← Book details Matar Habibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 9

Sashe 8

Matar Habibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shikuwa ko bai fada ba ta tabbata ya ba saba'in baya. Ba tajin tarin dukiyar shi zasu lullube mata shekarun shi. Samarin kuma da suke tareta bata ma bata lokacinta akansu, tunda ta tabbata ba aurenta zasuyi ba. Baffa shine namiji na farko da yazo wajenta taji ya kwanta mata har cikin ranta, duk kuwa da taso ace yafi haka kudi, saboda Mummy da ta tabbata Baffan ba zaiyi mata ba, ya aka kare ma lokacin auren Jalila da Balarabe. Shisa Mummy ta tattara burinta da fatanta kacokan akanta.

Aziza itace 'ya ta hudu a wajen Marigayi Malam Ayuba da matarshi Rahanatu. Shi din Bafullatani ne dan asalin garin Adamawa. Neman kudi ya shigo da iyayensu garin Kano, da kuma rabon suma din arzikinsu yana nan Kanon. Rahanatu kuma 'yar Dawakin tofa ce ta asalin garin Kano. Haka iyayenta duka 'yan Kano ne. Ta taso cikin gidan yawa, mata hudu, su kuwa yaran gidan sun bawa talatin baya. Haihuwa ake a gidansu da ta zama gasa, duk da mahaifinsu ba mai karfi bane ba. Dan 'yana aiki ne a gidan sarki, da yana cikin masu gadi, da yake mutum ne shi mai shisshigi da tusa kai, haka ya dinga shiga da fice har saida aka maidashi bangaren kula da dawakai. Sannan wannan shisshigin nashi yasa yake samun alkhairi babu laifi tunda gwani ne kwarai wajen koda duk wani ahali na gidan Sarkin.

Kusan a cikin yaran gidan, Rahanatu itace tafi kowa haske da manyan idanuwa, hakan yasa mutane suke cewa tafi kowa kyau, da yake za'a iya cewa ta biyo halin mahaifinta, saita kara da iyayi da kuma son ace wata ce, da ta kafa rigima da naci saida aka sakata a makarantar bokon da har mazan gidan ba damuwa sukayi da ita ba. Ta kuwa rungumi fadin rai ta dorawa kanta, duk inda zata zauna saita san yanda tayi ta fadi cewa ita jinin sarauta ce. Yaran unguwa da aka taso tare kullum cikin gulmar wannan karya ta Rahane suke tunda mafadaciya ce ta gaske ba'a isa ayi a gabanta ba. Ko Rahanen ma ta hana a kirata dashi sai Rahanatu.

Tana aji uku a sakandire ta hadu da Ayuba, dan gaye dai-dai da zamanin shi. Yana da shagon saida kayan masarufi. Gashi Bafullatanin usul, fari sol dashi. Cikin kankanin lokaci akayi bikinsu, yana kuma yi mata hidima har ya zarta karfinshi wani lokacin saboda yanda take da son harkar karya. Dai-dai gwargwado tsaye yake kansu. Data nemi komawa makaranta bai tauyeta ba, dakyar dai ta hada takardun sakandire, dole ta hakura, sabodq hidimar gida data yara. Tana da cikinta na biyar ya rasu, bayan gajeriyar jinya. Wannan rasuwa ta kidima Rahanatu, gashi daga shagon nan sai gidan daya bar musu. Yara kanana, tunda a lokacin Khalifa ne kawai yake da shekaru goma, Anwar takwas, Jalila shida, sai Aziza uku, dan ta samu tazarar shekaru 3 ne a wannan karin. Bayan ta haihu ta samu namiji sai aka mayar masa da suna Ayuba suna kiranshi da Nur.

