Sashe 18
Juyin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kyakkyawan dogon gashin idonta na sama ne ya ɗaga zuwa sama, farin idonta dake ɗauke da ƙwaya kalar (brown) ya bayyana, sake rufe idon nata ta yi, sannan ta sake buɗe shi a karo na biyu, ta saka dogayen fararen yatsun hannunta, ta murza idonta, sannan a hankali ta saka hannunta ta yaye mayafin da ta lulluɓa da shi, ta tashi zaune, yayin da gashin kanta me tsayi ya lulluɓe kafaɗunta da kuma gadon bayanta.
Lokacin da ta yi miƙa tare da hamma kuyangu da bayin da suka saba mata hidima a kullum rana suka fara shigowa ɗakin ɗaya bayan ɗaya, kowanne ya shigo ɗakin sai ya miƙa mata gaisuwa, sannan zai fara aikinsa na kullum. Yayin da ita kuma ta nufi bayin dake cikin ɗakin, wasu kuyangu biyu suka rakata zuwa bayin, domin tayata tsaftace jikinta.
Lokacin da suka dawo ɗakin har an gama tsaftace ko mai da ko ina, a kan wata kujera ta zauna, kuyangun da aikinsu shi ne shirya gimbiya suka kewayeta, kowa da aikin da yake, wasu na gyara mata gashi, wasu na aikin gyara mata fata, yayin da wasu na taimakawa wurin saka mata tufafi.
Sai da suka ƙawata sarauniyar da ado irin wanda ya dace da duk wata 'yar sarki me jin isa da iko a wannan zamanin, sannan suka koma gefe, masu aikin kawowa sarauniya shayinta na safe suka matso, aka bata shayin ta sha, sannan ta tashi domin zuwa ɗakin karin kummalo da kowa ya saba halarta domin cin abinci. Sai da ta yi taku uku, sai kuma ta dakata, hakan ya sa su ma bayin da suka shirya domin take mata baya suka dakata. Cikin iko isa da izza ta kalle su da gefen ido.
“Ku bani wuri, akwai abin da zan gabatar cikin sirri”
Ta furta cikin muryarta me sanyi da zaƙin sauraro. Dukan ma'aikatan nata suka risina mata, alamun sun amsa saƙon nata, sannan suka soma barin ɗakin ɗaya bayan ɗaya. Sai da suka fita daga ɗakin gaba ɗayansu, ya rage sai amintacciyar hadimarta kaɗai a ɗakin, ta kalli hadimar da kanta yake a ƙasa.
“EID ya aiko da wani saƙo?”
Hadimar ta jinjina kanta dake ƙasa.
“Ƙwarai gimbiyar kyawawa...”
Daga haka ta nufi tagar ɗakin dake a bangon gabas, ta saka hannayenta ta buɗe ƙofar, hakan ya bawa mujiyar (owl) dake waje damar shigowa ciki, ta shiga kaɗa fuka-fukanta har ta isa kafaɗar gimbiya. Wani kyakkyawan murmushi ta yi tana kallon mujiyar, sannan ta saka hannunta ta ciro takardar dake riƙe a cikin ƙafafun mujiyar. Ta buɗe takardar ta soma karanta wasiƙar soyayyar da masoyinta SA'EID ya aiko kamar kullum.
Kan wata kujera ta koma ta zauna tana murmushi kamar wadda ta samu taɓin hankali, haka kalaman soyayyarsa ke ratsa mata zuciya, sai da ta gama karanta wasiƙar, sannan ta ɗauki wata takardar da alƙalami, ta rubuta nata kalaman, sannan ta saka a cikin ƙafar mujiyar, ta buɗe mata ƙofa ta turata zuwa waje ta tagar tana murmushi.
“Ina da wata magana idan har ba za ta ɓata miki rai ba ya shugabata!”
Gimbiya Iqra ta dubeta hadimarta Champa, murmushin dake kan fuskarta na samun kalaman masoyinta SA'EID ALI bai gushe ba ta furta.
