← Book details Juyin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 25

Sashe 19

Juyin Kwado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wannan maganar tasa suka ci gaba da tafiya, kuma ba su yada zango ba har sai da suka fara hango gidan da tsoho yace musu shi za su fara gani kafin su kai ga shiga ƙauyen Askar. Duk da haka Arman bai tabbatar ba sai da ya buɗe taswirar da tsoho ya ba su, sannan ya ga waɗannan hasken ukun suna tsaye a kan ƙauyen Askar da aka masa alama, kansa ya ɗaga ya dubi su Adam.

“Wancan shi ne gidan da tsoho yace za mu fara gani kafin mu shiga ƙauyen Askar...”

Suka sake kallon gidan.

“To mu je mana”

Cewar Adam shi ne kan gaba, su ma bayansa suka bi zuwa gidan da aka gidan da ƙasa. Kasancewarsu 'ya'yan musulmai yasa sai da suka gabatar da sallama, kafin su kutsa kai gidan. Su ukun duka suka jeru a tsakar gidan. Suna kallon kallo da matar dake tsakar gidan.

Farar dattijuwa ce, wadda a ƙiyasin shekaru za ta kai hamsin da ɗori, sanye take da wasu tufafin da aka saƙa da zaren audiga, wanda aka rina shi zuwa kalar shuɗi. Ƙafafunta na cikin takalman fata irin na zamaninsu, hannunta riƙe da wata ƙwarya. Kamar yanda su ma suke kallonta, haka ita ma take kallonsu. Dan sam ba su mata kama da mutanen da ta sani ba.

“Barka! Mu baƙi ne a nan, akwai wani tsoho da ya ba mu wannan yace mu baki”

Cewar Arman yana nuna mata taswirar dake hannunsa. Nan take tsohuwar ta saki fuska, sannan ta musu alama da su shiga cikin ɗakinta.

“Anya za mu iya yarda da wannan tsohuwar me kamar yamusasshen ganye?”

Cewar Adam murya ƙasa yana duban abokansa. Arman ya bugi cikinsa da bayan hannunsa.

“Ka mana shiru, a wannan halin da muke ciki ba mu da ikon zargin kowa, mu dai kawai abin yin mu shi ne kare kai a lokacin da aka kawo mana farmaki”

Cewar Arman.

“Haka ne Adam, tun da har muka yarda da tsohon can ita ma babu dalilin da zai sa mu ƙi yarda da ita”

Cewar Ivana.

“Ku shiga mana”

Tsohuwar ta sake faɗa tana nuna musu ɗakinta da shi ma aka gina shi da ƙasa. Sai da suka gama ƙarewa gidan kallo, sannan suka shiga ɗakin nata da babu komai ciki sai wani gadon katako. Sai wasu jakukkunan fata dake gefe guda. A kan gadon dake ɗakin suka jeru su uku, Adam har da fitar da camera ya fara ɗaukan ɗakin a hoto.

A lokacin kuma matar ta shigo ɗakin, hannunta tiƙe da wani abu me kamar kofi, ta aje musu tana faɗin su sha abin ciki, dai suka girgiza mata kai a tare, alamun ba sa sha. Suna ganin sanda matar ta yi murmushi, sannan ta juya kanta tana kallon ƙofar ɗakin, cikin muryarta ta tsufa ta ƙwala ƙiran.

“UWAIS!”

Cikin abin da ya zarce mamaki Arman, Adam da Ivana suka dubi juna, sannan suka kalli farar dattijuwar, idan dai har ɗan rakiyar da za su tafi da shi ya kasance UWAIS ke nan wannan matar ita ce gimbiya FEROZA, wato mahaifiyar Amir UWAIS BIN DHAAKIR?.

_____•••____

UWAIS.

A hankali daddaɗar iskar dake busawa a dajin take kaɗa ganyayyakin bishiyun da suka ƙawata shi. Yayin da wani daddaɗan busar sarewa ke tashi a cikin dajin, da daɗin da yake naiman zarce na iskar da ake. Daga can kan reshen wata doguwar bishirya yake zaune, ya harɗe ƙafafunsa, yayin da iskar wurin ke ɗaga dogon gashin kansa, idanuwansa kuma a lumshe, domin shi kansa yana jin daɗin busar.

