← Book details Matar Habibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 9

Sashe 6

Matar Habibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da haka saida ya kara bata lokaci yana lallashinta da yi mata alkawura kala-kala duk da yaji an tayar da sallah. Ya ajiye mata dubu goma cifa, sababbin yan dubu-dubu. Yaji dadin yanda ta manta da hadashi da wannan cheese ball din. Daya fito ne ma sukayi kicibis da Jalila tana tsaye, bayanta goye da karamin Jawad, sai Jabir da Jafar da suke gefenta, ga wata katuwar leda data ajiye a gabanta, zuciyar Aziza ta tsinke, kar dai har yanzun Balarabe baizo ya daukesu ba

"Habibi ga Adda Jalila ku gaisa"

Cewar Aziza cikin karfin hali ganin idanuwan Baffa akansu ya fara sauka, ta kalli Jalilan tana fadin

"Matar Officer ga Habibina"

Duk da Baffa yasan ya girmeta haka ya dan rage tsaho yana gaishe da ita, ta amsa shi fuska a sake

"Kinga kila ma ciki zan koma, yanzun Officer ya kirani wai kaman ya taka abune tayarshi tayi faci"

Jalila ta fadi

"Babur din Baba ne yayi faci?"

Jabir ya fadi yana kallonta cikin maganarshi da bakowa bane yake ganewa, Aziza tayi saurin kallon Baffa da alama baiji abinda akace bama, dan hankalinshi naga masallaci da har anyi raka'ar farko, tunda da alwalarshi yacewa Aziza

"Bari kiga inyi sallah kafin in wuce, lafiya kalau mashin dina idan na barshi anan?"

Kai ta daga masa da sauri, dan unguwarsu tana da tsaro sosai duk kuwa da yawansu, akwai karancin sace-sace musamman irin wannan lokacin ma da jama'a suke hada-hada. Baffa na shigewa tana juyo karar mashin din Balarabe tun daga kan kwanar layinsu kamar babu salansa a jiki, suka hada ido ita da Jalila cike da takaicin da har yau basu daina shakarshi akan wannan mashin din nashi ba. Saikuwa gashi nan ya karyo kwanar, kana hango sabon uniform dinshi shar

"Officer take aure ashe, soja ne ko dan sanda?"

Baffa ya taba tambayarta da tace masa tana gidan Jalila din tana kiranta da Matar Officer, farko-farkon haduwarsu, babu shiri ta katse hirar da fadin

"Minti daya Habibi"

Ta kashe wayar, tunda ai ba zata sharo masa karya ba, idan aurenta zaiyi dole wannan likon zai cire, ta ina zata fara ce masa Balarabe dan karota ne?. Ko gaisawa bata tsaya sunyi ba, dan kafin ya karaso ta cewa Jalila

"Adda sai munyi waya"

Ta shige gida abinta. Baffa kuwa ana sallar nan kamar an kara zazzage masa hanji haka yakeji, gashi limamin nan kamar ya zabi yayi tilawa ne a sallar asham din, kafafuwan Baffa har sanyi sukeyi kafin ayi ruku'u. So kawai yakeyi a idar ya karasa gida ya dirarwa koma menene Jamila ta tanadar masa, Allaah Yasa tayi zobo, dan yau jinshi yakeyi kamar baisha abinda ya kai masa inda ya kamata ba.
#LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778

Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano.

9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan

Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani

*

Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode

MATAR HABIBI

4

(Free page)

Adai-daita na ajiyeta, ta dauki katon kwandon data hada komai a ciki, don da taga almajiri ma shi zata ba ya dauka ya tsallakar mata dashi saita bashi ko Naira dari ne sadaka. Kwandon yayi mata nauyi, haka ta kinkima saboda wani mai mota daya gansu a tsaye, mata su wajen biyar saiya daga musu kafa suka samu suka tsallaka, sai nishi takeyi, ta ajiye kwandon a kasa dan ta numfasa. Ta godewa Allaah da tabarwa Rufaida har Nana. Da yake ba kwiya gareta ba, su Asaad na dauke mata hankali ta samu ta silalo, ai da taji a jikinta da daukar wannan kwandon. Yanda Baffa yace ba zai dawo da wurin nan ba, sai kaga har goma ta wuce ma kafin ya shiga gida, tasan yana son shan ruwan shayi wani zubin, saita hada masa shi yasha kayan kamshi. Shisa kwandon ya kara nauyi.

Kamar ance ta juya, ta hangi Baffa yana daukar mashin dinshi, sai dai ba kayan daya fita dasu bane a jikin nashi, yadi ne yanzun, kuma daga inda take taga yayi kyau duk kuwa da bai saka hula ba. Babu yanda za'ayi ta ware baki ta kwala masa kira, bata kuma fito da wayarta ba. Hakan yasa ta dauki kwandon, nauyin shi na hanata sauri yanda ya kamata, sai dai kafin ma ta karasa Baffan ya haye mashin dinshi yayi gaba, tunda baya ya bata ya fice ta dayan bangaren shisa bai ganta ba

"To ko dai gida zai koma?"

Wata zuciyar ta raya mata, sai tayi tunanin ta karasa shagon taji. Haka kuwa akayi, Abbati ne ya fara ganinta tunda yana bakin kofar shagon a tsaye da kankana a hannunshi

"Maman Asaad"

Ya fadi yana dorawa da gaisheta a daburce

"Naganshi ya fita ma yanzun, kar dai gida ya koma, yace mun zaku dade yau a shago saboda akwai ayyuka"

Sai Baffa ya juya yana kallon Isma'il cikin neman dauki, dan shi karya bata cikin dabi'unshi, ko da kuwa ta kare kaice, kalamai ma gabaki daya basa yawaita a bakinshi.

