← Book details Matar Shege Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 21

Sashe 17

Matar Shege Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban gama tunanin ba na ji muryarsa cikin hargagi,kamar mak'ogoronsa zai fice "me ya kawo ki nan? Kuma waye ya miki haka!?" Ya yi maganar ya na nuni da kayan jikina

Sai na kai duba ga jikina,gabana ya yi wata mummunar fad'uwa ganin alamun jini a farin yadin jikina,na doguwar rigar da ta kwanta a jikina,kasancewar ta roba.Nan take na tuna ni fa atamfa na saka daga gida,kuma duka ma ba ni da irin rigar nan,hankalina ya yi matuk'ar tashi fiye da yanda za ku yi tsammani,k'irjina ya dinga lugude kamar ana daka a ciki

Sai da na maimaita innalillahi wa inna ilaihiraji'un kusan sau biyar sannan Salim ya sake katse ni,ta hanyar buga min wata gigitacciyar tsawa ya ce"ke Zinatu! Kar fa ki raina min hankali,tambayarki nake yi waye ya kawo ki nan!?"

Da k'yar na bud'e baki na ce"don Allah waye ya yi min haka? Allah yasa kai ne ka min fyad'e ba su ba,kai ne?" Na fashe da kuka.

Sai dai na yi saurin dakatar da kukan jin ana buga k'ofar d'akinsa da k'arfi.Ya zaro ido had'i da d'ora hannunsa a kai,alamar ya shiga tashin hankali,murya k'asa-k'asa kamar zai yi kuka ya ce"na shiga uku! Zinatu me na yi miki za ki yi min haka?"

Ni ma hawayen nake yi,amma ba na tausayin shi ko nadamar abin da na yi masa ba,ni kukan nawa na tunanin wanda ya yi min fyad'e ne

Aka sake buga k'ofar,wannan karon har da kiran sunan shi,muryar namiji ne,ina dai zargin mahaifinshi ne.Ya zo da sauri ya ja hannuna ya na fad'in "don Allah tashi ki b'uya,ki rufa min asiri kar wani ya ganki,wallahi ba zan iya wanke kaina ba,tashi don Allah!" Ya kai k'arshen maganar ya na k'ok'arin d'agani

Sai ya ba ni tausayi don haka na fara tunanin janye wannan mummunan k'udurin nawa,na yi masa sharrin fyad'e, na yunk'ura da nufin tashi,amma me? Sai na ji na kasa tashi,jikina kamar ba nawa ba nake ji,aka sake buga k'ofar ana kiran sunan shi,ban yi aune ba sai gani na yi ya sungume ni cak ya yi wata k'ofa da ni,band'aki ne kamar yanda na zata,cikin hanzari ya shiga ya wurga ni cikin bahon wanka,har k'uguna ya bugu,ya rufe k'ofar ya fita

Ban san yanda suka yi da me buga k'ofar ba,can dai na ga ya sake dawowa,har yanzu ba ya cikin nutsuwarsa,sai zare ido ya ke ya na huci

"Zinatu Allah ya isa tsakani na dake! Me na yi miki wai? Ta ya kika zo d'akina?" Ya fad'a ya na d'ora duka hannuwansa a ka.

Tausayin shi ya kama ni sosai,na yunk'ura na tashi zaune na fashe da kuka sosai kamar ya min umarni da kukan.Sai ya zaro duka idanunsa kamar za su fito ya ce"kuuut! Wai har damar kuka ma ki ka samu? Ni da zan yi kuka ban yi ba,sai ke? Zo ki fice daga gidan nan tun ban yi miki dukan mutuwa ba!". Ya kai k'arshen maganar muryarsa na rawa kuma cikin fad'a.

"Ina wayata?" Na tambaye shi.