Sanye yake da Sirwal, wani nau'in tufafi irin na wancan zamanin, wanda ake yinsa da zare lilin. Takalman ƙafarsa na fata ne, wanda suke da zaren ɗauri, akwai ɗan siririn rawani a kansa, wanda bai ɓoye dogon gashin kansa ba. Wasu kyawawan tsuntsaye dake kan bishirya da yake zaune ne ke ta kukansu me daɗin saurare, waɗan da suka ƙarawa busar tasa ta yau armashi.

Cak busar sarewar ta tsaya, sannan a hankali ya buɗe kyawawan idanuwansa masu ɗauke da shuɗiyar ƙwaya. Ya motsa kunnensa na ɓarin hagu, domin jiyo abin da yake dajin dake gaban wanda yake ciki. Gurnanin damusa haɗi da kukan barewa ya jiyo lokaci guda.

Hakan tasa ya yi saurin miƙewa a kan reshen bishirya, sannan ya sofare zarewar hannunsa a cikin ma'ajiyarta dake saƙale a ƙugunsa. Tsalle ya daka ya iyo ƙasa, sai dai kafin ya kai ƙasa ya buɗe fukafukansa da ba su bayyana sai idan har shi ya bayyanar da su ya tashi sama. Cikin abin da bai fi ƙiftawar ido ba ya isa dajin dake kusa da wanda ya baro.

A kusa da inda yake jin gurnanin damusar ya sauƙa, kuma yana sauƙa ya sake ɓoye fukafukansa guda biyu, ya tsaya yana kallon wata baƙar damisa da take shirin farmakar wata barewa. A hankali ya miƙe tsaye, sannan ya zaro sarewarsa dake maƙale a ƙugunsa, ya juyata a hannunsa, nan take ta rikiɗa zuwa bakar da aka ƙera da ɗanyar azurfa, sannan a hankali ya riƙeta da hannunsa na hagu, ya ɗagata sama, tare da saitata a kan damisar, yatsun hannunsa na dama ya motsa, wata farar siririyar kibiya ta faɗo hannun nasa, a hankali ya saita kibiyar a jikin bakar, sannan ya sakata cikin yatsun hannunsa biyu.

Ya kanne idonsa tare da karkatar da kansa gefe, sai da ya saita damisar sosai, sannan ya saki kibiyar, babu kuskure ko kauce hanya kai tsaye kibiyar ta soki damisar a gefen cikinta, kukan da damisar ta saka ya sa barewar da take hari da farko ta razana ta falla cikin dajin da gudu.

Murmushi ya yi kawai, sannan ya juya bakar ta rikiɗe zuwa sarewa, ya sake saƙalata a cikin ma'ajiyarta me kama da gidan takobi, sannan ya yi wurin da damisar ta faɗi tana numfashi da ƙyar, tsuggunawa ya yi a kanta, ya kalli wurin da ya harbeta na ta zubar jini.

“Idan aka ce ku koma cin ciyawa ba iyawa za ku yi ba, kuma idan aka ce kada ku cutar da dabbobin da ba su ji ba ba su gani ba ƙi kuke, ya za mu yi da ku ne?”

Ya tambaya yana ɗora hannunsa a kan kibiyar, sannan a hankali ya zareta daga cikinta, ya shafa wurin da ya harbeta, sannan ya miƙe yana kallonta.

“Allah ya baki lafiya”

Yana gama faɗar hakan ya buɗe fukafukansa ya tashi sama. Yana shawagi a iska kiran mahaifiyarsa ya riske shi, hakan yasa bai sauƙa a ko ina ba sai a cikin gidansu.

IQRAH.

Ƙuri ta yi da ido tana bin yariman da aka ce shi ne wanda za'a aura mata da kallo, fuskar nan a haɗe, dan sam babu alamar fara'a a tattare da ita, ta cika ta yi fam, jira take a tsikareta ta fashe tau!. Ba sai an yi wani tone-tone ba, sam ita matashin bai mata ba. Ba wai dan ba shi da kyau ba, ba kuma dan ba shi da nasaba me kyau ba, sai dan kawai Eid shi ne a zuciyarta.

