Sashe 9
Juyin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Maison De Curry, Souk Al Bahar, Sheikh Mohammed bin Rashid Blvd, Downtown Dubai, United Arab Emirates.*
*10:52 na dare.*
THE ADVENTURERS.
“Wai me ya faru ne?”
Ivana ta tambayi Arman da ya tarasu a restaurant ɗin, kuma ya zauna ya yi shiru ba tare da yace komai ba. Arman ya juya kansa ya kalli Fountain show dake nan kusa da restaurant ɗin, kuma ta tsakanin Fountain ɗin yana iya ganin dogon ginin Burj Khalifa.
“Yau saura kwana biyu zagayowar ranar da aka haifeni. Abby da Immi suna shirya shagalin zagayowar ranar”
Ivana da Adam suka dubi juna. Sannan suka kwashe da dariya suna tafawa, hakan ya sa Arman ya kallesu da mamaki.
“To ai duk mu ma mun san wannan. Dan mu ma muna shirya namu shagalin... Mi ye na damuwa a ciki”
Arman ya saka hannu ya shafa ganshi kansa dake a nannaɗe, sannan yace.
“Ba wai batun shagalin ne abin da yasa ma taraku a nan ba. Abby yana shirin danƙa min takardun shugabancin Alhadi... Kuma kun san cewa wannan shi ne abin da bana so”
Cak Adam da Ivana suka dakata da dariyar da suke, sannan suka dubi juna. Kafin Adam ya kalle shi.
“Man! Ni fa da za ka ji shawarata da ka karɓi shugabancin kamfanin nan. Kasancewarka shugaba shi ne burin mahaifinka na ƙarshe. Bayan duk abubuwan da ya mallaka maka a rayuwa kuma sai ka kasa cika masa wannan burin?... Burin da a ƙarshe kai ne wanda za ka amfana da shi”
Ya gyara glasses ɗinsa, sannan yace.
“Adam ina so na cika burin Abby, saboda ban taɓa neman komai a wurin Abby na rasa ba. Duk abin da na naima cikin gaggawa Abby ke mallaka min shi, dalilina na ƙin shugabanci shi ne, duk wani abu da zai sa a na min kallon nakasasshe ba na sonsa. Duk wani abu da zai zama silar da za a muzantani gudunsa nake, bana so ana aibanta ni Adam. Kuma ku duka kun san cewa ta dalilin wannan kamfanin Ammu Anwar da Faisal da kuma Sakina ke aibantani a ko ina... Shi ya sa nake gudun Alhadi”
Shiru ya ratsa tsakaninsu, dan duk abin da ya faɗa gaskiya ne.
“Arman”
Faɗin Ivana tana kama hannunsa.
“A ganina maganar mutane bai kamata tasa ka sare da rayuwa ba. Allah shi ne me bada lafiya, kuma idan ya so a yanzu zai iya baka lafiya. Kuma tun da kana iya gani da taimakon glasses me zai hana ba za ka jarraba bin abinda iyayenka ke so ba”
Ya girgiza kansa, Ivana da Adam suka sake duban juna. Sun san abokinsu da taurin kai, tun da yace a'a to fa ba zai sauya ra'ayinsa ba.
“Yanzu mi ye shirinka?”
Adam ya tambaya. Ya kallesu su duka biyu.
“Kamar yanda suke zato. Sam ba zan taɓa basu kunya ba, domin da ace ban san da batun shagalin nan ba da zan amince na je wurin shagalin, kuma idan ya bani takardar a gaban kowa zan saka hannu. Amma tun da har na sani ba zan je wurin shagalin ba”
“Me kake nufi?”
Ivana ta tambaya a mamakance.
“Zan bar Dubai a ranar da suka shirya shagalin, yayin da suke shirya shagali a nan ni kuma zan yi nawa shagalin a wata ƙasar”
Adam ya girgiza kai.
“Hakan bai kamata ba Arman. Da wannan abin da za ka yi sai ka fi basu kunya, fiye da ƙin amincewa ka sa hannu a gaban jama'a.”
