← Book details Hurriya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 29

Sashe 6

Hurriya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya amsa a fusace sannan ya saka talkaminsa ya fice daga falon, har lokacin Hurriya na tsaye bakin kofar ta kasa yin komai sai hawaye, a nan ta gane wani abun ake iya yi ma magana ko kuka, ta sani sarai tana kuka ko furta wani abun zai iya kara mata ko ya rufeta da duka, domin ba yau ya saba ba. Ko kwakkwaran motsi bata yi ba sai da ta ji ta a jikin Yassar ya rumgune yana bata hakuri sannan ta fashe da kuka.

“Yi hakuri Allah zai saka miki”

Hajiya Kaltume dake saukowa rike da plate ta soma fadin.

“Ya saka mata ga wa? Wai Yassar ba zaka daina wannan bakin shisshigin ba? Yadda kake da alaka da ita fa haka yake da alaka da ita, idan ma kwantar da ita yayi ya yanka ina ruwanka?”

Dagowa Yassar yayi ya kalleta.

“Haba Hajiya ai ko mai aikin gidan nan wani abu ba zai same ta na yi magana ki ce ina ruwana ba balle kuma Hurriya, marinta fa yayi kamar ya samu babbar mace”

Hajiya Kaltume ta yi fuskar tausayi kamar gaske yadda ta tambaya sai ka rantse bata san abun da ya faru ba, bayan kuma tana sama a tsaye stairs tana magana da Umm Khairi lokacin da Hurriya ta shigo.

“Ayya ah gaskiya be kyauta ba, me ta yi masa?”

“So take ta tantance waye a gurin kawai ya sauke mata mari”

“Oh Subhanallahi, Sannu Hurriya ina glass din naki?”

Cikin wani irin kuka mai tsarke numfashi Hurriya ta soma magana.

“Hamad.... Hamad... Hamad.. Ya fasa.. Shi..”

“Saboda me? Kai Hamad akwai mugun hali ita Iyami tana aikin me yayi miki haka?”

Line by line ta fada musu abun da ya faru tun a school har dawowarsu gida, ciki har da tafiyar Amma da hudubar da ta yi musu. Ciki wani yanayi na damuwa da rashin fahimta da kuma faduwar gaba a lokaci daya Yassar ya kalli Hajiya Kaltume, Hajiya Kaltume kuma ta juya ta kalli ƴarta Umm Khairi, suna haɗa ido fuskarsu ta soma fadada da murmushi, tunawa da Yassar na dakin ya saka Umm Khairi ta fara tarin karya, Hajiya Kaltume kuma ta daure fuska.
Yassar da ya tattara hankalinsa gaba daya gurin kanwarsa Hurriya ya ce

“Kamar ya sai ta haihu zata dawo?”

“Haka tace mana, kuma bata jima da tafiya ba, har ya fara min duka, Wallahi kashe ni zai yi idan muka zauna a can mu kadai”

Ya kalli Hajiyarsa cikin yanayin damuwa sai ta girgiza masa kai alamar bata san komai ba, hannun Hurriya ya rika.

“Zo muje part din na ku”

Har lokacin kuka Hurriya take tana biye da yayanta dake rike da hannunta suka fice. Umm Khairi ta sauko da sauri tana murmushi ta dafa Hajiya Kaltume da ta kai zaune baki har kunne tana mamakin jin kalaman Hurriya.

“Hajiya Appa ya saki Amma kenan?”

“Ina kyautata zaton haka, domin dazun da safe shi ya kira ni da kansa ya ce min na dauke Bedsheets dinta na kawo masa abun karyawa, har na ce masa bana son ta ga kamar ina shigar mata hakki, sai ya ce min baya son digon zance zan karbi girki a yau”

Umm Khairi ta rumgume Hajiya Kaltume da sauri tana murna.

“Wayyo Allah na dadi, amman me yasa ba ta fadawa Hurriya gaskiya ba?”

“Waya sani? Toh ko ganin take zata dawo? Zama be gan ni ba ungo wannan kai min Kitchen bari na kira Hajiya Fatee”

Ta mike tsaye da sauri, daga ita har yarta Umm Khairi kallo daya zaka yi musu ka fahimci farinciki dake zuciyarsu, da rawa Umm ta karasa kitchen ta aje plate din ta fito ta shiga dakinta ta dauki wayarta ta fara kiran yan'uwanta da basa gidan tana musu albishir domin sun dadi ba su samu wani labari mai dadi da faranta zuciya ba irin na yau.

Hajiya Kaltume na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta saka key dan tabbatar da ita kadai ce a dakin sannan ta nufi wayarta cikin nauyin jikin dake hana masu kiba da teba hanzari a duk lokacin da suka yi yunkurin yin haka. Sai da ta fara zaunawa sannan ta dauki wayar ta lalabo number aminiyarta Hajiya Fatee duk kuwa da kasancewar ta girme ta nesa ba kusa ba, sai dai friendship be duba age ko level idan jini ya hadu, cikin natsuwa Hajiya Kaltume ta aika mata da kira, zuciyarta har wani bugawa take irin na jindadi da farinciki da tun da aka auro Iyami rabonta da irinshi.

“Assalamu Alaikum Hajiya Kaltume”

“Na'am Hajiya Fatee ke kadai kike?”

“Ni kadai nake yanzu yar iskar yarinyar nan ta fita”

“Ba dai Afra ba?”

“Ita fa”

“Ikon Allah yaushe kuma ta fara zuwa gidanki?”

