamar barci ya ke ji.

Abbu ne zaune ya tasa uwayen kayan da aka kawo na tsaida lokacin ranar auren Fauzeey da Zee shi dai dan baida yanda zaiyi amma sam hankalinsa bai kwanta da auren nan na gaugawa ba musamman Zee da manemin auren nata ko sati biyu baiyi da fara nemanta ba amma ta nace akan saishi zata aura, ba laifi mai kuɗi ne sosai kuma yana da mata biyu amma duka ba a gari ɗaya suke zaune ba ɗaya na kaduna ɗayar kuma na Kano.

Hajiya Adamace ta shigo ta na washe baki tare da faɗin " Abbun yara kaga abun Allah ko cikin ƙanƙanin lokaci Allah ya kawowa yarannan mijin aure kuma lokaci ɗaya, da ma haka al'amarin Allah ya ke ai"
Lumfashi Abbu ya suke tare da jinjina kai kawai dan bai da ta cewa amma zuciyarsa fal tunanin halinda Samhad ke ciki a nata gidan auren dan ta na kiransa tun sanda tayi waya amma hankalinsa yaƙi kwanciya dukda suna waya da Daddy kuma yana sake tabbatar masa da tana lafiya.

DA GA ALƘALAMIN✍️
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJURTATTU💪🌹)

🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹

Write by maryam star ⭐⭐⭐�(Ƴar baiwar jajirtattu💪🌹).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GhuhVAo9XfoAsdj82FOnmC

Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Typing....

PAGE 4️⃣3️⃣

____________________________________________________________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.

Janyo wayarsa yayi ya na duba wani tsohon hoton Samhad wanda ya daɗe da yi mata shi wata ranar sallah da yayi musu ɗunkuna sai ya ɓoye nata bai kawosu gidan ba saboda su Zee da ke ɗauke mata kaya su ce ai ita bata fita ko ina yawan sallah saboda haka ba zasu bata ba, a ranar sallar kowa ya shirya cikin shirin zuwa eid sai ita kadai saboda bata da kayan sallah shine suka tafi suka barta wai ta tsare gida baiwar Allah batace komai ba duk da tana ɗaukin zuwa masallacin haka ta haƙura ta zauna, bayan tafiyarsu Abbu ya shigo gidan cikin ɗanyar shadda da tasha aiki da leda a hannunsa ya kirata ya bata yace tayi sauri ta shirya yana jiranta a waje, idan bai manta ba godiya har da hawaye tayi mishi kamar wanda ya bata kyautar kujerar maka.
Chapter 12 · 0% Book details