Sai ga takardun sunyi mata rana, shige-shigen mahaifinta da mutanen daya sani, sai gashi an samar mata aikin rubuta kati a Asibitin Aminu Kano. Kuma bata zauna haka da aikin ba, duk wata sana'a da zata kawo mata karin kudi bata sanya da ita. So take yaranta su haska sufi na kowa a unguwar tasu, su samu ilimi tunda ita dai taga ranarshi. Rayuwar karyar dai data dorawa kanta, Malam Ayuba kan nuna mata rashin jin dadin shi akan irin rayuwar lokacin da yake da rai, tunda yanayi mata komai, bayason yanda dai idonta yake kan wasu a cikin kawayenta, tana so ta taddosu ko ta zartasu. Yanzun da kasa ta rufe masa ido, ga aikin data samu, sai abinda yayi gaba.

Cikin yaran nata biyar kuwa, Khalifa ne ya fita zakka. Ya samu karatu zuwa NCE, yana aikin koyarwa, yanzun haka yana da mata da yaro daya. Ko kadan Khalifa bayason irin rayuwar da Mummy kamar yanda suke kiranta takeyi, ta kuma dora kannenshi akai. Ga Anwar nan, yana BUK a yanzun haka, saboda shi yace daman ba zai iya FCE ba, kusan yafi kowa jin kai a cikinsu, saboda shine sak ya biyo mahaifinsu, yana daga cikin matasan da suka rungumi mining din Pi lokacin da yazo, dan gani kasheni ne akan Pi, dan zaku iya raba jaha dashi idan kayi kokarin rage masa burinshi akan Pi. Haka yayi sa'a yana cikin wanda aka budewa yin kyc da wuri, saboda haka lokacin da aka fara bumburutun Pi saiya zamana ya samu kudin da bai taba rike irinsu ba.

Khalifa ya bashi shawara ya samu sana'ar da zai dingayi, suka zauna sukayi magana sosai, kuma Anwar ya nuna masa ya dauki shawarar, yana komawa gida, suka zauna da Mummy ya fada mata kudurinshi na da yayi niyyar yayi musu gyara ne a gidan, sai ta rushe duk wani tsari da Khalifa ya dorashi akai, sai gani yayi an dauko gyaran gida, gini ne na zamanin da, na kasa, sai akayi masa shafen suminti, dan haka katanga akaja bayan an ware daki daya akayi masa gyara na gaske, sai katangar ta raba wannan dakin da sauran gidan ba'a gyara ba, ya siyo wannan katon gate din aka kakaba a gidan.

Sauran Pi din yace ba zai siyar ba zai jira a shiga kasuwa dashi ne, dan abinda yayi saura ya fara saro gilasai, hulunan hana sallah da zobunan azurfa, daman yana dan taba siyar da takalma, yana samun rufin asiri dai-dai gwargwado dan kuwa Anwar ya iya kasuwanci, karya ce kawai takeyi masa cikas, tunda kudin maimakon yayi abinda ya kamata dasu sai a siyi turaruka ko takalma designers. A wajen Anwar dama Jalila a yanzun, da aji kunya gara an kwana da yunwa. Kawai wani hali da suke dashi su dukansu, suna son farin cikin Mummy, duk wani fata nasu na yanda zasu gatanta ne, ko Jalila tayi niyyar yin auren kudi yanda Mummy take so, sai ga Balarabe da suka fara wata irin soyayya mai tsayawa a rai duk kuwa da tarin talaucin shi. Haka Mummy naji tana gani ta hakura akayi auren.

Shikuwa Auta Nur yanda duk akayi dashi haka yake binsu. Jalila a yanzun haka ta gama diploma dinta anan Kano Poly, amman ita data samu mijin daya kwanta mata sam ba zatayi wani karatu ba. Aure take so, tunda ta tasa tasan ma'anarshi, ko yaushe cike take da mafarkin auren nan. Balle data kara samun babbar waya, tana cikin group din matan sirri na Facebook, tana bibiyar manyan bloggers a manhajar Instagram, sai ta karajin tanason auren, babu kuma abinda yafi burgeta irin ace yau ta mallaki kitchen dinta na kanta, tana dafa ma mijinta abubuwan burgewa itama ta dauki hotonsu ta shiga wannan trend din da ake yayi na 'ga abinda nake ciyar da mijina'.