"Ta na gidan ubanki!" Ya fad'a,sannan ya fusgoni daga cikin bahon ya warb'ar da ni a k'asa,k'afata ta bugu har na ji kamar babban yatsana ya karye

Da k'yar na tashi tsaye don fita na tafi gidan kamar yanda ya ce,amma da k'yar na samu na iya taku uku,wani irin juyi na ga garin ya na yi min,haka na yi ta layi ina dafa bango a k'ok'arina na fita daga band'akin,kallo d'aya dai za ka min ka san ba na cikin hayyaci na,ina fitowa daga band'akin na zube a k'ofar cikin mutuwar jiki,don k'arfina ya k'are duka,ba na jin zan iya wani takun

Salim ya zube shi ma a inda na fad'i murya na rawa ya fara jijjigani ya na fad'in"na shiga uku! Zinatu ki rufa min asiri kar ki mutu a d'akina don Allah!"

Ya tashi a guje ya d'akko robar ruwa ya watsa min,don shi a zaton sa suma na yi,na bud'e idona da suka yi jawur na ce"Salim... Don Allah Salim ka ji?"

"Uban me zan ji? Me za ki fad'a min? Ai har gani ma na yi ba ji ba,wannan shi ne sakamakon son da kika ce ki na yi min? Allah ya isa!"

Kawai sai ya jingina da bango ya fara share hawaye.Na daddafa na tashi da k'yar,idona ya na rufewa saboda har yanzu da sauran bacci a ciki na fara takawa a hankali nima ina share hawayen,ni dai hawayen tausayin kaina da nadama nake yi, shi kuma ban san ko na meye ba.

Har na kai bakin k'ofa na ji ya daka min tsawa ya ce"dawo!".

A maimakon na dawo sai na zauna a bakin k'ofar,idona ya na lumshewa,ya tashi ya fita daga d'akin.

Babu wani zafi ko zugi da nake ji daga k'asana,wanda zai tabbatar min da fyad'en da aka yi min,amma ko ban ji zafi ba dole na yarda tunda ga jini nan ya zama shaida,da kuma canza min kayan da aka yi,ni yanzu babbar damuwata na ga wayata kawai,don na kira Nazifi na ji wanda ya yi min fyad'e da kuma dalilinsa na yi d'in.

Bai jima ba ya dawo d'akin,ya bud'e sif ya d'akko kayan shi,ya buga min harara ya shige band'aki,ya fito sanye da k'ananun kaya ba na d'azu ba,ya zo ya tsugunna a gabana har ina jin hucin numfashin sa,ya ce"Zinatu! Don girman Allah waye ya kawo ki d'akina?"

Na kalli k'wayar idonsa da na ke karantar damuwa k'arara na ce"son ka ne Salim! Wallahi son ka ne k'addarata...".

"Ni ma kin zama k'addarata Zinatu,kuma ban yafe miki ba" Ya katseni

Na share hawaye ina lumshe ido,wata sabuwar k'aunar shi na dagargazar zuciyata wallahi burina kawai na ganni a kwance ina bacci,da ya san yanda nake ji a halin yanzu da tuni ya rungumeni na yi bacci a jikinsa.

"Da ki ka zo d'akin nan kin d'auki wata k'wayar kin sha ne?" Ya tambaye ni,ya na nuna min lokarsa

Na girgiza masa kai,alamar ban sha ba. Ya ce "ok dama can ki na shaye-shaye kenan?"

Na yi banza da shi

"Ki tashi na kai ki gidanku,gobe zan zo mu yi magana". Ya fad'a ya na d'akko mukullin mota.

Na tashi da k'yar, ina tangad'i idona na lumshewa,amma duk iya k'ok'arina sai na kasa tafiya,saboda tsabar jirin da nake ji

"Wuce mana!" Ya daka min tsawa

Ina d'aga k'afata na tafi luuu,na fad'a kanshi gabad'aya

"Bura'uba!" Ya fad'a da k'arfi,sannan ya hankad'e ni,Allah ya taimake ni a gado na fad'a, sai kuwa na gyara kwanciyata na lumshe ido.

"Yau na shiga uku ni Muhammad!" Na ji muryarsa sama-sama

Babu zato na ji ya shek'a min ruwa a jikina,Ina bud'e ido na gan shi tsaye da bokiti ya na huci,na tashi a firgice na ce"ka yi hak'uri don Allah, zo ka raka ni gida,ko kuma ka bar ni,na kwana anan wallahi gobe zan tafi".

