← Book details Matar Shege Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 21

Sashe 11

Matar Shege Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta rasa abin cewa,ta ce"Yaya sallar magriba". Ta bar d'akin jiki a sanyaye,amma sam ba ta yarda da zancen yayan nata ba,kuma za ta yi bincike.

Sai bayan la'asar na koma gida,na tadda Baba a k'ofar gida shi da wani mak'ocinmu,na gaishe su,kaina a k'asa na shige gida,na zauna ina ta tunanin k'aryar da zan yi masa idan ya ritsa ni.Ga mamaki na,sai na ga Baba ya bawa banza ajiya ta,aikuwa na ji dad'i sosai na ce watak'il ya sassauta hukuncin ne.

Washegari ko minti biyar ban k'ara ba akan lokacin da Junaina ta bani,yau ta na nan kuma ita kad'ai ce a wurin babu wannan matashin,bayan mun gaisa ta kawo min lemo da ruwa,ni dai ban sha ba,burina kawai na ji ta bakinta.

Ta nisa ta ce"ke dai yanzu idan na fahimce ki,ki na son sanin duk abin da Salim ya ke so,da kuma wanda ba ya so,abin da yake burge shi,da wanda ba sa burge shi ko?"

Na ce"e hakane,idan da dama ma har kalar abincin da ya fi so,da wanda ba ya so".

Ta yi wani murmushi ta ce"za ki ji komai,amma fa akwai sharad'i".

Na ce"na amince da sharad'in ki,fad'a min kawai".

Sai ta yi y'ar dariya ta ce"y'an mata da sauri haka?"

"Zan iya yin komai don Salim ya aureni" Na fad'a ina murmushi

Ta gyara zama ta ce"kin ga yaron da ki ka gani jiya anan? Abokina ne, shi yake taya ni jire wurin nan,kuma gidanmu d'aya da shi,to jiya ya fad'a min ya na son ki,kallo d'aya ya yi miki ya ji sha'awar ki ta kama shi"

Sai ta yi murmushi ta ce"ai ban ga laifin sa ba,kin had'u Zinatu.To a tak'aice dai ya na son kwanciya dake ko sau d'aya ne,wannan shi ne sharad'in idan kin amince ko yau a shirye yake,ni kuma da kun kammala zan ba ki bayanai".

Tunda ta fara magana wani abu ya zo ya tokare k'irjina,na ji kamar na tashi na yi ta fesa mata mari.Ni kam ko da wasa ban tab'a sha'awar aikata wannan mummunan abun ba, to ta zarge ni ne ma wai da take kawo min wannan tayin?

"Ki bani lambar ki,idan na yi shawara zan kira ki" Na fad'a ina mik'a mata wayata.

Ta saka min lambar na karb'a na yi mata godiya na tafi.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

Page 12

Lokacin da na k'arasa gida har an yi sallar isha'i,tun daga nesa na hango Habib zaune a bencin k'ofar gidanmu,na rage sauri na dinga d'aga k'afa kamar ba na so,kallon shi kawai nake yi cikin tausayawa,indai abin da na ke ji a zuciyata game da Salim,shi ma Habib haka ya ke ji game da ni,to kuwa tabbas zan tausaya masa,sai dai ba zan iya sadaukar da farincikina akan na wani ba.

"Barka da zuwa gimbiyata". Ya fad'a bayan na zo dab da shi

Na zauna a bencin nesa da shi na ce"daga ina haka?"

