← Book details Juyin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 25

Sashe 7

Juyin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dube shi, dan ta san Al Aida babban kamfani ne, da suke sarrafa abubuwa da dama. Shiru ya ratsa wurin na wasu mintuna, kafin ya miƙe tsaye yana faɗin.

“Ni zan tafi”

Ita ma sai ta miƙe tana kallonsa.

“Sai mun sake haɗuwa”

Ya miƙa mata hannunsa alamun su gaisa, tare da faɗin.

“Sunana Uwais Faizal”

Ta kalli hannun nasa, sannan ta miƙa nata hannun suka gaisa.

“Ivana Sagar”

A lokacin da ya jinjina hannunsa tare wani abu kamar wucewar iska ya gifta a cikin kanta. Haka kawai take jin kamar ta taɓa haɗuwa da wani kamar haka a can baya, kamar akwai wani me kammani irin nasa da suka taɓa gaisawa irin haka, amma ba'a Dubai Miracle Garden ba, a wani unknown wuri da ba ta isa tace ga shi ba.

“Na ji daɗin haɗuwa da ke Ivana”

Faɗin Uwais yana murmushi, ita ma sai ta jinjina kanta.

“Ni ma haka”

*Salma Ahmad Isah ✍️*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

. 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄

©️Salma Ahmad Isah

SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah @Wattpad

Page-4

*House No. 106, Street 14, Jumeirah Bay Island, Abu Dabhi, Dubai.*

“Ban san da wani yare zan yi wa Arman magana da shi domin ya gane abin da nake nufi ba... A ko da yaushe ɗana na nisantata saboda wannan dalilin guda ɗaya!”

Faɗin Abby, yayin da suke hira da Immi a cikin katafaren ɗakinsa, da aka ƙawata da kayan adon ɗaki na zamani, kuma masu kuɗin gaske. Immi ta aje cup ɗin shayin dake hannunta, sannan ta shiga wasa da yatsunta tana faɗin.

“Tun tasowarsa yayanka da wasu daga cikin 'yan uwanka ke nuna masa cewa kasancewarsa makaho ba shi da wani fata a rayuwa. Buri da mafarkin cimma shi na masu lafiya ne, shi da ya kasance nakasasshe ba shi da ikon son cimma wani buri nasa a rayuwa. Tun ɗana yana ƙarami aka nakasta min zuciyarsa, domin kalaman tozarci da na aibantawa su ne suka sa ya tsani duk wata harkar kamfani ko kasuwanci”

Abby ya kai hannu aje nasa cup ɗin da yake riƙe da shi, sannan ya lumshe idonsa yana shafa kyakkyawar sumar kansa.

“Abin da kika faɗa haka ne Zahra, amma a halin yanzu ba ni da ikon canzawa Arman ra'ayi, batun nakasa kuma ke kanki shaida ce, da ace ina da hali, da na bayar duk abin da na mallaka, domin sama masa lafiya...”

Ya buɗe idonsa yana jin zuciyarsa na masa zafi.

“Ina da wata shawara”

Abby ya kalli Immi da ta yi wannan batu.

“Shida ga watan nan da muke ciki ranar haihuwarsa za ta zagayo. Dan haka me zai hana mu haɗa shagalin taya shi murnar zagayowar ranar da aka haife shi. Ko da ba babban party ba, ɗan ƙarami, wanda za mu gayyaci ahali da abokai, yayin da ake cikin shagalin bikin, za ka gabatar masa da takardun kamfani, a gaban kowa, ka umarce shi da ya sa hannu, na tabbatar ba zai ƙi ba, kuma ka ga mu ma sai mu huta, dan daga zarar ya sa hannu magana ta ƙare, babu shi babu sake cewa ba ya son shugabanci!...”

Abby ya yi shiru na wani lokaci yana shafa sajensa.

“Arman yana da taurin kai, zai iya ƙin amincewa”

Immi ta girgiza kai.

“Duk taurin kansa ba zai so ya bamu kunya a idon duniya ba”

Abby ya yi murmushi.

