← Book details Juyin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 25

Sashe 4

Juyin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farar matashiyar da za ka iya kira da balarabiya sanye take da baƙin wide black jeans, da farar blouse top, ƙafafunta cikin fluffy sliders farare, dogon gashin kanta kuwa sai reto yake a bayanta. Ita sam ba ta kama da indiyawa, saɓanin Armaan da kammaninsa suka sirka da na Immi, ita Gulzar sak Abby ce, wayarta ce riƙe a hannunta tana latsawa, da alama ma ba ta lura da shi ba.

Arman ya yi murmushi yana gyara zaman glasses ɗinsa, sannan ya fara taku a hankali yana nufarta, sai da ya je dab da ita sannan yace.

“Me dogon gashi!”

Ya faɗa da ƙarfin da ya razana Gulzar, har wayarta na suɓucewa a hannunta, ta kalli wayarta da ta faɗi ƙasa sannan ta dube shi tana haɗe girar sama da ta ƙasa, ta kai masa duka a ciki tana faɗin.

“Duk ka bi ka tsorata ni!”

Arman ya dafe wurin da ta daka a cikinsa yana dariya, sannan ya sunkuya ya ɗauko mata wayarta, ya miƙa mata, ta warce wayar tana harararsa.

“Idan ka sake min irin wannan sai na faɗawa Immi ta min maganinka”

Ta faɗa tana nuna masa ɗan yatsa, Armaan na dariya ya dafata tare da juyata suka nufi ɗakinsa.

“Ina am imzah! Bas, mu aksar (Wasa fa kawai nake miki ba komai ba)”

Gul ta mintsini cikinsa tana faɗin.

“Kada ka sake min irin wannan wasan”

Armaan ya saketa yana dafe inda ta mintsi ne shi.

“Yarinyar nan kin iya mugunta”

Gul ta matsa daga jikinsa, dan ta san halinsa, yanzu zai ce zai riƙe mata gashinta da ta fi so, dan ko sau ɗaya ba ta jin ta taɓa rage tsayinsa.

“La wain rayiha? (Ina kuma za ki je?)”

Ya tambaya yana kallonta, ta ruga da gudu, shi ma ya bi bayanta zuwa ɗakinsa. Gul na shiga ɗakinsa ta faɗa kan gadonsa tana dariya. Shi kuma yana shigowa ɗakin ya yi tsaye yana kallonta a kan gadonsa. Kansa kawai ya girgiza, ya nufi wurin da ya saba aje awards ɗin da yake samu a wasan fencing da yake yi.

Ɗakin nasa na da girma, komai na ɗakin brown da fari ne, gadonsa na daga bangon yamma na ɗakin, yayin da balconyn dake cikin ɗakin yake ta bangon gabas, ta yanda daga hasken rana ya fito zai sauƙa kan gadon, dan slide glass door ce a wurin.

Akwai dressing mirror da 'yan wasu tarkacensa a ɗakin, yayin da closet ɗinsa ke cikin banɗaki. Babu tarkace da yawa a ɗakin, amma komai ka ga a ɗakin sunan kuɗinsa yake furtawa, dan kallo ɗaya za ka masa ka fara ƙissima tsadarsa. Daga kusa da chest drawern da ya saba jera awards ɗinsa kuwa, hotunansa, da wanda suka ɗauka shi da su Gulzar da Immi, da nasa shi da su Ivana ne manne a ko ina.

“Ni fa kallon mara aikin yi nake maka aki! Ni ban ga dalilin da zai sa ina koyon wasan takobi ba. Bayan ni ba a 18th century nake rayuwa ba. Yanzu kai ya waye, babu wanda yake faɗa da takobi, da ma koyon harbi kake da sai na ce dama-dama!”

Ya juya ya kalli Gulzar dake zaune a tsakiyar gadonsa tana danna wayarta. Lokaci guda kuma wannan yaƙin da ya saba yin mafarkinsa ya kutso cikin tunaninsa. Shi kansa ba ya ce ga dalilin da yabsa yake son koyon wasan takobi ba, amma haka kawai iya sarrafa takobi ke burge shi.

