← Book details Hurriya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 29

Sashe 20

Hurriya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hurriya ta share hawayenta da sauri ta juyo, sai gata ta sauko daga saman gadon bata ko kula Namra ba ta ratsa gefenta ta fice da gudu, duk wata dokar sauka ko hawa stairs na Momy manta su Hurriya ta yi a lokacin saboda zumudin zuwan Kakarta Hajiya Binta a gidan, kamar yau ne zata fara ganinta a gidan haka Hurriya ta ji. Da sauri ta bude kofar fita falon Momy bata kula komai ba ta saka kai zata fice, da mugun karfi ta ji kanta ya daki wani abu mai karfi har sai da ta yi baya kamar zata fadi. Dagowar da zata yi ta duba me ta buga domin be yi mata kama da karfe ko icce ba, ta ji an wanke mata fuska da lafiyayen marin da ya haddasa mata ganin wadansu kananan taurari, gilashin da yake mafaka ne a idonta ya fadi kasa, sai hudu da buji suka mamaye ilahirin idanuwanta. Sai ta tsaya cak irin tsayin da ta saba yi a duk lokacin da wani bakon al'amari ya ziyarceta.

Gafen fuskarta ya hau zugi yayi ja, idanuwanta suka masa tantance mutunen da ke tsaye a gabanta, fafadane ta ga hakan a cikin hudun idanuwanta, dogo ne irin tsayin da ta tsaya iyakar kirjinsa. A hankali ta sulale ta kai kasa ta saka hannayenta tana lalaben gilashinta hawaye na kwankwaso mata kofa. Lalabe ta yi ta yi amman ta kasa jin gilashin, kamar yadda ta duka haka ta mike tsaye a hankali ta juya ta lalabi kofar falon ta fara tafiya.

“Hurriya... Me ya same ki”

Namra ta tambaya tana nufota da sauri ta kama hannayenta ta rike domin hawaye take kamar an bude kofar fanfo.

“Ya... Ya... Namra... Gilashi... Na...”

Namra bata tsaya komai ba ta rika hannunta ta juya da ita suka fita tana janye da hannunta, har lokacin Mutumen da ya mareta yana a gurin tsaye ko yatsansa be motsa ba. Namra ta kalleshi kamin ta sako hannun Hurriya ta fara duba gilashin, can gefe ta hango shi ta nufi gurin da sauri ta dauko mata.

“Har gefen ido daya ya fashe daga sama, me ya faru Hurriya”

Ta saka mata gilashin da kanta, lokaci daya ganinta ya dawo fashewar da gilashin yayi ba irin wadda zai hanata gani ba ne, daga sama ne ya fashe shi ma kuma kadan. Hurriya ta daga ido ta kalli mutumen da be mata uzuri ba ya wanke fuskarta mai tsada da mari. Hawaye be daina mata zuba ba, hakan kuma be hana idanuwanta ganin mutumen da kyau, dubansa ta yi ta dube shi, ta sake dubansa sannan ta sauke idonta kasa ta ratsa gefensa ta fara sauka kasa. Slowly ya juya ya kalleta kamar mai son gasgata wani abu ko karyatawa.

“Bata gani sai da gilashi, me ya faru Yaya?”

Ya juyo ya kalli Namra a fusace.

“Aza min bindiga sai na fada miki”

Jinin jikinta ta sha ta kauce ta ba shi hanya ya shiga ciki, ita kuma ta ja kofar sannan ta bi bayan Hurriya domin gaishe da Hajiya Binta, kamar yadda Appa ya sabarwa kowa a gidan ko baka cikin gidan idan mahaifiyarsa ta zo matukar kana cikin garin sai ka zo ka gaisheta...

[10/18, 5:16 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆

𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Pease ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy

𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣3️⃣

Da kallo ya bi Hurriya da Hamad har suka fice sannan ya kalli Hajiya Kaltume ya dauke kai ya nufi stairs. Yana shiga dakinsa abun da ya fara yi shi ne duba gurin da ya aje gilasan Hurriya, amman be ga ko daya ba, a nan ya fara tunanin ko ya canja musu gurin ajiya ya manta, haka ya bi komai na dakin ya duba ba gilasan babu alamarsu, fitowar yayi mamaki duk ya cika fuskarsa ya sauka kasa sai ya samu mahaifiyarsa a gurin da ya barta zaune sai dai wannan karon waya take amsawa, gefenta ya zauna a hannu kujera har sai da ta gama wayar sannan ya tambaye ko ta dauka.

“Me zan yi da gilasai kuma? Komai dai ni, ubanka ya dora min laifi matan ubanka su adabe ni kai kuma yanzu ka zarge ni da satar gilasan Hurriya saboda ga Kaltume makiyiyarta ko?”

Maganar Hajiya bata masa dadi ba kuma ya san duk wani kalami da zai dora bayan nata a yanzu ba zai fahimtar da ita. Dan haka ya tashi ba tare da ya sake cewa komai ba ya nufi dakin yan'uwa daya bayan daya ya bi yana tambayarsu kowacce tace masa bata dauka ba, Khairi har da hadawa da rantsuwa saboda ta fi kowa rashin tsoron Allah.

‘Toh ko Hurriya ta zo ta dauka ko Hamad ban sani ba?’

Ya tambayi kansa, sai dai ya san ba su taba masa haka ba, idan tana bukatar abu zata yi masa magana kuma idan ma ta dauka zata fada masa. Fitowa yayi daga bangaresu ya nufi bangaren Momy, kamar ance masa juya ka gani, yana juya ya kalli bangaren Appa sai ya hango Hurriya tsaye tare da Appanta ta rike hannunsa tana ta bata rai da alama makiya take masa kan wani abu. Fasa nufar bangaren Momy yayi sai ya nufi bangaren mahaifinsa domin tambayarta ko ta dauko gilashin be sani ba.

