← Book details Juyin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 25

Sashe 12

Juyin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“To yanzu da kika iyo kaina dukana za ki yi? Na ce dukana za ki yi?”

Nan fa cecekuce ya kaure a tsakanin dangin Abby da na Immi.

“Ya isheku haka!”

Faɗin Immi cikin ƙaraji. Hakan ya sa wurin ya yi tsit.

“Ku barmu mu ji da ɓatan ɗanmu mana. Bayan wannan abin da ya faru da mu kuma me yasa kuke son ƙara mana wata damuwa?”

Ta ƙarashe tana kwantar da kanta a kafaɗar mijinta da ta jingina da shi, sannan ta fashe da wani sabon kukan.

“Ko kana ina yanzu haka ɗana?”

°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°

A hankali Arman ya leƙa windown dake a ta gefensa, ya kalli gajimare dake ƙasan jirginsu da ya tashi sama, kafin ya juyo ya kalli Ivana da Adam dake kusa da shi, dan tikitin kujeru ukun dake kusa da juna suka siye, kasancewar jirgin da suka hau babba ne.

Ita Ivana kallo take a system, yayin da Adam ke cin abinci hankali kwance, amma shi sam ji yake hankalinsa ya ƙi kwanciya, da ko wani ƙarin daƙiƙa da jirginsu ke nufar birnin Regen dake ƙasar Germany, wanda ya kasanci gari mafi kusa da Bavarian forest ji yake kamar yana ƙaura daga duniyarsa zuwa wata duniyar da bai sani ba.

Idonsa ne ya kai kan agogon dake tsintsinyar hannunsa, a hankali ya furzar da iska daga bakinsa, sannan ya gyara glasses ɗinsa tare da tura sumar dake kan goshinsa baya. Ya lusmhe makafin idonsa yana jin wani abu na rashin daɗi na masa yawo a zuciya.

“Arman? Shu fi (Me ya faru)”

Adam da ya lura da shi ya tambaya. Amma sai ya buɗe idonsa yana girgiza kai. Sannan ya ɗauke kansa ya jingina da kujera yana kallon window, kasancewar shi ne a window seat. Adam ya kira ɗaya daga cikin flight attendant. Jim kaɗan ta iso seat ɗinsu tana murmushi, kamar yanda aka saba ganinsu, cike da girmamawa ta risina tana faɗin.

“Me kake buƙata yallaɓai?”

“Ruwa me sanyi”

Adam ya amsa.

“An gama yallaɓai”

“Sannan ki tafi da wannan, na kammala”

Ta sake amsawa, sannan ta ɗauke trayn da ya gama cin abinci da shi, ta juya ta tafi, sai da ta kawo ruwan, sannan ya bawa Arman.

“Ka sha”

Arman ya kalli ruwan, sannan ya kalle shi, ya sa hannu ya karɓa, ya sha sosai, sannan ya aje yana sake ɗauke kai ba tare da yace komai ba. Hankalinsa gaba ɗaya yana kan agogon hannunsa, dan jira kawai yake 12 ta cika. Kuma a dai-dai lokacin da ta cika, ya lusmhe idonsa, a hankali ya furta.

“Eid Milad sa'id ya Arman (Happy birthday Arman)!”.

Salma Ahmad Isah ✍️

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

. 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄

©️Salma Ahmad Isah

SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah @Wattpad

Page-7

*Furstlich zeil Hotel, Lower Town, 168, Regen, Germany.*

*11:04 na rana.*

IVANA POV.

A karo na uku ta sake ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Arman, sannan ta janye hannunta tana jiran ya buɗe. Jiya bayan jirginsu ya sauƙa a birnin Regen kamfanin da Arman ya ɗauka musu domin su kaisu duk wasu wuraren buɗe ido ne suka aiko wakilinsu ya ɗaukesu a airport. Kuma shi ne ya kawosu wannan hotel ɗin, inda suka kama musu ɗakuna uku, kowa da ɗakinsa.