“Adam ya zan yi?... Sam ba na son abin da suke so, na kasa fahimtar da su, ya suke so na yi?”
Suka yi shiru, tausayin abokinsu na kama su.
“Shikenan. Mun yarda da shirinka, amma ba za mu barka ka tafi kai kaɗai ba, duk inda za ka je za mu kasance tare da kai”
Faɗin Ivana tana kallon Adam, shi ma Adam kansa ya jinjina, alamun ya amince. Arman ya yi murmushi yana kallon abokansa biyu.
“Amma ina kuke ganin za mu tafi?”
“Tun da ni zan je ɗaukan hoto me zai hana mu tafi Nigeria?”
Adam ya tambaya. Arman ya girgiza kai, a lokacin da idonsa ya kai kan allon da zai sauya akalar labarin gaba ɗaya, kuma allon dake ɗauke da zanen ƙaddararsu. Wadda za ta yi juyi irin na kwaɗo, daga ruwa zuwa ruwan zafi. Lokacin da ya gama karanta sunan wurin a jikin allon, fatar bakinsa ta furta sunan dajin a hankali.
“Bayericher wald (Bavarian forest)!”
“Germany ke nan?”
Cewar Adam, Arman ya gyaɗa kansa.
“Dajin yana da kyau sosai. Sannan za mu shaƙata a cikinsa, kai kuma za ka samu abubuwan da za ka ɗauka a cikin dajin... Kamar dai wancan hoton!”
Ya ƙarashe yana nuna musu wani allo dake ɗauke da hoton Bavarian forest ɗin. Suka waiga suka kalli board ɗin a tare, allon dake ɗauke da zanen sauya labarin kowanne a cikinsu.
*House No 27, Street 45, Mirdif, Dubai*
IVANA POV.
Sanye take da yellow maxi skirt, da farar shirt, wadda a samanta ta saka denim jacket. Tana zaune a kan gadonta, yayin da take goge guitar ɗinta da hanki, Yumma kuma na shirya mata kayanta a cikin jaka, dan ta riga da ta sanar mata da cewar za su yi tafiya tare da su Arman.
“Ivana”
Yumma ta kirata tana saka wasu takalmanta a cikin jakar da take shirya mata kayan.
“Na'am Yumma”
Ta amsa tana ɗaga kanta, tare da kallon Yumman.
“Me ya sa Arman ba ya son ya karɓi abin da yake nasa?”
Ivana ta girgiza kanta tana murmushi, ta saka hannu ta ta saƙala gashinta a bayan kunnenta, sannan tace.
“Tun yana yaro kawunsa da wasu daga cikin 'yan uwansa suka raunata masa zuciya. Bayan nakasar ido da yake da ita sun ƙara masa da nakasar zuciya Yumma. Abokina yana da zuciyar zinare, yana son taimakon wanda ba shi da shi, duk da tarin dukiya da Allah ya yi wa mahaifinsa sam ba ya dubawa, domin ba ya nuna banbanci tsakanin mu da shi. Amma wannan raunin da suka yi a zuciyarsa yasa sam ba ya son zama shugaban Alhadi...”
Ta ƙarashe tana ɗaga kafaɗunta tare da taɓe bakinta.
“Da ace Arman zai karɓi shugabancin nan Yumma da an yi shugaban da ba'a taɓa yin irinsa ba”
Yumma ta girgiza kanta.
“Allah ya karkato da zuciyarsa kan kamfanin, su kuma Allah ya musu abin da suka masa”
“Amin”
Ta amsa dai-dai lokacin da wayarta dake chaji a kan side drawer ta fara ringing, hannu ta miƙa ta ɗauki wayar, ganin lambar Uwais Fazil ya sa ta ɗaga wayar, tare da karawa a kunnenta.
“Marhaba”
Muryarsa me sanyi ta faɗa daga ɗayan ɓangaren.
“Alo”
Ta faɗa tana murmushi.
“Shin zan iya ganinki?”