"Daga gida nake" Ya bani amsa

"A yi hak'uri dai a min uzuri,na karya dokar sarauniya,ina fatan za a tausayawa raunanniyar zuciyata wurin yi mata hukunci. Na ji kin ce kin tafi hutun amsa kira,kuma ban sani ba ko har yau ba ki dawo ba,shi yasa ban kira ki ba na yi gaban kaina na zo". Ya k'arashe maganar a raunane,wai a dole na ji tausayin shi

Na k'ura masa ido tun daga kanshi,har yatsun k'afarsa,har yau na kasa gano makusar Habib,ya na so na sosai ga shi d'an'uwana,ko bai b'ata bakinsa ya fad'a min ba,na san zai kula da ni da soyayya idan ya aureni,ya na da hak'uri sosai duk wani laifi da nake yi masa da gangan ya na sani ya ke sharewa,ko wani bai fad'a min ba na san idan na aure shi zan ji dad'i.Amma sai dai kash! Kwata-kwata Allah bai d'iga min son shi a zuciyata ba,a da na amince da shi ne saboda ina ganin ni fa duk duniya babu wani namiji da zan so da aure,ashe lokaci ne bai yi ba,ni kuma GAJEN HAK'URI na ya sa ni saurin zab'ar Habib, ashe sarkin zuciyar tawa ya na dab da bayyana,gaskiya na yi garaje.

Ban san hawaye na ke yi ba sai da na ji muryarsa ya na fad'in "subhanallah! Zinatu lafiya kuwa? Me ya ke damun ki? Ko ba ki da lafiya ne?"

Na share hawayen cikin dakiya da jarumta na ce"Yaya Habib, ina son magana da kai ta fahimta,Allah yasa za ka fahimce ni".

Ya sake tattara hankalin sa wurina,alamun damuwa k'arara sun bayyana a fuskarsa ya ce"me zai hana? Zan fahimce ki Zinatu, ki fad'a min don Allah"

"Idan na tambaye ka,ka na so na ban yi maka adalci ba, na san duk duniya babu wani namiji da ya ke so na sama da kai Yaya Habib,amma a wane mataki ka ajiye so na a zuciyarka?"

Ya sauke numfashi har yanzu dai da alama bai nutsu na ya ce"Zinatu,ba iya son ki nake ba,har da k'aunarki,k'auna me tsanani ma kuwa,kuma kin kai mataki na k'arshen k'arshe a zuciyata".

Na d'auke kaina daga kallon sa na ce "idan na fasa auren ka ya za ka ji? Ma'ana idan k'adddara ta sa na auri wanin ka..."

Ban k'arasa ba ya katse ni,a sanyaye"amma me ya kawo wannan maganar?"

"Ka fara bani amsa kafin ka ji dalili" Na fad'a har yanzu ban kalle shi ba.

Cikin raunin murya ya ce"Zinatu ni musulmi ne,na yarda da k'addara me kyau da akasin ta,wallahi ina tunanin irin yanda zan ji,da kuma yanda rayuwata za ta kasance idan ban aure ki ba, saboda ke kad'ai nake so.Amma hakan ba zai sa na kasa yarda da k'addara ba,tunda na sani wani ba ya auren matar wani,kuma duk da ke kad'ai ce a zuciyata,amma a kullum ina sake neman zab'in Allah".

Jikina ya yi wani mugun sanyi,gaskiya Habib ya na da hankali,kuma na san har da ilimin addini a wannan kyaun zuciyar nasa,ina ma ace shi ne Salim! Da zan bugi k'irji cikin dubunnan mata na ce na fi kowace mace dacen miji,sai dai kash! Zanen k'addara ba ya gogewa,don kuwa har yanzu ban ji son Habib a raina ba,sai dai tausayin shi,kuma wallahi ba zan iya sadaukar da farincikina ba akan shi,sai dai ya yi hak'uri ya d'auki tasa k'addarar kamar yanda nake shirin rungumar tawa

"Akwai wata matsala akan maganar aurenmu ne Zinatu?" Ya tambaye ni

Kamar na yi masa k'arya sai dai na daure na ce"Yaya Habib ko a cikin maza kai namiji ne,ka had'a abubuwa da dama wanda duk mace me hankali za ta so ta same ka a matsayin abokin rayuwa,sai dai ni har yau na kasa jin son ka a zuciyata saboda ba ni da hankali..."

