← Book details Matar Shege Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 21

Sashe 20

Matar Shege Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina fitowa na tadda Mama Saude a d'akin,ta dinga kallon k'afata kamar wadda aka ba ta aikin k'irga taku na,na san dai tsabar gulma ce take cinta,na had'e rai na k'araso na gaishe ta.

Ba ta amsa ba ta ce"oh! Zinatu ashe haka abu ya faru?"

"Uhm!" Kawai na ce,na d'auki d'ankwalina na shimfid'a a k'asa,na tada sallah

"To kin yi wankan tsarki ne?" Na ji tambayar tata a bazata.

Na juyo na kalle ta na sakan uku,sannan na tada sallata.Kafin na idar ta fita ta shigo da kwando me d'auke da kuloli,ta had'a shayi kofi biyu, ta ja d'aya gabanta,ta mik'o min d'aya,haka abincin ma ta zuba faranti biyu, ta gyara zama ta fara antayawa ba tare da ta min magana ba.

"Mama a ina aka samu wannan abincin?" Na tambaye ta,ina d'aukar kofin shayin

Ta ce"daga gidansu yaron aka kawo.Ai ya na nan ma,ya na jira a sallame ki, ya maida mu gida,wallahi yaro kyakkyawa me hankali da kirki,ni na san k'addara ce kawai kifta".

Na ce"Baba da Ummi sun sani?"

Ta na yagar naman kaza ta ce"yo kema dai zancen ki ke so,idan ba su sani ba ni taya zan ji har na zo jinya? Ai har da mahaifin yaron ma baban naki sun zauna,ban dai ji abin da suka tattauna ba tukun,sai mun koma gida".

"Ummi ta zo?" Na tambaye ta.

Sai ta tab'e baki ta ce"ta zo ina? A gabana Na'ima ta kira ta ta sanar mata,amma wallahi bud'ar bakin matar nan,sai cewa ta yi Allah ya ba ki lafiya.To dama waye dolenki idan ba ni ba? Wallahi na san na fi mahaifiyarki shiga tashin hankali,ke ni yanzu fargabata d'aya ,kar Habibu ya ji labari".

Ni dai na yi shiru ban sake tanka mata ba,ta na ta surutun ta,ni kuwa tunanin yanda za mu yi da mahaifana kawai na ke yi. So na ke ma ta bani space na samu damar kiran Nazifi a waya,amma ta zaune min.

Mu na nan zaune Salim ya shigo da sallama,Mama ta amsa ta na yi masa sannu,ni kuwa binsa da kallo kawai na yi,ina jin wata k'aunar shi, Kai! Gaskiya ina son Salim fiye da zaton ku.

Kallo d'aya ya yi min ya kauda kai,ya kalli Mama ya ce"kun ci abincin kuwa?"

Ta washe baki ta ce"mun ci abinci mun k'oshi".

"Ok! Za mu wuce gidan". Ya fad'a ya na d'aukar kwandon kayan abincin.

Ya fita,muka bi bayansa,sai kallon shi nake yi.Muna shirin shiga motar wannan likitan ya dakatar da mu,ta hanyar k'walla min kira,na dakata,shi kuwa Salim ya shige motar bayan ya bud'ewa Mama ta shiga gidan baya.

Likitan ya ce" kin ba ni mamaki".

"Na me kenan?" Na tambaye shi.

Ya ce"akan irin yanda na fad'i abin da ba haka bane,kuma ba ki nemi jin dalili ba".

Na ce"to meye dalilin?"

Ya ce"saboda ba na son tarayyarku da Habib". Na yi masa kallon mamaki

Ya d'ora"Sam! Habib bai dace da mace irinki na,ya na da hak'uri da halaye masu kyau,mace me hankali da hak'uri ce kawai ta dace da shi.Ya na yawan ba ni labarin irin yanda ya ke son ki,ke kuma ba ki damu da shi ba...".

"Kai dakata malam! Idan ka yi ne don ka raba ni da shi,to ka sani shi ka cuta ba ni ba,kuma tunda ka ga tun farko ban nemi jin dalili ba,idan da tunani ai za ka gane hakan dad'i ya yi min.Ba ni da lokacin ku!".