Shisa duk shiriritarta, tunda Mummy tayi musu tsaye a bangaren boko dama Islamiyya, itace dai sai taga dama take zuwa Islamiyar lokacin, bata wasa da addu'a akan aurenta. Dan bata dagowa daga sujjada bata roki Allaah daya bata miji nagari ba, kuma tana da yakinin rokonta Allaah Ya amsa ya jeho mata Baffa. Duk da karsashinta ya rage lokacin da taji yana da aure harda yara uku, amman shi da kanshi Baffan ne ya kara mata karfin gwiwa, a bakinshi takejin shi da Jamila aure ne akayi musu na hadi, yanzun a tare da son da takeyi masa, akwai tausayi mai yawan gaske da yake bata. Ace matashi dan kwalisa kamarshi, ga rufin asiri yana dashi dai-dai gwargwado amman baiyi sa'ar mata ba.

A goman karshen nan batayi wasa ba wajen addu'a, harda Mummy take hadawa idan Baffa shine mijin nata, to abin ya kwantawa Mummy a rai. Tasan duk yanda zasu so juna da Baffa, in dai Mummy bata karbe shi da budaddiyar zuciya ba, ba zataji dadin zaman yanda ya kamata ba. Ai tana gani akan Jalila, duk wani abu da Balarabe zaiyiwa Jalila sai ta kushe, ko ita kuwa ya bada aka kawowa haka zata karba tana kushe abin da Balaraben ma gabaki daya. Wani zubin ma da kuka Jalila take barin gidan saboda kwarzabar Mummy akan auren nata. Shisa ba zata taba wasa da addu'a ba ita kam, tunda tasan babu wanda zai tausaya mata sama da Ubangijinta, to kuwa gara ta gurfana a gabanShi ta kai kukanta.

Yanzun a cikin kawayenta su shida, Aisha da Hassana duk sunyi aure, saura su hudu, ita, Mimi, Nabila da kuma Maryam. Sunfi dasawa da Mimi saboda yanayin rayuwarsu yazo daya, suna da son asan dasu a waje, gayu, dama karya, duk da ita Mimi suna da kudi, amman kudin nasu bai kai yanda ita take zuzutawa ba. Maryam yanzun haka ansa ranarta, Nabila ma anyi gaisuwa, shiya karawa Aziza jin kamar ta janyo Baffa yazo ayi magana tasan cewa da gaske yakeyi, yau ma sunyi zasu hadu a gidan Hassana,ita, Mimi da kuma Nabila, tunda duk Hassana dince takeyi musu dinki. Ta kware sosai, haka kuwa akayi, suna cikin hira ne, Mimi take basu labarin saurayin da tayi Nawaf

"Nifa bawai baiyi mun bane ba, yanda yake isata da hirar matarshi da yaranshi shine abinda yasa duk ya fice a raina, to tunda yana son matar tashi uwarme ya kawo shi wajena?"

Hassana tayi dariya

"Ke dai Allaah Ya shiryeki, ai wannan alama ce mai kyau, ba wai hirar matar tashi ba da yakeyi miki, yanda yake nuna miki iyalanshi ma da muhimmanci a wajenshi, kema sai kiyi fatan idan abin ya tabbata Allaah Yasa kiyi muhimmancin nan"

Kai Nabila take girgizawa

"Koma menene, karka kawomun maganar matarka, babu ruwana da ita, kazo muyi hira kan abinda ya shafemu, nifa shisa sam bana son ma in kwasowa kaina mijin wata, duk yanda zakiyi dashi sai an samu damuwa, wannan makirar matar tashi saita kawowa soyayyar taku wani cikas din"

Aziza da take jinsu ce tace

"Bafa kowacce ba, wata ma bata da wannan muhimmancin a wajenshi, kinga kaman Habibi na, wallahi har tausayi yake bani, saboda dama can shi ba auren soyayya sukayi ba, wata dusa ce aka hadashi da ita, hakuri kawai yakeyi, shisa nake ta shiri, dan na tabbata kwace shi a hannunta ba wahala zaiyi mun ba"

Wannan karin Nabila ce tayi dariyar harda kyakyatawa
Chapter 8 · 0% Book details