“Ina jinki Champa”
“Ɗazu jakadan fada yake sanar da ni wani batu da nake da tabbacin ba ki san da shi ba...”
Murmushin fuskarta na shirin ɓacewa ta furta.
“Wani batu ne wannan?”
“A yau yarima Wajid ɗan sarkin Mamlakatul Azad zai zo tare da mahaifinsa a kan batun naiman aurenki?...”
Ɓat murmushin kan fuskarta ya ɓace a iska, wani abu me kama da ƙwai ya faɗo ya fashe a ƙirjinta. Sannan ta saki baki da hanci tana kallon Champa. Duk bayan tsawon lokacin da suka shafe suna soyayya da Eid masoyinta a rasa a gaɓar da za'a rabasu sai yanzu da soyayyarsu ta ɗauko daɗi?... Zuwan wani da ban fadar a kan maganar aurenta ba Eid ba na nufin za'a aura mata waninsa.
Kuma sam ita ba za ta lamunci hakan ba, ko da za ta gudu daga fadar ne za ta yi, domin tseratar da soyayyarta. Ta san ko da ta gabatar da Eid a gaban Malik Cangaz a matsayin mijin da take so ya aura mata ba zai amince ba, domin Eid ba shi da mulki, sannan ba shi da kuɗi ko wata dukiya da za ta siya masa mutunci a idon mahaifinta ballantana ta kai ga ya aura mata shi.
Salma Ahmad Isah ✍️
A zo a fara biyan kuɗin book, saboda book one ya ɗauko hanyar ƙarewa. If you wanna be part of the journey, pay ₦400 for nomarl group, and ₦800 for VIP group.
5487270431
Salma Isah
Monie point
Sai a tura shaidar biya ta 08130172702.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
. 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄
©️Salma Ahmad Isah
SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah @Wattpad
Page-10
ARMAN.
A rana ta gaba ma haka suka ci gaba da tafiya a cikin dajin, kasancewar suna duba taswirar da tsoho ya basu yasa ba su ɓata hanya ba ko sau ɗaya. Har rana ta biyu a tafiyar tasu ta ƙare babu wata matsala da ta samesu, ko wani baƙon abu da ya ziyarce su, sai a rana ta uku, ranar da suke hasashen iske ƙauyen Askar wani baƙon lamari ya riskesu a hanya.
Tun cikin daren ranar ake iska me ƙarfi, wadda take tafe da ƙura da kuma sanyi me shiga jiki, kuma tun a safiyar ranar iska ta ɗauke tentunan da suka kafa, lokacin da suka tafi naiman ruwan wanke jikunansu, sanda suka dawo suka iske babu tentin iska ta ɗauke.
Sa'arsu ɗaya, jakukkunansu ba su cikin tent ɗin lokacin da iska ta yi gaba da su, cike da salallamin rashin tent ɗin suka haɗa kayansu suka ci gaba da tafiya, dan yanzu abin ma ya fara zame musu jiki, har sun fara sabawa da yanayin tafiyar.
Suna tsaka da tafiya a tsakanin wasu bishiyoyi suka fara jin kuwwar wasu mutane, Adam ne ya fara jiyo kuwwar, hakan yasa ya ankarar da sauran, sai suka tsaya suna duba kewayen da suke, wai ko za su ga ta inda masu kuwwar za su ɓullo. Amma har bayan shuɗewar daƙiƙu biyu babu alamar komai. Sai da suka sakankance sannan suka ji faɗowar abu daga sama tim!.
Hakan ya sa suka ƙara razana, Arman ya turasu bayansa domin basu kariya, yayin da yake kallon ta inda abin ya faɗo, girman idonsa ya rage yana kallon mutumin dake tsaye a gabansu, alamun dai shi ne ya faɗo daga saman. Tun daga kan kwarjallen dake ƙugunsa zuwa rigar dake sanye a jikinsa duka na fata ne, kuma fuskarsa a rufe take, shi yasa ba su iya banbance kamarsa.