“Na gode da wannan shawarar taki Azizati”

Ya ƙarashe yana kamo hannunta na dama, tare da sumbatarsa. Immi ta yi murmushi tana kallon mijinta.

“Bari na je na duba yaran nan, wata ƙila sun yi bacci”

Ta miƙe tana tura gashin kanta baya.

“Sai kin dawo”

Cewar Abby yana ɗaukan cup ɗin teans. Immi na fita ta fara da ɗakin Gulzar, kuma kamar yanda ta yi zato ne, sanda ta isa ɗakin nata samunta ta yi tana bacci. Dan haka ta shiga ɗakin cikin kulawa, ba tare da ta bari ta yi making sound ɗin da zai sa ta farka ba. Sunkuyawa ta yi ta sumbaci kanta, sannan ta juya ta bar ɗakin. Daga nan kuma ɗakin Arman ta wuce, shi kam bai yi bacci ba, dan zaune ta same shi a kan gadonsa yana kallo a system.

Tana shiga ɗakin ya tsayar da kallon, sannan ya rufe system ɗin yana binta da kallo, har ta zauna a kan gadon nasa.

“Tu abhi tak kyun nahin soya?” (Me yasa ba ka yi bacci ba har yanzu?)

Ta tambaya cikin harshen Urdu tana kallon kayan dake jikinsa, dan yana sanye da khaki trouser da shirt ne, sumar kansa duka ta sauƙo kan goshinsa, sannan glasses ɗin da suke tamkar rayuwarsa na maƙale a fuskarsa. Sai ya kwanta a kan gadon, sannan ya ɗora kansa a kan cinyarta.

“Main neend mehsoos nahi kar raha, isi liye Immi”

(Bana jin baccin ne, shi yasa Immi)

Shi ma ya amsa mata da Urdu ɗin. Ta shafa sumar kansa da take a nannaɗe, saboda style ɗin curl ɗin da aka mata, dan babu wani aski da yakewa sumar tasa bayan top curly, kuma iyaka tsakiyar kan ne yake tara gashi, gefe da gefen da kuma ta baya aske shi ake.

“Laish manak na'asan?”

(Me yasa ba ka jin bacci?)

Wannan karon da larabci ta tambaye shi. Dan duka yaren biyu babu wanda ba sa ji shi da Gulzar, kasancewar Urdu shi ne yaran ƙasarta Pakistan, duk da yana kamanceceniya da Hindi. Amma asalin yarenta Urdu ne, larabci kuma shi ne yaren mahaifinsu, hakan yasa duka yarikan biyu sun iyasu.

“Bas haik Immi”

(Haka kawai Immi)

Ya bata amsa da larabcin shi ma.

“Arman!”

Ta kira sunansa tare da sumbatar sumar kansa, sai ya lumshe idonsa yana amsawa.

“Umm”

“Me yasa ba ka son faranta mana ta hanyar yin abin da muke so ni da Abby?”

Tambayar tata tasa ya buɗe idonsa.

“Immi ba zan iya yin shugabanci ba. Saboda ina da nakasa...”

“Shiiiiii!”

Immi ta yi saurin dakatar da shi, sannan ta sa hannu ta tura sumar kanta bata.

“Na san cewa kana da halayen da kai kanka ba lalle ace ka san kana da su ba... A ƙalla ma'aikata ashirin ne ke aiki a gidan nan. Amma cikin mutum ashirin ɗin nan ba na jin akwai guda ɗaya da ka taɓa tozartawa, kuma ban taɓa gani ko jin sanda ka saka wani cikinsu aikin da ba za su iya ba. A wasu lokutan ma kana yin ayyukan da ya kamata ace su ne suke yi, kuma kana ɗaukansu a matsayin abokai. Duk da a ƙasanka suke aiki, ko ni da Gulzar sukan koka damu a wasu lokutan, amma ban da kai Arman. Hakan yasa na gane cewa ɗana shugaba ne, shugaba ne da zai iya jan ragamar masarauta ba iyaka Majmu'at Shirkat Alhadi kaɗai ba. (Alhadi Group of Companies)...”

