Sashe 2
Matar Habibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun tana tunane-tunane har bacci ya kwasheta, rigimar Nana ce ta tasheta wajen karfe takwas da rabi, saita mike gabaki daya, tayi mata wanka, ta shiryata, tukunna ta hada mata shayi ta zuba mata a kofinta ta bata, ta kama hannunta zuwa dakinsu Asaad, ta lekasu, bacci sukeyi daga shi har Arif din. Idan akwai abinda take kara godewa Allaah akai shine yanda in dai babu makaranta sukeyin baccin safe, tana yawanjin iyayen yara na korafin yanda suke tashi da sanyin safiya idan babu makaranta, amman ita dai Allaah Ya duba mata. Ta gyara musu labulen dakin, taja hannun Nana suka nufi kitchen, saida ta zaunar da ita akan kujera irin ta katakon nan a cikin kitchen din tukunna ta hada wanke-wanke.
Ta gama tana goge wajen Baffa ya fito, ya shirya cikin kananun kaya, fuskarshi fayau, yayi kyau kamar ko da yaushe, zuwa yanzun kuma ta tabbata bawai a idanuwanta bane kawai Baffan yake da kyau, tunda gashi nan ya haska a idanuwan wata ma
"Sannu da aiki"
Yace mata, ta amsa shi da
"Yawwa Babansu..."
Kamar yanda ta lakaba masa, shikuma ya kirata da
"Mamin yara"
In yanajin nishadi, gaisuwar safen da basuyi ba dazun ita tayi masa ya amsa a sanyaye yana dorawa da
"Zan fita, saboda nasan aiki nacan ya cushe mana"
A jikin doguwar rigarta dinkin bubu ta kara goge hannuwanta da suke da danshi tana fitowa daga kitchen din
"Allaah Ya tsare Ya bada sa'a"
Ta fadi tana rakashi har wajen mashin dinshi, ita ta bude masa gate tunda ba maigadi ne dasu ba, saida ya fita ta mayar da gate din ta rufe, ta koma ciki.
*
Karfe shida da kwata tagama komai tunda ba wani abu mai wahala tayi ba, doya fa kwai ta soya, tayi zobo, tana da sauran dafaffen nama, tayi miyar ganye, dan wannan tun safe ma tayi ta, saita tuka tuwon shinkafa dai-dai cikinsu, kuma ita da wuri take fara aikinta koma meye zata dafa kuwa, bataso ana shan ruwa tana kitchen sai dai bacin rana, sai su Asaad da Nana da suke binta, Asaad nata yi mata surutunshi kan abinda batajin ta fahimta gabaki daya, wani tsohon labarine akan yanda littafinshi ya bace a Islamiyya
Tana kwasar komai zuwa falo, Arif yana nan zaune akan kafet yana kallon MBC3, Baffa kuma yana kan doguwar kujera a kwance kamar gawa, ko mintina goma baiyi da shigowa ba, sannu da zuwan da tayi masa ma da kai ya amsa, daga shi har mashin din kamar zasu tuntsire, idanuwan nan sun shige ciki, yayi zuru-zuru, ko dasu Nana suka dinga masa oyoyo ma dan rikesu yayi kadan batare da yace komai ba
"Kuzo nan Babanku yau ya gaji, karku dame shi"
Sai suka kyale shi din kuwa
"Ka tashi an kusa kiran sallah"
Tace tana kokarin danne dariyar da take neman kwace mata
"Barni a kwancen nan, ki dai cikamun jug da koma menene kikayi mana na sha dan Allaah, ki matsomun dashi kusa, ki kuma zubamun abinci, yau inaga a gida zanyi Magriba"
Saida dariya ta kwace mata, tun asali daman Baffa bashi da jumurin yunwa, dan azumi daga Ramadan, sitta shawwal sai kuma na arfa yakeyi, bayansu baya karayin wani azumi
"Karka bada maza mana"
Cewar Jamila tana karayin dariya
"Ke ba zaki gane ba..."
Dakinta ta shige bayan tasa su Asaad da Nana sun zauna kusa da Arif, ta dauro alwala tukunna ta fito, bata biyewa Baffa ba, ta samu kofi madaidaici, ta zuba masa zobo, sannan ta hada masa doyar ma a plate. Ya kuwa tashi zaune yana karbar kofin
"Wai har yanzun ba'a kira ba?"
Kafin ta amsa sukaji kiran sallar kuwa, nan da nan ya kwankwade zobon hannun shi, jikinshi har rawa yake lokacin daya sauke kofin ya dirarwa doyar
"Baba kaci a hankali, babu kyau cin abinci da sauri ko Mami?"
Asaad ya fadi
"Bari ka fara azumi tukunna Asaad"
Dariyar dai suka sake bawa Jamila, ta tashi ta tafi dan ta gabatar da sallar magriba yanda zatayi buda bakin cikin natsuwa. Sanda ta dawo a kwance ta samu Baffa
"Kwanciya ka sakeyi?"
A hankali yace mata
"Cikina ke juyamun"
Wani abu na rashin jin dadi ya tsarga mata, cike da tausayawa take ta jera masa sannu, doyar ma data dorawa buri saita kasa ci da yawa, ta dai zubawa yaran, zobo daman kowa na da robar shi da take zuba musu saboda a kofi za'a iya zubarwa a sakata aiki. Itafa ba haka taso ba, kawai dai taso ya dan sha wahala ne kadan, azumin ya gasa shi, bawai yayi ciwo ba. Sai gashi sallar Magriba a gida yayita, ya samu ya lallaba Isha'i saboda Tarawih. Daya dawo yasa ta zuba masa tuwo, saita tashi dansu Asaad da wuri suke kwanciya, kuma saita tsaya tana biya musu addu'ar bacci suna maimaitawa duk da sun haddace, ta karayi musu wata tukunna, ta goya Nana, dan itace take hirar dare wani lokacin
Sanda ta koma falon Baffa ta samu rike da wayarshi, da alama ranshi a bace yake, tana zama yana mikewa ya nufi dakinshi, tana juyo yanda ya turo kofar garam kamar itace ta bata masa rai
"Allaah Ya kyauta..."