“... Yanzu amincewar Gimbiya kawai muke buƙata, daga zarar tace eh sai a saka ranar aure!’

Mahaifin yariman ya faɗa, Iqrah ta kalle shi, sannan ta kalli mahaifinta Malik Cangaz da shi ma ke zaune a ɗakin cin abincin. Amma shi sai ya ƙi ya kalleta, ya yi murmushi me kyau, sannan yace.

“Babu buƙatar sai mun ji daga gareta, dan haka yanzu ma za mu iya saka ranar da za'a yi auren”

Maganarsa ta tarwatsa duk wani fata da Iqrah ke da shi, kuma dalilin maganarsa yasa ta ƙudiri aikata abin da ba zai musu daɗi ba daga ita har shi. Ta kalli yariman tana jin kamar ta shaƙo wuyansa ta maƙure shi a bango har sai ya daina numfashi, sannan ta kalli mahaifinta, sai dai ba ta da ikon cewa uffan. Har suka gama yanke abin da za su yanke, aka sallameta.

Champa da sauran hadimanta suka mata rakiya zuwa ɗakinta. Sai da suka sadata da ɗakinta, sannan ta sallami sauran hadiman, ta dakatar da Champa kawai. Sannan ta dubeta tana faɗin.

“Gobe ki tabbatar kin zo min da kayan da kika saba kawo min na saka a duk lokacin da nake son na yi shigar ɓadda kama na fita, kada ki bari kowa ya san cewa gobe zan fita domin ganawa da Eid!”

Kan Champa a ƙasa ta jinjina shi.

“An gama gimbiyar kyawawa”

Daga haka ta mata lamunim fita daga ɗakin. Tana shirin zama a bakin gadonta ASRA ta shigo ɗakin, kamar kullum, sanye ce kin shigar yaƙi, domin a ko da yaushe ita tana cikin shirinta na yaƙi. Kallon juna suka yi, kafin Iqrah ta ɗauke kai ta zauna a kan gadon cike da damuwa. Asra ta ƙarasa cikin ɗakin, sannan ta zauna kusa da 'yar uwarta me matuƙar kama da ita.

“Ina kika tafi tsawon kwana uku bana ganinki?”

Iqrah ta gefo mata tambayar bayan wani lokaci. Asra ta yi murmushi.

“Malik ne ya tura mu yaƙar wani ƙauye dake cikin dajin Urf al-tawul... Tafiyar ta taso a bazata, shi yasa ban sanar miki ba kafin mu tafi!”

Iqrah ta kalli 'yar uwarta, ita ke nan rayuwarta ba hutu, a ko da yaushe sarki na bata ayyukan da suka girmi hankali, har suna ganin kamar ya manta a mace aka haifeta ba namiji ba. Domin ya mayar da ita tamkar namiji, hatta da muryarta ta fi ta mata girma, yanayin tafiyarta da kuma shigarta ya banbantata ta mata, duk da ta kasance mace.

“Darvesh (Holy man) yace min ya zaɓa miki mijin aure, hasali ma nan da mako guda za'a yi aurenki... Faɗa min kina farin ciki?”

Asra ta tambaya, Iqrah ya juya idonta.

“Bana farin ciki Asra, saboda bana son zaɓin Abbu, ni ina da wanda nake so, amma na san ko da na sanar masa da hakan ba zai goyi bayana ba”

Asra ta dafa kafaɗar ƙanwarta.

“Haka ƙaddarorinmu suke Iqrah, daga ni har ke ba za mu iya sauyasu ba, dole ne mu bi abin da Malik yake so, ko da kuwa mu ba ma ra'ayin hakan!”

Iqrah ta miƙe tsaye.

“Na daɗe ina bin duk wasu dokoki da zai kafa min, amma ba zan bi wannan ba...”

“Me za ki yi ke nan?”

Asra ta kasteta tana miƙewa ita ma.
Chapter 19 · 0% Book details