“Ba ni na zaɓi fencing ba Gul! Fencing ne ya zaɓeni”

Ya bata amsar yana cilla mata backpack ɗinsa, ta cafe jakar tana kallonsa sanda ya shiga bathroom. Wayarta ta aje a gefe, sanna ta buɗe jakar, ta soma fitar da wasiƙun dake ciki, wanda yawancinsu 'yan matan dake sonsa ne ke turowa.

“Aki waɗannan fa? Ko tsofi ne?”

Ta tambaya da ɗan ƙarfi, dan ta ji ya kunna ruwa, alamun wanka zai yi.

“Satin da ya wuce aka aiko da su!”

Shi ma ya bata amsa daga cikin bayin, Gulzar ta buɗe ɗaya daga ciki, sannan ta fara karantawa a bayya ne.

“Zuwa ga kyakkyawan tauraron wasan fencing da babu kamarsa a MK fencing acadamy. Haƙiƙa ka iya sarrafa takobi cikin ƙwarewa, kana bawa takobi umarni cikin iko da burgewa, ka haɗu sosai Arman!...”

Gulzar ta zaro ido tana rufe bakinta.

“Aki ai wanna 'yar makarantarku ce”

Tana jiyowa dariyarsa a cikin bayin, kafin taji ya bata amsa da.

“Ba ɗaliba ba ce, malama ce!”

Ita ma Gulzar ɗin kwashewa ta yi da dariya, sannan ta aje wadda ke hannunta ta ɗauko wata ta shiga karantawa, har Armaan ya fito daga bathroom ɗin sanye cikin blue polo shirt da baƙin cargo trouser. Ya tsaya a jikin dressing mirror yana busar da sumarsa da ya jiƙa yayin wankan da ya yi.

“Ke dan Allah ki aje wannan wasiƙun da ba ƙarewa suke ba”

Gulzar ta kalle shi ta cikin madubin da yake tsaye a gabansa, sannan ta aje wasiƙun agefe, ta saka hannunta a cikin jakar, ta fito da tikitin Coca-cola Arena da suka siya ɗazu. Ta karanta tikitin, sannan ta kalli Arman tana faɗin.

“Wai yau Chris Brown ya yi live performance kuma ka je amma ba ka faɗa min ba?”

Ta tambaya tana sauƙa daga kan gadonsa, Arman ya aje dryer dake hannunsa, sannan ya juyo ya kalleta.

“To ai abin ne ya zo a ƙurace!”

Gulzar ta iyo kansa da gudu tana faɗin.

“Ai ka iya ɗaukan abokanka zuwa wurin! Ni kuma ka barni a nan”

Shi ma gudun ya saka ya fice daga ɗakin, tana biye da shi har zuwa saman gidan, dake ɗauke da sitting areas, daku ma runfunan shaƙatawa. Masu aikin gidan kuma ma aikin tsaftace wurin, Arman ya zauna a kan kujera yana kallonta.

“Ki yi hakuri mana me gashi”

Gulzar da take a fusace, ta sa hannu ta mayar da gashinta da ya suƙo mata kan fuska zuwa baya tana huci, sannan ta zauna kusa da shi tana ture shi.

“Ni dai ka cuceni”

Ta faɗa tana sake ture shi, hakan ya sa glasses ɗin dake idonsa ya faɗi ƙasa, duhu ya mamaye sashin ganinsa, dan daga zarar ya rabu da glasses ɗin babu abin da yake gani face duhu. Cak ya tsaya yana motsa idonsa da babu abin da yake gani da shi, hannunsa ya miƙa kan inda yake zaune, yana laluben glasses ɗin nasa, dan ko tafin hannunsa ba ya iya gani, ita ma Gulzar ɗin sai a lokacin ta lura da shi.

“Ya Ilahi ana asfe aki” (Wayyo Allahana ka yi haƙuri Yayana)

Ta faɗa tana ɗaukan glasses ɗin nasa da ya faɗi ƙasa, ta goge shi a jikin rigarta, sannan ta saka masa shi. Glasses ɗin na hawa kan fuskarsa ya fara gani, sai ya raintse idonsa, sannan ya buɗe.

“Mein bahut off-sori hoon bhradaar, mein iss ka matlab nahin tha...”