Tun a daren jiya ita da Adam suka tsara cewa za su je siyayya, dan haka ne ma yanzu suka shirya domin fita, kuma wakilin kamfanin da kan zaga da masu yawon buɗe idon na tare da su, dan shi ne wanda zai zaga da su a cikin gari, kafin zuwa gobe kuma su nufi Bavarian forest, inda kaddararsu ke jiransu a cikinsa.

Kallon Arman ta yi, wanda ya buɗe ƙofar a kasalance, sanye yake da sweate shirt eggplant color, da farin chinos trouser, idonsa saye cikin glasses ɗinsa, wanda rims ɗinsa ya kasance white color. Babu ko takalmi a ƙafarsa, hatta da gashin kansa a hargitse yake, alamar bai ga gyara ba. Shi ma kallonsu ya tsaya yi su duka ukun, sannan ya bar ƙofar ɗakin a buɗe, ya juya cikin ɗakin.

Ivana da Adam suka shiga ɗakin, yayin da ɗan rakiyarsu me suna Hans ya tsaya a waje. Ivana da Adam kallonsa kawai suke, har ya zauna kan sofa yana ɗauke kai, ba tare da ya bari sun haɗa ido ba. Ivana da Adam suka dubi juna, dan sun gane cewa kamar abokinsu na cikin damuwa.

“Za mu je siyayya ne, idan kana da ra'ayin zuwa”

Cewar Adam. Kansa ya girgiza yana shafa sumar kansa, tare da ƙifta idonsa a hankali, kuma bai bari ya kallesu ba.

“Arman”

Ivana ta kira tana zauna a gefensa. Dubanta kawai ya yi yana aje wayarsa dake riƙe a hannunsa, dan ba amfanin komai yake da ita ba, hasalima a kashe take, domin ba ya so wani na gida ya kirashi.

“Kamar akwai abin da yake damunka?”

Ta tambaya tana son su haɗa ido, amma ya ƙi bata damar hakan. Tun jiya da suka baro Dubai har zuwa yau ɗin nan ba ya jin daɗi sam, duk tsayin awa shidan da suka kwashe a jirgi kafin su iso Regen sam bai ji daɗinsu ba, hatta yanzu haka da yake zaune ba ya jin daɗi. Kuma jinyar ba a jikinsa take ba, a zuciyarsa take.

“Ka ga Arman! Idan har kana jin hukuncin da ka yanke bai maka ba muna tare da kai. Idan kana jin cewa ka yi nadamar abin da ka aikata za mu kasance tare da kai, wannan rayuwarka ce, kuma lokacinka ne, ka yi abin da ya dace a lokacin da ya dace, ka yi tunani me zurfi a kan wannan hukuncin, duk abin da ka yanke za mu amince da shi. Ko da kuwa kana so mu koma Dubai a ranar yau ne za mu koma, mu dai burinmu shi ne ka yi farin ciki!”

Cewar Adam yana dafa shi, ya ɗaga kai ya kalli Adam, sannan ya kalli Ivana dake jinjina masa kai, alamun abin da Adam ya faɗa haka ne. Ya sauƙe ajiyar zuciya me nauyi, sannan ya shafa kansa yana rinte ido.

“Mu za mu tafi siyayya. Ka tabbatar ka yanke hukunci kafin mu dawo”

Cewar Ivana tana miƙewa, tare da ɗaukan bag ɗinta, ta bubbuga kafaɗarsa sau biyu, sannan tace da Adam su tafi, suka tafi suka bar shi cikin tunani me zurfi.

Ivana da Adam sun zaga sosai a cikin garin Regen, kuma tun a cikin garin ma Adam ya samu ya ɗauki wasu hotuna. Sun shiga manyan kantuna da gidajen abinci, domin sun ɗauki alƙawarin shiryawa abokinsu babban bikin ƙarin shekara. Ta hanyar siya masa kyautuka da dama.

