← Book details Masarautar Jondan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 9

Sashe 2

Masarautar Jondan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza mata kai yayi a sanyayye yace.
"Ya fita!"
"Allah ya bada na mora"
"Amin Ya Allah! Kuma an mata daurin mahaifa, amma dake Ubangiji yafi mu son abin cikin kinga mahaifar ta bud'e."

"Allah ya baku ikon cinye jarabawarku"
"Amin Ammah!"
Ofishin sa ya wucce tare da cire kayan jikin shi na aiki ya zauna a kujeran, yana me dafe goshinsa.
"Hakkinki SAFINAH yaki barina na huta! Yaki barina na sami Sallama, Ya Allah ka yafe min"
Tunda suka rabu da SAFINAH, matar sa tana da ƙaramin ciki a lokacin, bayan kwana biyu da rabuwar su, ne matar shi tayi barin wata biyu,, tun daga wannan ranar da zaran ta sami ciki toh baya wucce wata biyu zai zub'e, kuma duk irin kulawar da zasu bawa cikin bazai tsaya ba, yayi imanin da Allah kamar yadda ya zubda mata cikinta shine shima yake fuskanta. Ajiyar zuciya ya sauke sau biyu ya zubda na SAFINAH yau gashi na hudu ya zuba, tausayin matar shi yake, dan iya wahala tasha, yasan SAFINAH itama tasha wahalar da yafi nata.
Tunda shi yayi ta zubda na SAFINAH, a yanzun yayi dana sani yafi kwandon dubu, ya tsani kan shi yafi sau dubu, babbar burin shi yadda zai hadu da SAFINAH ya nemi yafiyarta, ko zai samu salama, a zuciyarshi. Gyara zama yayi tare, kurawa wayar shi ido Dr Kyari yake son kira ko zai same number SAFINAH kunya da laifin shi suna dawainiyya da shi, dan haka ya ajiye kudirin shi ya cigaba da Addu'a ko Allah zai sa a dace.

Mik'ewa yayi ya fita ya duba halin da take ciki, yana shiga ya samu tana ta barci tayi fayau, kamar wacce jininta ya kare, zama yayi tare da riko hannunta, ya saka a fuskarshi, yana cewa.
"Laifina ne! Ni na aikata Allah yake hukunta ki da laifina, ki yafe min Ni naja miki komai, gashi kin rasa d'anki, ki yafe min ko nauyin da yake kaina zai ragu,"

Mik'ewa yayi ya bar d'akin, cike da tausayinta, da lokacin da jinin ya fara zuba ce mishi take.
"Dr kayi wani abu don Allah kar na rasa baby a wannan karon Dr ka dakatar da jinin."

Duk da sun zo asibitin akan lokaci bai hana cikin zub'ewa ba, suna cikin jarabta sosai.

★★★
An gama duba Nannah aka samu babu komai a jikinta da jininta, dan haka suka baro asibitin ta tsinewa Zoyah yafi cikin kwandon.

.......
Ya juya daukar wayar shi idanunshi ya sauka akan sakon da Ta rubuta mishi, dauka yayi ya zauna sai da ya karanta tsaf, cikin sanyin jiki ya ajiye takardan.
"Ba yanzun kika so fita a rayuwata ba, SAFINAH tuntuni kike da burin haka, amma kaunar da kike min ya hanaki tafiya. Me yasa sai da idanuna suka rufe zaki tafi? Me yasa baki hakura kin zauna dani a haka ba, SAFINAH ina kewarki da Yarana, kin tafi kin barni cikin kad'aicin da kika."

Daukar park bag din shi yayi ya fito, haɗu yayi da Nannah. Tana kallon shi, cikin ki d'imauta tace.
"Ina zaka? Ko ka manta kai din shugaba ne?"

Takowa yayi har gabanta yace..
"Me zanyi da shugabancin da ya hanani fahimtar matar da tasani zama mutum, a da baki tuna dani ba! Sai da kika lalata tarbiyyar yar mutane sannan tazo ta miki sanadin gani na, amadadin ta samu jinjina da kambamawa, wai ita ce kika tsana, kuma kika tsamgwame ta shin Ammyn meye laifin SAFINAH? Meye tayi miki da zafi haƙa, Ni A sani na abin arziki tayi me yasa ya zame mata sharri."

"Har ka manta itace ta kashe maka yara biyu! SAFINAH da ta zage ni, kake magana akanta yarinyar da bata ji maganar iyayenta ba! Ka farka mana"

Kura mata ido yayi, sannan yace.
"Tabbas Kinyi gaskiya kuma Mahaifiyarta tayi gaskiya da tace Allah sai yabi mata hakkin Yarta da muka zalunta, Ammyn kece kike cewa SAFINAH taki jin maganar iyayenta bayan kece kika daurata akan wannan hanyar, kece kika nuna mata komai tayi dai dai ne, yau gashi kina kiranta sunan mara jin magana, nayi Imani da Allah SAFINAH bazata tana kashe abinda ta haifa ba, dan koni da nake Ubansu bazan nuna mata kaunarsu ba, shine kike tunanin zata kashe Yaranta Ammyna yarinyar da tasha wahalar rayuwa saboda suce zata saka musu guba, wai meye nayi haka na hadu da uwa Mara Adalci irin tabbas ke baki min Adalci ba shine kike tunanin itama bazatawa Yaranta ba."

"Amma ai kasan dole yaran ma su mutu tun da shegune, meye naka makin zafin dan a rage mata nauyin wulakancin da zata fuskanta."

