← Book details Matar Habibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 9

Sashe 9

Matar Habibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Wallahi karya yakeyi miki..."

Take fadi har lokacin tana dariya

"Wato zama yayi yana shirya miki drama ke kuma kika hau? Auren hadin shekara mai zuwa ma kina iya ganinta da lodin shagamu, in babu kenan, ya mika mata ta karbe da hannu biyu, yazo yana shirgaki"

Wannan karin su duka sukayi dariya banda Aziza da maganar ta bata mata rai sosai

"Meye kuma shagamu? Kefa Nabila kina da matsala"

Mimi tace

"Ciki mana, ba haka suke zuwa suna samun su Aziza suna shirga musu karya ba, yanzun daya shiga gida zakiga ba zai sake waya dake ba sai gobe idan ya fito, makirin"

Fuska sosai Aziza ta sake daurewa

"To ni ba waya ba, wallahi har video call munyi dashi jiya da daddare, yana gidan nashi kuma balle wata waya"

Hassana tayi mata wani kallo

"Video call da daddare? Ita matar tashi tana ina?"

Dan murmushi tayi

"Nace miki fa wata dusa ce yake aure, tana can tana baccin asara mana"

Aziza ta bata amsa sunayin dariya tare da Nabila, amman banda Hassana da fuskarta ke kara hadewa waje daya

"Amman kinsan daga ke harshi baku kyauta mata ba, saboda abune da idan akayi miki shi ke ba zakiji dadi ba"

Mima ce ta karbe zancen

"Babu wani rashin jin dadi, aina dauka shirga mun kawa yakeyi, in har yana video call da ita a gida to da gaske waccen batama san ciwon kanta ba balle har tayi muhimmancin a wajen miji, idan irin wannan wawayen matan ne to fa kwace miji a hannunsu ba zaiyi wuya ba, ke dai kawai ki shiga da shirinki"

Ganin kome zata fada ba zasu taba fahimtarta ba,sai tayi shiru, amman ita tayi samari masu mata, bama guda daya ba. Ita asalima bataso ka kwaso mata maganar matarka, sannan in dai ka shiga gida, tasan lokacin komawarka gida yayi, koya zaka kirata ba zata amsa maka ba, da yake da anyi isha'i in ba wani abu zatayi ba, kwanciya takeyi tai bacci, ba'a wannan chatting din daren da ita sam. Tana kokarin kiyaye kin yin duk wani abu da ba zataso ayi mata ba a matsayinta na mace to kar tayiwa wata macen.

Sai ta cigaba da fere doyar da takeyi tunda daman suna tsakar gidane

"Duk dani dai in ba kaddara ba auren mijin watan nan bai kwanta mun ba"

Aziza ta kalli Mimi

"Nifa na kasa gane wannan maganar ta mijin wata, waishi namijin inace don mace hudu aka halicce shi? Sai wata ta kwakume tace ita kadai zata rayu dashi, ni wallahi babu wani mijin wata, mijinmu dai"

Nan fa musu ya kaure tsakanin Mima da Aziza da kowa yaki fahimtar dan uwanshi, ganin abin na neman zama rigima Nabila ta katse su da fadin

"Kuna da fadin, yanzun fa akayi azahar, kuna nema ku karar da dan energy din naku akan gardamar da banga amfaninta ba, kowa ba sai ya auri wanda yayi masa ba"

Kafin su amsa Hassana tace

"Ni iskancin kawo mun dinki a kurarren lokaci ma nake so ku duka ku bari, nayi muku magana kunqi jiko, to zaku sha mamaki wannan karin"

Su duka sai suka koma lallashinta, dan sun san Hassana, tsaf zata iya kin dinkawa ko da kuwa tana da lokaci, gashi sun kasa sake wani wajen dinkin, bayan kwarewar da tayi, suna samun rangwame saboda kawancen da yake tsakaninsu. Duk da haka Aziza da Nabila saida suka sake zantawa akan Baffa da suka tashi tafiya tunda hanyar su daya ce, acan ma suka bar Mima da yake ita bata da nisa da gidan Hassana din, unguwa dayace, layi biyu ne ya rabasu

A lokacin da Nabila take karawa Aziza kwarin gwiwar shiga gidan Baffa, da kuma karin dabarun da zatayi amfani dasu ta kamashi a hannu, wasu dabaru da take hadawa da fatan bawai ta kama Baffa kawai ba, a'a ta jijjige Jamila daga gidan gabaki daya ta rayu ita dashi su kadai. Shikuma yana can shago ulcer din da bashi da ita na neman duk wata hanya da zasu kulla zumunta...

********************** **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
************************* **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** **************************
Chapter 9 · 0% Book details