Jamila ta fadi, ta sauko Nana, ta janyo kulolin gabanta, a cikin kwanon da yaci tuwon ta zuba itama, tana ci tana bawa Nana itama, suka gama ta sake goya Nana dan tanaso ta kimtsa wajen kafin su kwanta. Kuma hasashenta ya zama gaskiya, ran Baffa a bace yake. Gabaki daya yau tunda ya fita shago komai ya rincabe masa, ya samu yaran shagon nashi sunata aiki, danma sun rufe karbar dinkin sallah tun saura sati biyu azumi, kuma shi yayiwa kanshi alkawari tuntuni, duk runtsi ba zai dinga kwana a shago yana dinki ba. Suna cikin aikin aka dauke wuta, tun jiya Gen dinsu yaketa wata qara, yau ma sai yaki tashi, daya kira Sani dan yazo ya duba musu sai yace masa sunje wata gaisuwa baya ma cikin garin Kano, sai yammaci, zaizo ya duba bayan shan ruwa, dan haka dole yayi abinda bayaso, aiki da keken dinki wanda bana wuta ba.
Zuwa la'asar duk ya zazzage dan abinda yayi saura a cikinshi, ga ciwon cinyoyi da yakeji duk sun rike, kwata-kwata baima samu natsuwar danna waya ba, yama manta a silent ya sakata har sai bayan ya dawo daha Tarawih din nan, sai abin ya fado masa, ya riga yasan dole zai sha mita wajen Aziza. Yana duba wayar kuwa ya samu ta kirashi babu adadi, ga sakonni ta text da WhatsApp ta bar masa har yana rasa ta inda zai fara karantasu, sai kawai ya fara da tura mata da gajeran sako
"Ayimun hakuri Babe, yau abubuwane suka rincabemun a shago, wayar kuma tana silent. Nayi missing dinki da yawa"
Saida ya tura ya fara bin nata sakonnin, sai kuma zuciyarshi ta buga daya tuna yau yayi mata alkawarin zuwa yayi buda baki a wajenta, tun kwanaki biyar da suka wuce sukayi wannan tsarin, ya tabbata ta shirya masa shagali, lokaci daya yaji ranshi ya baci, musamman ma da ta dawo masa da sakon daya tura da
"Ka kusa? Inata jiranka tun dazun. Gashi har tara saura"
Yana shirin kiranta ne Jamila ta shigo, shisa ya tashi ya shiga dakinshi yana addu'ar Allaah Yasa karta biyo bayanshi, yasan halinta da naci wani zubin
"Dan Allaah kiyi mun hakuri Aziza, dan Allaah..."
Yake fadi cikin magiya da kwantar da kai saboda yanda Aziza ta birkice masa, kamar ma kuka takeyi
"Ni ba sai kaci anan ba, kazo ka dauka kawai dan bansan yanda zanyi da abubuwan nan dana shirya maka ba"
Muryarshi ya karayin kasa da ita
"Na fada miki da zazzabi na dawo, yanzun haka ina cikin bargo a kwance, dan Allaah kiyi hakuri, ki sakamun komai a firij, na miki alkawari gobe In Shaa Allaah zanzo da wuri ma"
Wani shiru ya ratsa a tsakaninsu kafin tace
"Hmmm..."
Gabaki daya a gajiye yake jinshi, bayajin ma yana da cikakke karfin fita da mashin din daya riga ya shigo dashi, balle harya falla unguwarsu Aziza
"Ke kinsan babu yanda za'ayi haka kawai da gangan inyi missing din abubuwan da nasan kin shiryamun, kinsan yaushe rabon da inji wani abu mai dadi a bakina?"
Cike da shagwabarta da take kara narkar dashi tace masa
"Habibi saboda zuwanka fa nace yau 'yan gidama suci albarkacinka nayi tortilla da sauce din kwai"
Duk da in za'a tsire shi baisan meye tortilla din ba, amman yanda ta fade shi tanayi kamar zata taune harshenta yasa Baffa hasaso wani abu da yaji naman kaza a cikin kanshi, ga kuma kwai data kira
"Duk ki ajiyemun dan Allaah..."
Bai sauke wayar ba saida ya tabbata Aziza ta hakura, musamman daya fara dauko mata hirar daya kula tafi faranta mata rai akan komai, hirar yanda in ta shigo gidanshi zata wanke masa takaicin rashin iya girkin Jamila, za kuma ta zame masa fitilar daya jima yana nema, a takaice dai, Baffa yace mata
"Kina saka inaji kamar sai yanzun zanyi aure Aziza, kamar banma san iya abubuwan da na rasa ba sai yanzun da kika shigo rayuwata..."
*
Maza nawa ne irin Baffa?
Mata nawa ne irin Jamila?
'Yan mata nawa ne irin Aziza?
Kun shiryawa wannan tafiyar kuwa?
#LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano.
9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan
Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani
*
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
MATAR HABIBI
2
(Free page)
Yau kam fuskarshi ta nuna rashin jin dadinshi sosai
"Nifa naji wani Malami na wa'azi in dai har sallar dare zatasa ka makara gara ka hakura da ita"
A nutse take kallonshi
"Babansu ai ana maganar sallar asuba ne, yau kuma bamu makara ba yanzun ma ake shirin tayarwa"
A hasale ya amsa ta da