(Ka yi haƙuri Yayana, ba da niyya na maka hakan ba)

Ta faɗi cikin harshen Urdu tana dafa kafaɗunsa, sai ya riƙe hannunta yana girgiza mata kai.

“Ma fi shi, insi halla (Ba komai fa, ki manta kawai)”

Gulzar ta jinjina kanta, sannan ta miƙa hannu ta ɗauki Hummus daga cikin kayan maƙulashen dake kan teburin kusa da su, ta miƙa masa.

“Za ka ci?”

Ya ɗan yi murmushi yana gyara zaman glasses ɗinsa, sannan ya karɓa daga hannunta, ita ma ta ɗauki wani bowl ɗin suka fara ci tare.

“Yau mun haɗu da Faisal a Coca-cola Arena”

Arman ya faɗa yana kallonta, ita ma sai ta kalle shi tana gyara zama.

“Ya faɗa maka wani abin ko?... Kuma me ka masa?”

Ta jero masa tambayoyin, sai ya yi dariya yana shafa sumarsa dake cikin askin curly top, dan har sauƙowa take kan goshinsa.

“Ban masa komai ba, kuma ban ce masa komai ba, Ivana ma da ta yi ƙoƙarin ce masa wani abin hanata na yi”

Gulzar ta harare shi.

“Shi ya sa gaba ɗaya ya bi ya rainaka, ba finka ya yi a haife ba amma kullum gainka yake kamar ƙaninsa. Ni ba za ka burgeni ba sai ka yarda ka karɓi shugabancin Alhadi. Ba ma ni kaɗai ba daga lokacin za ka bawa kowa na ahalin nan mamaki”

Arman ya ɗaga kansa sama yana kallon taurarin dake ko ina a sararin samaniya.

“Shugabancin babban kamfani kamar Alhadi Group of Companies ya fi ƙarfin makaho kamar Arman, bara a gefen hanya ita ce tafi dacewa da shi!”

Gul ta ja tsaki tana aje bowl ɗin hannunta.

“Wannan ra'yin wasu mutane ne da ban, kuma idan har ka ci gaba da faɗin haka kana nufin shugabancin ya fi dacewa da shashashan mutum kamar Faisal?”

Armaan ya kalleta yana ɗage kafaɗunsa.

“Ban sani ba!”

Gulzar ta ɗauke ka tana juya idonta, kuma idon nata bai sauƙa a ko ina ba sai a kan saman gidan su Faisal dake ɗan gaba da nasu. Daga nan inda suke tana iya hango Faisal da ƙanwarsa Sakina zaune a saman nasu gidan, masu aikin gidan zaune a wurinsu suna musu hidima.

“Kalli can”

Arman ya kalli inda take kallo.

“Yanda Sakina take ji da kanta kai kace ita matar sarkin Dubai ce. Ko a makaranta ba ta da ƙawaye sai 'ya'yan masu kuɗi. Kullum jin kanta take kamar wata sarauniya, tana kashe kuɗi ta yi yanda ranta yake so. Shi kuma Faisal, lalataccen ɗan da babu uban da zai yi alfahari da shi, a ƙalla 'yan matansa sun kai sha bakwai, babu hotel ɗin da bai taɓa zuwa ba a Dubhai, har ɗaki yake da shi a Burj Khalifa, yanda yake wadaƙa da kuɗi za ka ɗauka cewa babansa ne a kan kujerar shugabancin Majmu'at Shirkat Alhadi, daga an taɓasu za su ce su ne Faisak (FAISAL AND SAKINA)! Humm! Abin haushi”

Ta ƙarashe tana mayar da gashinta dake kan kafaɗunta zuwa bayanta, Arman ya yi dariya.

“Komai lokaci ne Gul, ki ƙara haƙuri”

Ta masa wani irin kallo, sannan ta ɗauke kai.

“Lokacin ba zai ƙare ba har sai ka karɓi shugabancin Alhadi.”

“Wannan lokacin ba zai taɓa zuwa ba”

Arman ya bata amsa zuciyarsa ɗaya. Da Gulzar ta ga takaicin ɗan uwan nata na neman kasheta sai ta miƙe ta bar shi a wurin.

“Gobe laraba, ka shirya zan rakaka wurin Doctor Ƙuraishi”
Chapter 4 · 0% Book details