Ya dafe goshinsa ya na wani irin huci.Can dai kamar wanda aka yiwa umarni kawai ya zo ya sungume ni,ya sab'a a kafad'a,dama ba wata k'iba ce da ni ba,bare na yi nauyi,ya yi waje da ni.Don dole na wartsake saboda wani sanyi da nake ji,sakamakon rigar jikina da ta jik'e jak'ab,sad'af-sad'af haka ya dinga tafiya da ni a kafad'a,ya na jera min Allah ya isa,har mu ka kusa fita daga falon.

"Salim!" Ya tsaya cak! Jin muryar mahaifinsa.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya furta a sanyaye,sannan ya dawo ya ajiye ni a kujera ya durk'usa,ya saka gwuiwowinsa a k'asa. Taku d'aya bayan d'aya mutumin ya k'araso har gaban shi, murya a sanyaye ya ce"Salim yaushe ka fara satar mutane a cikin gidana?"

Salim ya runtse ido bai yi magana ba. Ya daka masa tsawar da ni kaina sai da na firgita na wartsake sosai,na gyara zamana, ya ce "da kai na ke magana!"

Salim ma ya firgita ya ce"na rantse da Allah Abba..."

Bai k'arasa ba ya katse shi da fad'in"rantsuwa na tambaye ka?"

Ya sunkuyar da kai ya ce"wallahi Abba ban san wanda ya kawo yarinyar nan d'akina ba,ai ka ga dai tare muka shigo gidan da ku,ina zuwa na tadda ita a kwance,na rantse da Allah Abba".

Abba ya ce"to to to, wato aljanu ne su ka kawo ta ko? Idan gaskiya ne ai tun lokacin da ka ganta za ka zo a guje ka sanar mana,ba ka yi tunanin ko aljana bace yanzu da ka kinkime ta? To ina ma za ka kai ta da ban fito ba?"

Kafin Salim ya kai ga magana Ammi ta fito ta na fad'in "wai hayaniyar me nake ji cikin dare?"

Sai ta zaro ido ta na kallona ta ce"wacece wannan?"

"Amsar wanda ya kawo ta na ke jira!" Abba ya fad'a, ya na zama a kujera

Ammi ta kalle ni da kyau,sannan ta dafe k'irji ta ce"mun shiga uku! Wannan ai k'awar Baby ce,Nuratu ko?"

"A'a Zinatu,ita ce,k'awar Baby ce" Cewar Salim da rawar murya.

Abba ya ce"zance ya fara fitowa,ashe har sunanta ka sani?"

Ammi ta koma da sauri,sai ga ta sun fito tare da Baby,ta na murtsuke ido,alamar ta fara bacci.Turus! Ta ja ta tsaya,ba tare da ta k'araso inda muke ba, ta nuna ni da yatsa ta na fad'in "Zi zinatu?"

Na runtse idona hawaye suka zubo,sannan na sunkuyar da kai

"Tambayar ka mu ke yi,me ya kawo mace d'akinka?" Cewar Abba

Salim ya ce"wallahi Abba ba ni na kawo ta ba,kuma ban san wanda ya kawo ta ba".

Sai Abba ya juyo da kallonsa gareni ya ce"ke maganar da ya fad'a gaskiya ce?"

Na d'ago,mu ka yi ido hud'u da Baby,da ta k'ank'ance ido ta na kallona,na maida duba na ga Salim,na ga idanunsa taf da k'walla

Na sunkuyar da kaina k'asa na ce"ba gaskiya bane,shi...shi ne ya kawo ni" Na fashe da kuka

Wallahi da na san haka abun zai kasance babu yanda za a yi na yarda da wannan aikin,ban gama tunani ba na ji muryar Abba "to kidnapping d'inki ya yi?"

Salim ya kalle shi da sauri ya ce"haba Abba!"

"Yi min shiru!" Cewar Abban

Sannan ya kalle ni ya ce"biyan kud'in fansar aka yi,shi ne zai maida ki gida ko?"

Na girgiza kai alamar ba haka bane.

Abba ya ce"to me ya yi miki?"
Chapter 17 · 0% Book details