← Book details Hurriya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 29

Sashe 22

Hurriya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Toh ni dai ina ganin abun da ya kamata kawai mu saka a nemo mana malamin nan ko Allah zai saka mu dace”

Hajiya Fatee ta mata wani kallo galala.

“Waya zai koma a wannan dajin? Ko gawata ba za a kai ba”

“Aa ina fa? Ni ma ai ba zan yarda ba, ba komawa zamu yi ba nemansa zamu yi idan ya so shi sai ya zo ya same mu”

“Ta ina? Duka wayoyin mu suka karbe fa, ba ni da number ba, kuma da aka yi welcome din Sim din har yanzu be kira ni ba, waya sani ma ko shi ya turo a dauke mu? Mutanen nan kauye nan fa ba su da kyau”

“Kai bana tunani haka, kin ga ni fa na ga kyau aikinsa domin shi kadai ne yayi min aiki kuma aikin yayi yadda nake so har Iyami ta bar gidan nan, shekara nawa ina kashe kudi a banza ban dace ba sai a gunsa, sa zaki yi a nema mana shi waya nuna miki gurin Malamin”

“Wata kawata ce Salame”

“Toh ita zaki saka ta je ta dauko mana shi, sai mu saka gurin haduwa da shi ba dole sai ya san gidan mu ba, mu gabatar masa da bukatanmu mu basa kudin aiki, daga nan ma sai na tambaye shi ina aka kwana zancen aikin Iyami, ke kuma sai ki saka yayi miki na wannan mugun abun da yake cikinki”

Kallon rashin fahimta Hajiya Fatee ta yi mata

“Ya danne miki shi mana, ba zai taba tashi ba har ki mutu, ko baki san ana haka ba? Na Iyami ma so nake a danne shi kar ta haifa ma Alhaji mugun abu, dan na san duk wayonta be wuce Alhaji ya mutu ta ci gado ba”

Hajiya Fatee ta kalleta wata rahma na saukar mata a ruhi, jin kamar ta samu mafitar masifar da take ciki.

“Kuma kina ganin hakan zai yi?”

“Me zai hana? Ki dai ki zuba masa kudi kawai, ni ma kudin zan zuba masa, kuma a hannun Alhaji zan karbe su, kudin sarkar zinarin da ya siyawa Hurriya da kudin da ya bawa Iyami duk sai na fanshesu a hannunsa, yanzu ne za su gane sun yi kuskuren taba mace kamar ni, kuma Wallahi sai na malleke Alhaji ko ta halin yaya, sai ya dawo a tafi hannuna Iyami da ƴaƴanta sai sun ɗanɗana kuɗarsu, Iyami sai ta gane kuskuren da ta aikata na aurar min miji, sai ta yi nadamar hada shimfida da Alhaji, matsayin da ta taka a baya na tana Matar Alhaji ina Matar Alhaji sai na saka ta yi nadamar haka... Ba ita ba har Nafisa sai na sake mata sabon karatu na goge mata hadda. Dukansu sai sun dawo a tafin hannuna”

Ya daki tafin hannunta tana kashe ido alamar yanzu ta shiryawa rashin imani, da kuma fada da Iyami da Momy.

________________

Hmmmmmm Allah yasa kuna hango abubuwan da nake hangowa 🤔

Tafiyar fa duk duka yanzu aka fara.... Ku daura ɗamara ku zage damtse domin domin alkalinmin da zafinsa ya zo 😁

Kar a manta idan an karanta ayi sharing 🥰
[10/18, 6:15 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆

𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Hello Habibaties 😍🥰
Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy

𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣2️⃣

Musib ya aje ma Captain keys din motar Momy da ta bada umarnin a dauko masa. Kallon Keys din yayi sannan ya mika hannu ya dauka ya mike tsaye. Tsabar bacin rai zuciyarsa har zafi take kamar zata fashe, baya jin yana da sauran wata magana a yanzu kuma baya bukatar yi ma Momy sallama bayan an bata masa tayun mota a gidanta. Shi ya fara fita sannan mahaifiyarsa ta bi bayansa Momy da Musib suka biyo shi suna ba shi hakuri kamar su suka masa laifin shi dai be ce uffan ba ya matsa key hannunsa motar ta fita key ya sannan ya nufita har suka bar gidan kalma daya bata sake fitowa daga bakinsa. Ran Momy be yi dadi ba ganin ďan ďan'uwanta da take ji da shi ya fita cikin bacin rai.

“Ni abun nan ya ba ni mamaki, wai waye yayi wannan aika-aikar”

“Zai wuce Kaltume? Ai bata son kowa da alheri a gidan nan kuma ta ga mota mai tsada ina za so haka, ballantana fitowar nan da ta yi dan uwa ko daya be je ya mata barka da fitowa ba”

“Amman Momy Yasir dai ba zai yi haka ba kin san ko da ta saka shi”

“Su matan fa? Kuma shi ma ba munafurci ba ne da nuna soyayyar ido, ai ta ciki na ciki dan'uwa be taba son dan'uba ba har abada”

“Ko kuma ta aiko wani yayi ba”

Ta juyo tare da Musib suka shigo falon, ko zama ba su yi ba motar Appa ta faka a harabar ya bude ya fito ya shigo cikin falon fuska a dauke.