Sake baki yayi yana kallon ta cike da mamaki, sannan ya mai maita kalmar da ta furta.

*Amma kasan dole yaran su mutu? Meye naka na ɗaukar zafi tunda shegune nauyi aka rage mata*
Kamar wanda aka make take lokacin da likitan nan da ya amshi apple a hannun Ablah ya dawo mishi, sai bayanin da Dr Fu'ad yayi mishi.
*Yaran an ciyar dasu guba ne? Sannan itama me nakudar guba aka bata, sai dai bata ci sosai ba dan babu abinda ya same yaron cikinta*

Kallon Nannah tayi sannan saka ya fita, har ya isa bakin kofa yace.
"Da hannunki a kashe min Yarana? Da Hannunki A ciwon Natashah? Ammyn na barki da Allah, Ammyn na bar muku Mulkin dan na ajiye, bazan muku hukuncin ba, amma Allah da kanshi zai hukunta ku."
Komawa cikin gidan yayi ya kuma diban abinda zai diba, sannan ya je ya saka a mota, daga nan gidan yarin ya wucce yasa aka fidda Bilal, ya mika mishi dukiyar shi, sannan yace.
"Daga Ni har kai dole mu hakura da Mulkin jordan domin yafi ƙarfin mu, matukar kace zaka yi sai ka rasa wani abu me daraja naka, kaje Sandia da Ummanshi suna jiranka, nima na bar barwa Ammar mulkin dan naga Adalci a cikin idanunshi."

Rungume juna suka yi sannan Bilal yace.
"Zan koma inda muka fito ne, Moscow ko zamu koma tare, sai mu sayi gida a can"

Murmushi Ashraf yayi sannan yace.
"Toh haka ma duk shawara ce, ka saya mana babba wanda zamu zauna da jama'ata dan akwai abokaina biyu."

"Ai idan ma da duk jordan nan ina tabbatarwa da Sarkin Jordan da yayi murabus sabida mace"

Murmushi yayi kawai sannan yace.
"Muje"

Haka suka jera har cikin masarautar, inda ya same Ghaniyu da Fahad sun had'a kan jama'an padar, shiga suka yi sannan ya nemi guri ya zauna.

Shiru yayi kafin ya mik'e yace.
"Natara kune dan ku fahimci abinda nake son nayi, Yau 24-5-2018 Ni Muhammad Ashraf bini Abdullahi bini Yasir na ajiye."
Shiru padar yayi sakamakon nauyin abinda zai fada, sannan ya cigaba da cewa.
"Na ajiye mulkin jordan baki d'ayan,. Na bawa Ammar bini Abu Zarri."

Toh fa ga Ashraf ya ajiye mulki, wata fata kuke mishi......

[3/26, 2:54 PM] +234 806 222 4030: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs  +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*

MJ3
4️⃣
"Ina me baku hakuri abinsa murabus din da nay, Ni kaina bani da yadda na iya ne."

   Muryan shine ya kama rawa, sannan ya d'ago kai ya kalle su sannan yace.
"Na rasa mata na biyu da yarana, don Allah ku manta na zama wani abu a cikin masarautar nan, don Allah karku nime dan yin haka zai sanya Ni a damuwam"
  "Insha Allah! Ashraf bazamu tab'a damunka ba, sai dai idan kujeran taki wanda aka bawa dole zamu nimeka tunda kana kuma raye, bawai ka mutu ba, ban ji dad'in abinda ya faru ba, amma Allah yasa haka shine mafi alkhairi."

          Jingina kai yayi sannan ya mika musu takardan, murabus ya juya gurin Ammar ya mika mishi hannu yace.
"Ina taya ka murna! Allah ya tayaka riko."

   Jingina kai Ammar yayi, yana zubda kwalla saboda tashin hankali dake cikin mulki, masifa ce idan baka bida  ita yadda ya dace ba sai ta kaika ga hallaka.

        Godiya da ban hakuri yayi musu sannan ya bar cikin padar, tausayin Mahaifiyarshi yake ji sabida shi ta wurga kanta cikin wannan matsalar, sai dai bazai tafi da ita ko ina ba, Oman yake son fara zuwa yaga halin da Natashah take ciki, kafin ya diro naija.
           A hankali yake tafiya suna bin bayan shi har inda Ghani ya ajiye motarshi, sannan suka bar Masarautar.
        "Sultan ina zamu nufa?!"
    "Gidan su Sandia inda Umma take"
          Sun isa gidan, suka tattauna da Mahaifin Sandia, sannan suka bar gidan. Dan Ashraf yace musu shi Oman zai je, zai bar Bilal a cikin Jordan dan iyayen yarinyar sun bashi aurenta.

         Tun kafin Ashraf ya isa Oman ya aikawa Amirah Khadijah cewa gashi nan zuwa,
       ★★★
   Shiru nayi ina kewar shi, wanda ya cika min zuciya, tsigar jikina har mik'ewa yake. A hankali cikin raina na ambace shi.
         *Ashuuna*
       Tunanin irin zargin da yake min ne ya sani jin kwalla sun cika min ido, tabbas Ashraf zargin nice na kashe yaranmu yake, meye yasa haka me yasa ya gaza fahimtar bazan kashe abinda nafi kauna a duniya ba, yarana nafi son su da komai, nafi kaunar su da komai.

   Kuka ne ya kwace min, na tashi zaune sai da nayi me isata sannan, na mike zuwa ban daki nayi uzurina sannan nafito.
Chapter 2 · 0% Book details