“Appa dan Allah daga wannan ba zaka sake yi ba”

Ta fada cike da shagwaba tana kara rike hannunsa.

“Haramun ne, ba kyau Hurriya ni bana sha'awar irin abubuwan nan”

Appa ya fada yana kallon Yasir da ya iso gurin fuska a sake.

“Me take so Appa?”

“Birthday kuma ka sa be da kyau ba al'adar mu ba ce hausawa wannan dabi'un turawa ne”

“Oh Appa yanzu kai ya waye fa, ba wani abun ba ne kawai dai ana samun tsabanin fahimta ne ga mutane, kuma yanzu zamani ya canja ba kamar lokacin baya ba”

“Ko zamani ya canja ni ban canja ba Yasir, abun da duk ba tarbiya ba bana sha'awar”

“Appa sau daya zamu yi fa, daga wannan ba zaka sake ba? Appa please kawaye na duk ana musu sai ni”

Tana maganar tana son yin kuka Appa yayi murmushi.

“Shi ke nan na ji, za a dafa shimkafa fara ayi sadaka”

Ta buga kafa daya a kasa tana kukan da babu hawaye, Yasir kuma ya saka dariya.

“Appa dan Allah dai Appa”

Ba kasai Hurriya take zuwa masa da bukata ba, kusan duk wata bukata da take gabatar masa da ita kidayayyyiya ce, hakan ya sak idan ta zo masa sai ya biya mata ko dan tausayinta da yake na lalurar dake tare da ita, balle kuma yanzu da tausayinta ya ninku a zuciyarsa saboda rashin Amma a gidan, sai yake ganin yaransa kamar wasu marayu da uwarsu ta mutu ta bar su.

“Na ji amman daga wannan ba za'a sake ba?”

Ta amsa da sauri tana tsalle.

“Na yarda Appa na yarda Allah ya saka da alheri, Appa Allah ya biya maka bukatunka na alheri ya rabaka da Hajiya Lafiya ya kara buda maka a kasuwanci ya kyautata karshenka”

Ta masa kwatankwacin addu'ar da Amma take masa idan yayi mata wani abun kyautata da ta ji dadi. Appa ya shafa kansa yana jin zuciyarsa da tausayin da be san na minene ba. Yasir ma murmushi yayi yana taya ta murna yadda Appansy ya amince da wuri.

“Bari mu fara neman Gift din da zamu bawa mai birthday”

“Har da kyauta ake badawa?”

Appa ya tambaya sai Yasir ya amsa masa.

“Eh Appa idan mutum yayi birthday ana ba shi kyau sosai ma, kowa da kalar abun da yake ba shi”

“Oh toh saboda ki ci kudinmu kike son yi birthday kenan?”

Cewar Appa yana kallonta da zolaya, sai ta saka dariya kamar ba ita ta rufe idonta.

“Appa ba da kai ba an yafe maka”

Shi ma dariyar yayi, ya bita da kallo domin tuni ta nufi bangaren Momy domin labartawa Hamad cewar Appa ya yarda zai mata birthday kamin ya isa gurin hawaye ya cika idonta domin ta saba idan aka mata albishir Amma take fara fadawa sai dai a yau babu Amma a gidan kuma ta san babu wanda zai taya ta farinciki da murna sai dan'uwanta. Tana ahiga falon sai ta ja ta tsaya tana kallon Musib da ya hada hannayen Hamad ya rike yana zabga masa mari.

“Ba zaka yi magana ba? Waye yaje ma fadawa Appa karya da gaskiya ya zo ya rufata ta fada? Tsakanin kai da Hurriya”

“Ni ce”

Ta amsa kai tsaye domin ba zata jure ganin ana duka dan'uwanta ba da yaki yayi magana kuma ya ki yayi kuka sai dai idanuwansa sun kada sun yi ja sosai sai wani cika yake yana batsewa alamar zuciyarsa ta gama kawowa.

“Okay zo nan bakar mufuka wato daga dawowarku za ku fara hada Momy fada da Appa ko?”

Bata zo ba kamar yadda ya bukata sai dai kuma bata matsa daga inda take tsaye ba ssi hawayen da ta shigo da su suka fara sauko mata, Hamad ya juya ya kalleta har lokacin be ce komai ba, daman tun shigowarsa falon Musib ya rike shi wai sai ya fada masa waya fadawa Appa gulma har ya shigo yana mata fada ta yi kukan, Hamad ta kafiya ya ki magana hakan ya saka Musib dukansa. Musib ya saki hannun Hamad ya nufi gurin da Hurtiya take tsaye ya fara kai mata duka sai ta boye fuskarta ta fara kuka, yadda Hamad ya nufo gurin da suke tsaye sai ka dauka zai yi dambe yayansa Musib ne, ficewa yayi daga falon Musib na kokarin rikoshi ya fisge ya fice da gudu, be zame ko'ina ba sai gurin da Garden din gidan yake ya samo manya manyan duwatsu ya dauko har uku ya fito da su ya nufi gurin da Motar Momy take ta fara jefan gilashin a take ya fasa mata gilashin mota ya koma dayan bangaren ya sake jefawa. Kamin yayi na uku Appa da Yasir da suke tsaye a gurin da Hurriya ta bar su, suka iso gurin da sauri domin sun lura da lokacin da ya dauko duwatsu sun san ba za'ayi mai kyau ba, Yasir yayi saurin rike Hamad.

“Kai miye haka?”

Sai a lokacin Hamad ya fashe da kuka yana maida magana.
Chapter 20 · 0% Book details