Kamar yanda ya saba shiru a kan maganar da ba shi da amsarta haka yau ma ya yi shiru, dan ba ya jin zai iya ce mata wani abin kuma...

*House No 27, Street 45, Mirdif, Dubai*

IVANA POV.

Zaune take a kan kujerar falo, ta lanƙwashe ƙafarta ɗaya a kan kujerar da take zaune, ɗayar ƙafar tata kuma na ƙasa, sanye take da casual palazzo trouser, me ɗauke da zanen dogayen layin baƙi da kore, sai baƙar tube top. Gashin kanta na cikin style ɗin halp up- halp down. Idonta a kan Tv, tana kallon wani show da ake haskawa a Wanash tv. Yayarta Hala mahaifiyar Imran na zaune a gefenta suna kallon shirin tare.

“Ivana waye saurayin da Imran yace min kuna tare da shi a Miracle garden?.”

Ta ji tambayar a bazata, dan sam ba ta yi zaton tambayar ba, kanta ta juyo ta kalli Hala, sannan ta ɗage kafaɗunta tana barbaza gashin kanta dake kwance a gadon bayanta.

“Uwais Fazil! Haka yace min sunansa”

Hala ta gwalalo ido tana kallonta.

“Kada ki ce min jinin masu kamfanin Al Aida ne?”

Ivana ta tattare naman goshinta cikin mamakin saiyawar yanayin Hala lokaci guda.

“Eh shi ne. Mi ye wani abu na musamman a kasancewarsa jinin ahalin?”

Ta tambaya. Hala ta yi dariya.

“To idan ba ki sani ba na sanar da ke. Kin ga girman kamfanin baban abokinki Arman? To da kaɗan zai faɗawa Al Aida girma. Kuma idan har kamfanin Iƙbal Alhadi zai zama na farko cikin jerin manya-manyan kamfanunuwa a Dubai to Al Aida zai zamo na biyu!”

“Waye bai san wannan ba to?... Ni ban ga wani abin birgewa a nan ba!”

Ba ta kai ga rufe bakinta ba wayarta ta shiga ruri. Da ta duba kuma sai ta ga lambace babu suna, ta ɗauka da niyyar ba za ta ɗaga ba.

“Ya kamata ki ɗaga, dan ba ki san wani alkairi ne yake shirin faruwa da ke sanadiyyar kiran ba”

Cewar Hala, kuma a lokacin Yumma da ta tafi sama wankewa Imran rigarsa da ya ɓata suka sauƙo ƙasa tare da Imran ɗin. Dan haka Ivana ta ɗauki wayar ta yi sama, har Yumma da Ivanan ta raɓa ta wuce na binta da kallo, saboda saurin da take. Tana shiga ɗakinta ta rufe ƙofar, sannan ta kalli screen ɗin wayar, lokacin da kiran yake shigowa a karo na biyu. Sai da ta tsaya nazari na wasu sakanni, kafin ta ɗaga kiran.

“Marhaba (Hello)”

Ta faɗa tana lasar lips ɗinta, a lokaci guda kuma ta ɗora hannunta a kan ƙugunta.

“Ahalain (Hii)”

Tun da ta ji muryar ta gane waye. Amma abin mamakin shi ne, a ina ya samu lambarta?. Wa ya ba shi? Me yasa ya kirata.

“Uwais Fazil ke magana”

Ya sake faɗa daga ɗayan ɓangaren, jin ta yi shiru, Ivana ta zauna a bakin gadonta tana faɗin.

“Na gane ai”

“Good to ya kike?”

“Ina lafiya, da fatan kai ma haka”

“Ni ma ina cikin ƙoshin lafiya da amincin rai da zuciya!”

Amsar da ya bata ta sa ta yi murmushi.

“Na kiraki ne mu gaisa... Saboda tun bayan waccan ranar da muka rabu nake ta tunani da burin sake haɗuwa dake”

“Wani abu ne na musamman haka da ya faru a haɗuwarmu ta farko da har zai sa ka yi marmarin sake haɗuwa da ni?”

Ta tambaya.
Chapter 7 · 0% Book details