Sai ta kalli Yumma da ke shirya mata kaya, da alama sam ba ta lura da wayar da take ba. Sai ta sauƙa daga kan gadon tana saka toe wrap shoes ɗinta dake kusa da gadon, sannan ta fita daga ɗakin. Sai a sanda take sauƙa downstairs sannan ta amsa.
“Zan so hakan, domin ina sa ran zan yi tafiya nan da gobe...”
“Yanzu haka ina ƙofar gida me lamba 27, titi na 45, a tsakiyar unguwar Mirdif.”
Ido ta zaro tana rufe baki, sannan cikin sanɗa ta isa jikin windown dake kusa da ƙofa, ta ture curtain ɗin dake jikin windown ta leƙa. Daga nan inda take ta samu damar ganinsa, jingine a jikin motar da ya zo da ita. Yana sanye da baƙin sweat blazer trouser, me ratsin ja a gefe, da farar crew-neck sweater, wadda ya saka baƙar shirt a ƙasanta. Ƙafafunsa cikin garin sneakers. Gashin kansa na cikin askin high pade, sannan wayarsa kare a kunnensa, kuma suna haɗa ido ya ɗaga mata hannu, sai ta yi saurin sakin curtain ɗin tana dariya ƙasa-ƙasa.
“Ina jiranki”
Ba tare da tace komai ba ta sauƙe wayar, sannan ta koma sama da gudu. Har Yumma na tambayarta shin lafiya, ta amsa mata da tana zuwa. Guitar ɗinta kawai ta saka a cikin jakarta, sannan ta ɗauki canvas ɗinta ta saka a ƙafarta, ta tsaya a jikin mirror ta gyara gashin kanta. Sannan ta goya jakar guitar ɗin a bayanta, ta fita ba tare da mayafi ba, dan ta saba yin hakan kullum.
Ba ma ita kaɗai ba, a muslman 'yan matan larabawa ba kowacce ce ke saka mayafi lokacin da za ya fita ba. Mafiya yawan waɗan da za ka ga da mayafi a waje to matan aure ne, dan 'yan matan ba su cika yin hakan ba, shi ya sa idan aka gansu a waje za a ɗauka cewa ba musulmai ba ne, dan duk wasu ɗabi'u na turawa sun ɗauka sun yafa a jikinsu.
“Ina ya kamata mu je?”
Uwais ya tambaya yana duban Ivana dake zaune a kujerar gefensa. Yayin da yake tuƙa motarsa cikin nutsuwa, kuma da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana kan bakinsa. Ivana ta kalli hanya tana murmushi.
“Duk inda kake ganin zai yi kyau da zama a lokaci irin wannan”
Ya sake dubanta, sannan ya ɗauke kai yana dariya, bluewaters island shi ne wurin da ya fara zuwa ransa. Dan haka ya nufi wurin, a gefe ya samu wuri ya faka motarsa, sannan suka fito daga motar, yana riƙe da bag ɗin guitar ɗinta. Yayin da suka jera suna tafiya a cikin yammacin.
Daddaɗar iskar da ruwan wurin ke badawa tana busawa a ko ina, akwai kaikawon mutane a wurin, kowa yana harkar da ta kawo shi. Da haka suka samu wani bench suka zauna. Kafin Uwais yace bari ya siyo musu abin sha, tana zaune a wurin har ya siyo ya dawo, ya bata drink ɗin, ta masa godiya tana kallonsa yayin da yake zama, a lokaci guda ta saƙala gashinta a bayan kunnenta, sakamakon iskar wurin dake kaɗa gashin nata.
“Ina za ki je?”
Uwais ya tambaya. Sai ta kalle shi tana shan drink ɗin da ya bata, sannan ta jinjina kanta.
“Akwai abokina da zamu taya murnar ƙarin shekara. Dan haka muka shirya tafiya zuwa Germany”
Ta ba shi amsa tana kallon wheel ɗin dake wurin. Uwais ya jinjina kansa.
“Kamar kwana nawa kike ganin za ki yi?”
Ta ɗan juya idonta, sannan ta tura gashinta baya tana faɗin.
“A ƙalla sati ɗaya... Da wani abu ne?”