Kafin su yi wani yunƙuri wasu mutum uku dake sanye da kaya irin nasa suka sake dirowa daga saman bishiya, Arman ya sake kare Ivana da Adam da suke a matuƙar tsorace, shi ma kansa a tsorace yake, amma dole ya ɓoye tsoronsa domin kare abokansa.
Kallon-kallo aka tsaya yi, su suna karantar kama da kuma nau'in tufafin dake jikin mutanen huɗu, yayin da su ma suke kallonsu, dan za su iya cewa tun da suke fashi a hanyar, tsawon shekaru tara, ba su taɓa ganin mutane masu kama da waɗannan ba, bawai dan sun banbanta da mutane ba ne, a'a su ma kamar mutane suke, amma kalar tufafin jikinsu shi ne abin mamaki... Sai dai mamakin son sanin su wasu nau'in mutane ne ba shi zai hana su ƙwace duk wani abu da suke tafe da shi ba, dan haka wanda ya kasance shugansu ya miƙa musu hannunsa, cikin larabcinsa me kyau yace.
“Ku bamu kayanku!”
“Kaya?”
Adam ya maimata.
“Ku bamu kaya ko kuɗi, idan ba haka ba ku yi ta ranku!”
Dariya ta so kama Adam, dan shi ne ya fara fahimtar wasu irin mutane ne. Camera ɗinsa ya fitar ya shiga ɗaukansu a hoto. Yayin da su kuma suka shiga kare fuskokinsu saboda hasken flasher da Adam ke haskasu da ita.
“Adam me suke buƙata ne?”
Ivana ta tambaya tana kallonsa lokacin da ya gama ɗaukansu a hoto yana dariya.
“Wai 'yan fashi ne”
Ita kanta sai da abin ya so bata dariya. Ganin suna dariya ya harzuƙa 'yan fashin, ai rainin hankali ne ma, ya za'ayi su tambayesu kudi ko kayan kuɗi su zauna suna musu dariya. Hakan yasa suka fitar da makamansu masu firgita bil adama, suka yi kansu da shi. Amma Arman bai bari sun kai ga cutar da su ba, dan cikin azama shi ma ya fitar da nasa takobin ya nunasu da shi.
“Kada ku sake ko da taku ɗaya zuwa garemu, duk wanda ya sake kuma zan raba kansa da gangar jikinsa”
Ya faɗi a dake yana dubansu, juna suka kalla, dan ba sosai suka gane abin da yace ba. Ɗaya daga cikinsu ya sake yin wani takun zuwa gaba. Cikin ƙwarewa da iya sarrafa takobi, Arman ya juya takobin a hannunsa, sannan shi ma ya nufe shi, yana zuwa dab da shi ya kare farmakin da ɗan fashin ya kawo masa, sannan ya jujjuya takobin da hannunsa ɗaya, ya kai masa suka a gefen ciki, shi kansa bai ɗauka cewa zai iya samun wurin da ya hara ba. Domin bai taɓa amfani da takobin gaskiya ba, amma sai ga shi ya samu gefen cikin ɗan fashin.
Ya ƙwalla ƙara yana naiman ɗauki a wurin 'yan uwansa, su kuma kallon Arman kawai suka tsaya yi baki sake, dan a fashin da suka kwashi tsawon shekaru sun yi ba su taɓa haɗuwa da wanda ya mayar musu da martani ba sai yau. Arman ya zare takobin da ya sokawa ɗan fashin, sannan ya tura shi wurin 'yan uwansa. Da sauri suka ɗauki ɗan uwansu suka ruga cikin dajin da gudu.
“Hooooo! Abokina wai da ma haka ka iya sarrafa takobi!?”
Cewar Adam baki buɗe, dan bai taɓa ganin Arman ɗin na wasan takobi ba sai yau. Ita kuma Ivana takan je ta ga wasan nasa idan suna yi a Fencing Academy ɗinsu, amma duk da haka abin ya bata mamaki. Shi kansa Arman mamakin abin yake ji, takobin dake ɗigar jini ya ɗaga yana kallo, kafin ya mayar da shi cikin gidansa.
“Ya kamata mu yi saurin barin wurin nan, kafin wasu mugayen mutanen su zo”