“Yanzu fa, ina zaune sai gata ta zo ita da yara wai an zo a gaishe ni, waya sani ko wani mugun abun aka kullo min a kawo min, ta mallake ni kamar yadda ta mallake min ďa”

“Tsab kuwa zata iya shi, indai magani ne wannan yarinyar babu inda bata sani ba, gashi ta tsaneki ko maganin mutuwa ma zata iya miki”

“Kamar an yi a gabanki, ai an sha fada min ta yi ta yi samun sa'a ne bata yi ba, shiyasa na tsaya a kafata bana wasa kar ta jedar da ni a zuciyarsa kuma Wallahi idan ina da rai sai Fadil ya kara aure”

“To ke Hajiya Fatee anya wannan shedaniyar surukar ta ki zata yarda ta bar Fadil yayi aure?”

Hajiya Fatee ta yi dariya.

“Hajiya Kaltume kenan kina magana kamar baki san wacece ni ba, ai idan ta kwana da shiri wani a hanya ya kwana, daga ita har uwarta sai sun kyale min ďana, komai shige shigensu da tsafe tsafe da yardar Allah sai hankalin Fadil ya juyo kaina ni ma sai na sarrafa ďana yadda nake so”

Hajiya Kaltume ta jinjina kai tana kara yarda da zancen Hajiya Fatee.

“Na yarda da haka, domin a yanzu na sarawa lamarinki, ni yanzu ma kira na yi na yi miki albishir, dazun da safe Alhaji yake ce min na kawo masa abun karyawa na cire Bedsheets din da Iyami ta saka, ni tun a lokacin na san wani abu zai faru, kuma na tambaye shi lafiya be fada min ba, yanzu kuma Hurriya ta shigo tana kuka wai Hamad ya daketa a nan take fada mana Amma bata gidan wai ta tafi gidansu har sai ta haihu zata dawo”

Hajiya Fatee ta daki cinyarta da karfi ta kyalkyale da dariyar ƙeta da jindadi.

“Ke daga jin haka ai kin san abun da muke nema ya samu, ai duk wanda ya ci tuwo da mu miya ya sha, kuma gadon ari sai fanna, sirrin iya sai marɗibo, yanzu kam sama ta yi wa yaro nisa sai dai ya tada kai yayi kallo, ai na faɗa miki kowa yace zai iya haɗeye gatari to sakar masa ɓota, kuma idan ta sha mu ba mu karya ba, yaro baya ja da mu muja da ubansa...”

Haka Hajiya Fatee ta rika jero kirari da karin magana cikin alfamari da tinƙaho. Hajiya Kaltume ta miƙe tsaye ta fara yawo a ɗakin tana jin kamar ta taka rawa.

“Wallahi sai a yau na ji wannan ƙunci da nauyin da ya tsaya min a zuciya ya sauka, tun da Alhaji ya auri Iyami farinciki ya gagareni, duk wani abun da zan samu a duniyar nan farincikina raggage ne, saboda Iyami, yarinya daga zuwa aiki kin aure mai gida har da su ƴaƴa gashi ya murje ido ya nuna kamar ya fi sonta da kowa, ƴaƴanta ma kamar ya bude ciki ya saka su ya rufe haka yake ji”

“Toh daman ina ke ina kwanciyar hankali da farinciki Hajiya? Mai aiki ta aure miki miji? Ai haka suke shiyasa ake cewa ďan iska na birni shege na kauye sai tsoron ɗansa, ai da zarar sun yalla ido sun ga ana jindadi a gida to sai sun aure miki miji, ita wannan shegiyar gorar Afra da ta fahimci duniya kin ga duk bokonta bata son ko mai raino balle kuma wata mai aiki”

“Tana da gaskiya Wallahi, sai dai haka kuma ba zai hana ďan mu kara aure ba”

“Aure kadai? Ai sai ta bar gidan nan matukar ina raye, duk wata mallaka da ta yi ma ďana sai na kwance ta, kuma ki zuba ido ki gani ba dai wannan Malamin ya iya aiki ba zaki sha mamaki”

“Yanzu so nake ki shirya mu kai masa sallama kuma na sake fada masa bukatar domin ina gudun kar ya maida ita”

“Karki damu, bari sai kura ta laba zamu sake komawa, daman ai na fada masa duk abun da aka ba shi karin alkalami ne kawai, biya sai bukata ta biya”

“Lallai kuwa zan masa biya mai kyau, domin ya yaye min bakincikin da nake kwana na tashi da shi, a kullum burina Iyami ta tafi ta bar min miji, yau kuma wannan burin ya cika Alhamdulillah”

Dariya suka yi a tare sannan Hajiya Kaltume ta yi mata sallama ta sauke wayar tana jin kamar an mata bushara da gafara.
[10/18, 5:34 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆

𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

𝗣𝗮𝗴𝗲 4️⃣

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”

Shi ne abun da Hajiya Binta take ta nanatawa idonta a rufe domin danta be zo mata da labari mai dadi ba, a cikin matansa daga wanda ta rasu har wadanda suke a gidansa yanzu babu wanda take so irin Iyami, domin macece wadda ta san kanta take bata girma take rawar jiki da ita tana kyautata mata kamar uwarta.

“Subhanallahi Tsoho baka kyauta ba, ka yi gaggawa kuma daman gaggawa aikin sheidan ne, ina ma baka aikata ba ka dan daga mata kafa ko kuma na turata gidansu har sai ka samu natsuwa”

Cikin wani kalar rauni da rashin sukunin abun da ya aikata ya sake noce kansa kasa ya sauke ajiyar zuciya.
Chapter 6 · 0% Book details