Yayin da suke siyayya a cikin wani shagon da ake saida kayan tarihi irin na da can. Adam ya yi arba da wata sarƙa a cikin wani kit, zaren sarƙar baƙi ne, pendant ɗinta kuma wani abu ne me kama da key, kuma daga ganinsa an ƙera shi ne da gold. Tsabar muhimmanci da darajar sarƙar a keɓe take a cikin shagon, an sanyata cikin wani glass me ɗaukar ido.

“Wannan ta kai kimanin nawa?”

Ya tambaya yana ɗaukan glass ɗin da aka sakata a ciki, me kantin ya yanko maƙudan kuɗaɗe ya faɗa, duk da sarƙar ta yi tsada hakan bai sa Adam ya fasa siyawa Arman ita ba, domin ko da zai ƙarar da kuɗin da yake da shi zai yi domin faranta ran Arman. Ita kuma Ivana sabon takobin fencing ta sai masa, da wasu ƙanun kyautuka da ta san za su burgeshi.

*Dubai...*

“Ina zuwa!”

Faɗin Maama dake wanke hannu a sink, yayin da take kallon ƙofar gidan da ake ƙwanƙwasawa. Hannunta ta goge, sannan ta nufi ƙofar ta buɗe, mamaki ya kamata, ganin Sayyid Iƙbal Alhadi da matarsa Zahra, da kuma 'yarsu Gulzar.

“Barkanku da zuwa... Ku shigo ciki mana”

Ta faɗa tana murmushi, tare da buɗe ƙofar gaba ɗaya, Abby ya ɗan yi murmushin yaƙe yana mata sallama, ta amsa yayin da yake shiga falon, ita kam Immi babu wata alamar walwala tare da ita, ta yi sallamar kamar da aka mata dole, sannan ta shiga falon ita ma, Gulzar kuwa bayan ta yi sallamar sai da ta gaida Maama sannan ta shiga. Su duka ukun a falo suka zauna, yayin da Maama ta koma flat kitchen ɗinta ta ɗauko abin sha, ta aje musu a center table suna sake gaisawa.

“Shin Adam yana nan?”

Abby ya tambaya, mamaki ya sa Maama ta kallesu, kafin cikin kokwanto tace.

“Adam? Ai jiya suka tafi Regen, Germany, kuma yace min tare da Arman za su tafi, ko dai Arman ɗin bai samu zuwa ba?”

Abby ya dafe kansa. Yayin da hawaye ya zubowa Immi.

“Arman guduwa ya yi ya bar gida ba tare da saninmu ba, yanzu haka ba dan kin faɗa ba da ba mu san inda yake ba”

Maama ta yi shiru, ta san irin haka sam ba daɗi. Da ace ita ce a matsayinsu da yanzu ita ma nata hankalin a tashe yake.

“Sayyid Iƙbal ka yi haƙuri, haƙiƙa abu irin wannan babu daɗi, amma su yaran yanzu idan har suka yanke hukunci babu wanda ya isa ya tablnƙwarasu, dan za su iya aikata abin da suke so a ɓoye ba tare da sun sanar da kai ba, ku yi haƙuri ku ci gaba da masa addu'a”

Abby ya dubi Maama, sannan ya yi murmushi kawai. Dan shi tun da har ya san inda yake matsala ta kau, Arman ba ƙaramin yaro ba ne da zai ɓata, ya sha yin tafiye-tafiye irin wannan, kuma shi kaɗai, dan haka yanzu hankalinsa ya kwanta, domin ko ba komai idan ya gama kwanakin nasa a Regen dole zai dawo gida!...

“Allah ya kareka shugaba!”

Shi ne kawai abin da ya furta. Dan ba ya jin yana da wani abin cewar bayan wannan.

*Regen, Germany.*

Adam ya ja tsaki a karo na barkatai, yayin da suke duban ƙofar hotel ɗin da suka kwana ciki, tsaye suke shi da Ivana da kuma Arman, a jikin motar da suka yo hayarta yau, domin yau ne za su shiga Bavarian forest. Ga shi rana ta kusa faɗuwa, amma har yanzu Hans bai zo ba.
Chapter 12 · 0% Book details