Ya yi saurin katse ni da fad'in"a'a Zinatu,kar na sake jin haka daga bakinki,ki na da hankali,wannan ba laifinki bane laifin zuciyarki ne,shi ya sa ake son mutum ya dinga addu'ar Allah yasa ya fi k'arfin zuciyarsa,zuciyarki ta fi k'arfin ki,da ace kin fi k'arfin ta za ki iya yi mata tilas ta so abin da hankalin ki ya ke baki daidai ne".

Wasu hawaye suka zubo min,na share na ce"wallahi har zuciyata,na so na yi wa mahaifana biyayya don na faranta musu,su yi alfahari da ni ko da sau d'aya ne a rayuwa,amma rafkananniyar zuciyata ta gaza bani had'in kai.Ka yi hak'uri Yaya Habib na fasa auren ka,saboda ko da na aure ka ba zan tab'a iya baka farincikin da ya dace namiji nagartacce irin ka ya samu daga matarsa ba".

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ya furta kawai

Shiru na tsawon lokaci sannan ya ce"Zinatu na sani dama can ba kya so na,amma na tabbata yanzu akwai dalilin ki na fasa aurena,me ya sa? Don Allah kar ki b'oye min".

Gaskiya ban ji zan iya ba shi labarin Salim ba,don haka na girgiza masa kai alamar a'a sannan na ce"ka d'auka hakan k'addara ce kamar yanda ka sanar da ni ka yarda da ita.Ni dai yanzy alfarma d'aya nake nema a wurin ka, wannan alfarmar idan ka yi min ita ce kawai za ta sani na tabbatar da k'aunar da kake yi min,kuma zan rik'e ka a zuciyata masoyi na gaskiya,na yi maka alk'awarin duk sallolina biyar na kowace rana zan yi maka addu'ar Allah ya baka mace ta gari,kuma Allah ya cire maka so na a zuciyarka".

"Wace alfarma ce wannan?" Ya tambaye ni,jikinsa duk ya yi sanyi

Na gyara zama ina fuskantar sa na ce"Yaya Habib so na ke ka fad'awa manya ka janye maganar aure na,don Allah ka yi min wannan".

Ya saka yatsan sa a baki ya ciza kafin ya ce"haba Zinatu! Me yasa ki ke da son kanki da yawa? So ki ke ni aga laifina fa kenan,ki na so a saka ni a jeren masu sab'a alk'awari kenan? Kuma da wane idon kike so na kalli mahaifanki?"

"Ka na nufin ba za ka iya yi min wannan alfarmar ba,a matsayina na wadda ka ke kira farincikin ka?" Na tambaye shi muryata na rawa.

Ya tashi tsaye ya ce"e,ban yi miki k'arya ba Zinatu,ke ce farincikina,amma ba zan iya yi miki wannan abun da kika nema ba,gaskiya sai dai ki yi da kanki.Kuma ki yi tunani kafin ki yanke hukunci,so da yawa mutane su na son abu kuma abun ba alkhairi bane a rayuwarsu,kuma sai su k'i abun da shi ne alkhairi a duniyarsu da lahirarsu,shi ya sa istihara take da amfani,ki je ki yi ta istihara ki nemi zab'in ubangiji,idan still kin ji ba za ki iya aurena ba,sai ki sanar musu da abin da kika yanke,ni ma zan saka ki cikin addu'o'ina in sha Allah, Allah ya mana zab'in alkhairi".

Ya na gama maganar ya buga mashin d'insa ya tafi,ni kuma na tashi na shiga gida ina kukan rashin gaskiya.

'Dakina na shiga na fad'a a katifa,na fashe da kuka sosai,ni ma na san ban yi wa Habib adalci ba,to amma ya zan yi? Haka k'addarar mu ta zo mu duka ukun,da ni, da shi da Kuma Salim,duk Allah ya jarabce mu da son maso wani.
Chapter 11 · 0% Book details