Ina gama maganar na wuce wurin motar na bud'e gidan gaba na shiga, ya ja muka tafi.

Gidan Babana mu ka je,na ji wata sabuwar fargaba ta kamani,Mama ta bud'e ta fita,ina shirin bud'ewa na fita,babu zato kawai na ji Salim ya...
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

Page 20

Na ji ya kira sunana a sanyaye,na juyo na kalle shi ina jiran abin da zai fad'a,sai kawai ya tsaya ya na kallo na,ni ma na zuba masa ido son shin na ratsa duk wasu jijiyoyin jikina,wajan minti biyu muna a haka,sannan ya jinjina kai ya d'auke idonsa a kaina ya ce"je ki".

"Na gode" Na fad'a,sannan na fice na rufo masa motarsa,tsaye na yi ina kallon motar har sai da ya b'acewa gani na,na sauke ajiyar zuciya na shiga gida da fargaba.

A tsakar gida na tadda Mama,anti Na'ima,anti Halima,da kuma yayata ta Rijiyar lemo anti Maimuna,na yi sallama na k'arasa inda suke a sanyaye,da na gaishe su ma babu wanda ya amsa,ni dai na d'auki buta na shige band'aki,ina shiga na duba wayata,na dannawa Nazifi kira,bugu biyu ya d'auka ko sallama ban jira ya yi ba,na fara magana
"Nazifi me kuka yi min?"

Ya ce"ya ya? Da fatan komai ya tafi daidai,ban kira ki bane saboda kar a samu matsala".

"Wai da gaske an yi min fyad'e?" Na tambaye shi,cikin zafi-zafi.

Ya yi dariya ya ce"haba Zinatu! Zargi na kike yi?"

Na ce"ka ga kawai ka sanar min!"

Ya ce"wallahi Zinatu babu wani fyad'e da aka yi miki,kuma cikin mu babu wanda ya tab'a ki".

Na d'an ji dama-dama a raina, na ce"ta ya zan yarda da kai,bayan na ga kun canza min kaya?"

"Wallahi mace ce ta canza miki kaya,ba mu ba". Ya fad'a

Sai na yi mamaki,na ce" to wace ita? A ina kuka samo ta? Kuma jinin jikin rigar fa!?"

Ya ce"k'anwar abokina ce,kuma ta ina za mu samu jini? Zob'o ne muka zuba".

Har raina na yarda da zancen sa,ashe ya b'oye min wani babban abu,sai nan gaba za ku ji illar da suka yi min!

Na ce"to amma meyesa duka jikina yake ciwo? Kuma maganin bacci kuka bani ko?"

Ya yi dariya ya ce"ai dole jikinki ya yi ciwo,tunda ba ki tab'a shan irin k'wayar ba,ke ta ma fa sake ki da wuri".

Na ce"amma Nazifi meyasa kuka ba ni k'waya?"

Ya ce"to Zinatu gani na yi idan idonki biyu za ki iya kawo cikas wurin gudanar da aikin,ko kuma bayan mun kai ki,ki ji tsoro daga baya ki lalata aikin,amma wallahi babu abin da aka yi miki".

Na sauke ajiyar zuciya na ce"to shi ke nan,Nazifi na gode sosai, Allah ya biya ku".

"Amin matar oga J.S" Ya fad'a yana dariya. Na yi murmushi na kashe kiran.

Bayan na fito aka tisa ni a gaba,da fad'a kamar za a min ciki da hak'ora,ni dai ban wani damu da hayaniyar su ba,tunda dama na san ta zama wajibi,kuma ko dukana za a yi tunda burina zai cika ba zan damu ba.Bayan sun gama bambamin su,sai kuma suka sakko suna tambaya ta a inda na had'u da Salim har ya min fyad'e,na fad'a musu dama can saurayina ne,kuma ba halinsa bane,shi ma tsautsayi ne ya afka masa.

Anti ta katse ni da fad'in"to idan ma halinsa ne cutar y'ay'an mutane ai yanzu ya yi wanda ba zai kub'uta ba,don kuwa yanzu sati d'aya aka tsayar auren ku".