"A'a um...yaje ya dawo ne"

Cewar Isma'il shima sarkin maganar yau da alama ya rasa ta cewa, kuma hakan nada nasaba da yanda Jamila takeyi musu kwarjini. Macece da nagartarta take shimfide akan fuskarta. Yanayinsu, da kuma yadin jikin Baffa ta hada waje daya a cikin kanta, kwakwalwarta ta dai-daita mata lissafin. Shisa ya kirata yau kenan? Shisa yayi mata kirki? Saboda zaije zance wajen AZ dinshi kenan, acan zaiyi buda baki kome? Ita tana can tana kitimillin hada masa, banda ruwa da dabino bata saka komai a cikinta ba tanata sauri ta fito, ashe tana da rabon ta cika cikin nata taf da bakin ciki.

"Na bar yara a makota, ga kayan buda baki nan, bari in wuce"

Saboda jikinsu a sanyaye yake su duka, kamar sune suka saka Baffa tafiya zance a ranar yau, sai suka kasa wani yunkuri har Jamila ta juya, ta tare napep, zuciyarta na wani irin tafasa. Numfashi kawai take maidawa har suka isa, dari biyar din data bashi ma ca tayi ya rike canjin ta wuce ta shiga gidan Rufaida, taji dadin samunta ta tayar da sallah dan kwata-kwata bata son wani dogon surutu, ta sabi Nana tana riketa a hannu ta cewa su Asaad

"Ku taso mu tafi"

Bata san ko muryarta bace ko yanayin fuskarta yasa duk suka shiga hankalinsu. Tana zuwa kofar gida kuwa ta samu Yayarta Yasmin da take tsaye tana danna waya

"Yanzun nake shirin juyawa dan nagaji da kwankwasa kofa..."

Murmushin karfin hali Jamila tayi

"Kai su Maman Danjuma babu hakuri"

Yasmin din tayi dariya. Tun haihuwar Yasmin ta biyu, ta kwallafa rai akan idan namiji ne za'a saka sunan mahaifinta Abubakar, har shafa cikin take tana fadin Assadiqu kamar yanda take da niyyar kiranshi, ta shiga watan haihuwarta, Kanin mijinta ya rasu, kawai tana haihuwa da yayi masa huduba, bata kawowa ranta ba Abubakar din ya saka ba, sai ranar suna taji ana

"Ashe yaro sunan margayi yaci, Allaah Sarki Ya'u"

Ta tabbata da ba'a zaune take ba sai jiri ya tikata da kasa, ita tun yana da rai ma ba shiri sukeyi ba, duk da ance babu kyau tado da halayen mamaci musamman wanda ba nagartattu ba, shi kam mutum ne mai tsugudidi, sannan ya saka mata ido ainun, duk wani husumi da zai taso tsakaninta da dangin mijin nata in aka bibiya shi ya kitsa zancen. Kamar mace haka yake da gutsiri tsoma. Da yake kuwa ranar Juma'a ne ta haihu, saita fara kiran yaron da Danjuma, wani suna da mijin nata da dangin shi suka tsana saboda sunce akan meye zata boye sunan yaro, shima mijin da yayi magana sai tace masa

"Ni da nayi dakon wata shida, nayi nishin nakuda ai ayi mun alfarmar kiran yaro da sunan daya kwantamun ko? Tunda ban hana kowa ya kirashi da sunan da aka rada masa ba"

Haka dole ya hakura ya kyaleta, tunda yasan hali, jan maganar kamar neman zunguro sama da kara ne tunda har batace masa ta tafasa ba akan sauyin sunan da aka samu. Tun daga lokacin ta tashi daga Adda Yamin a wajen kannenta ta koma Maman Danjuma, tun suna kiran sunan da zolaya har yanzun kusan kowa ma haka yake kiranta dashi. Gidan Jamila ta bude suka shiga, su Arif suka gaishe da ita

"Mu karasa ciki mana"

Kai Yasmin ta girgiza

"Keni ba zama zanyi ba, Yaya Babangida ne ya hadani da aiki, ga sakonki nan"

Cewar Yasmin tana mika mata ledar data shigo da ita, kafin ta fara kokarin sauke jakar kafadarta, sai ga wuta sun kawo, daman fitilar caji ce da take dorawa sama, ita ta haske tsakar gida, saita wuce daki da yara ta kunna musu tv ta dawo, Nana ce kawai ta makale taki sauka. Kudi ne Yasmin ta mika mata, tasa hannu ta karba

"Kudin dinkin kine yace a baki"

Haka kawai sai taji hawaye ya balle mata, wani irin rauni ya mamaye ta

"Jamila, ikon Allaah, meya faru kuma?"

Da sauri tasa hannu ta goge hawayen, kawai tana hasaso tarin kauna da hadin kan da suke dashi, yanda ta fahimci ba sai iyayenka nada kudi bane kake kasancewa dangata, ita kam 'yar gata ce, sun taso cikin tarin kulawa, yanzun gashi aure ya rabota da gidan nasu, ya kuma sakata yunwar wannan kulawar. Tunda in ba yunwarta da takeyi ba, wayar kasa da mintina biyu da sukayi da Baffa itace fa tasa ta son faranta masa

"Wai menene? Kinsan banason wannan shirmen banzar naki"

Yasmin tayi maganar cikin fada, amman zaka iya tsintar damuwa a kasan muryarta. Saboda tasan halin Jamila, abinda zaisaka hawayenta zuba ba karami bane ba, akwai kujerun roba guda hudu, wata cikin wata daga can gefe, Yasmin ta karasa ta dauko guda daya, duk da batayi niyyar zama ba

"Kiyi mun magana tunda dai ai baki da wanda suka fimu"

Numfashi Jamila taja tana saukewa

"Baffa ne"
Chapter 6 · 0% Book details