Na ji zuciyata ta motsa,sai na rasa farinciki zan ji ko akasin sa? Ni dai abu d'aya da na tsana yanzu bai wuce yanda y'an'uwana su ke yiwa Salim kallon macuci ba,na san alhaki a kaina,sai dai na kan ji dama-dama idan na tuna da anyi auren komai zai wuce...

Na tashi na shige d'aki,na kwanta,ina jiyo tattaunawar su,har aka kira la'asar.

Ina idar da sallar la'asar Baba ya shigo,ya kira ni,na zo na tsugunna kaina a k'asa,to shima dai fad'an ne babu k'akk'autawa,kuma ya tabbatar min ranar Asabar za a d'aura aurenmu da Salim, kamar yanda mahaifinsa ya tsara, ya ce min shi ma kuma ya amince don shi ne kawai mafita a gareni.

Washegari da safe Anti Maimuna yi min waya, ta ce na je gidan Ummi yanzu, na shirya na tafi ina ta fargaba.A d'akin Umma na same ta,na zauna na gaishe su suka amsa babu yabo babu fallasa,na yi shiru ina jiran ta inda za su fara tasu tijarar,jin shirun ya yi yawa na ce"Ummi ga ni".

Ta ce"ai na gan ki, me zan yi miki? Ko na kira ki ne?"

Na ce"Anti Maimuna ta ce na zo".

Ta ce"to ki kira ta ki tambayi wurin wanda za ki je,ni dai ban kira ki ba".

Na sunkuyar da kai na ce"don Allah Ummi ki yi hak'uri".

Ta ce"hak'uri ai ke ya kama Zinatu,ke da za ki zama MATAR SHIGE...".

Babu wanda ya sake yi min magana, har dai na gaji da zama na,na tashi na koma gida. Tun daga nesa na hango Habib a k'ofar gidanmu,na k'araso na yi masa kallo d'aya,ina niyyar shigewa ya zo ya tare hanya,sannan ya ce"Zinatu zan yi magana da ke".

Ban ce komai ba,na tsaya sauraron shi

Ya ce"yaushe ku ka had'u da J.S,har kuka yi nisa a soyayya ban sani ba?"

"Ba mu dad'e ba" Na ba shi amsa.

Ya ce"kuma da gaske ne ya yi miki fyad'e?"

Na ce"to kai meye matsalar ka da hakan?"

Ya ce"amma ai kin san ya kamata na sani ko?"

Na ce"saboda me?"

Ya ce"saboda ni zan aureki,kin ga kuwa ya dace na san komai game da matsalar".

Na yi shiru ina mamakin sa.

Ya d'ora da fad'in"saura fa sati biyu ya rage,zuwa gobe na ke son a buga invitation,sai ki lissafi abin da ki ke buk'ata,na baki kud'in,lokaci ya na k'urewa".

Daga haka ya tafi,ya bar ni tsaye da mamakin sa.

SALIM

Tunda ya maida su Zinatu ,gida ya dawo ya kwanta,zuciyarsa fal bak'inciki,ya san dai ko giyar wake ya sha bai isa ya kalli Abba ya ce masa ba zai auri Zinatu ba,shi a yanzu ba ma auren nata ne damuwarsa ba,yanda Junaina za ta d'auki lamarin kawai ya ke ji,ace aure nan da sati d'aya? Anya kuwa za ta yarda da shi?

Ya tashi zaune jin k'irjinsa ya yi masa nauyi,ya je ya d'akko lemo a fridge ya yi had'in k'wayoyin sa,ya fara kwankwad'a.

Ya na cikin wannan yanayin Baby ta zo ta same shi,kasa ajiye jarkar ya yi,saboda burinsa kawai ya shanye ya samu bacci ko zai samu nutsuwa.

Ta na k'araso wa,ta warce jarkar ta jefar,ta zauna ta fashe da kuka, ya dafe kansa ya na furzar da iska. Ta ce"Yaya..."

Ba ta k'arasa ba ya katse ta"wallahi Baby Zinatu sharri ta yi min,ban san komai ba".
Chapter 20 · 0% Book details