“Ku ba mu guri zan yi magana da mahaifiyarku”

Appa ya fada immediately after ya rufe kofar falon, Musib ya dubi Miwan sannan suka tashi suka haura sama, Momy kuma ta zauna ita ma nata ran a bace tana sauraren da wacce Appa ya zo.

“Nafisa ina son na tambaye ki, akwai laifin da Hurriya ta yi miki ko kuma Hamad?”

“Wani abun aka fada kuma?”

“Akan wani dalili zaki nemi banbanta su da sauran yayanki? Fada min banbanci dake tsakinsu da Namra ko Miwan, dukansu ba Yayana ba ne? Akan wane dalili zaki ce Hurriya sai dai ta share dakinta da kanta kuma idan zata hau stairs ko ta sauka ba ta hau kamar yadda Namra ko Musib suke yi ba?”

Momy ta rike baki.

“Oh Allah na ni Nafisa, yaushe aka yi haka? Kuma shi kenan daga fada maka zance karya da gaskiya sai ka hau ka zauna har da zuwa gurin fada ba tare da ka tsaya ka bincika ba? Shiyasa ka dauko su ka kawo min? Me yasa ba a kaiwa Kaltume ba? Ita da yake tsoronta kake sai Nafisa da aka raina itace mai dadi hawa, gashi sai mulki take mana ciki gidan ita da yaranta”

“Daga ke har ita karkashin kulawata kuke kuma karkashin ikona, dan haka duk gurin da nake ra'ayi a can yarana za su zauna, kuma ina gargadinki wannan ya zama na karshe da zan sake jin wani abu marar dadi akan Hurriya da Hamad, zan iya canja mata ban zanja yaya ba, gaba daya yarana babu na yarwa kuma bana son a batawa kowa”

“Eh amman ai ka ware wadanda kake so kake kauna, na tabbatar da nawa yayan Kaltume ko Iyami take yi ma wani abu ba zaka yi magana ba, amman da yake yayan mowa ne ai gashi nan ka shigo falo cikin bacin rai saboda an taba yan gold, ni da zaka nuna musu kauna ka dawo da uwarsu ai da duk yafi wannan nema musu yanci da kake, idan ya so sai ta rike yayanta na rike nawa”

“Abun da na ga damar aiwatarwa shi zan aiwatar, babu mai fada min gabas, na san Allah, daman ke haka kike banta zuwa da wata magana ba ki musa min ba, ban taba fada kin yi shiru kin saurareni ba sai kin fada, sa'insa da ni ba yau kika fara ba, daga ke har Kaltume babu wadda nake jin sanyinta kowacce ku da lagon da take matsawa ta bata min rai”

Momy ta fashe da kuka domin kalaman Appa sun mata zafi, ta san abun da Appa ya fada akam Iyami gaskiya ne, domin ya saba yi mata fada ko a gabansu kamar yadda su ma zai iya musu a gabanta ko kuma ya tara su gaba daya yayi musu fadan idan wani abu ya faru, su kan tanka shi su kare kansu ko maida martani amman Iyami bata cewa idan yana fada har yayi ya gama, ko daga kai ba zata yi ta kalleshi ba, wannan ta saka suke yawan yi mata kallon munafuka, hawaye shar Momy take yi daman kuma bata gama hucewa daga bacin ran abun da aka yi ma Captain ba.

“Eh sai Iyami, abar kaunarka, yanzu gashi nan ka rufe da fada akan yayanta, matarka Kaltume kuma ta takura min ta takurawa bakina, yanzu Captain ne ya zo, ka san dai yadda nake da Captain amman haka matar nan ta saka aka fasa mata tayun mota saboda bakin ciki, ban gama huce wannan haushin ba gashi nan kai kuma ka zo ka rufe ni da wani, toh Wallahi ka jawa yayanka kunne su daina munafurci, kuma ka jawa matarka matarka kunne ta fita safgata da ta bakina babu ruwanta da ni idan ba haka ba Wallahi za 'ayi tashin hankali da ba taba yi ba ko a lokacin da ka auro karamar yarinyar can Iyami”

“Ni dai na fada miki, karki sake banbanta min to ƴaƴa duk daya suke a gurina, babu wanda ya fi wani, zan iya canja mata ban canja ƴaƴa ba bana ni da kamar ƴaƴana!”

Yana kawai nan ya juya ya fice, cikin motarsa ya koma yaja ta zuwa bangare ya ajeta ya fito ya taka da kafa ya nufi bangaren Hajiya Kaltume yana shiga ita ma ya salllami yaranta suka haura sama ban da Yasir da baya gidan ma a lokacin ya fita gurin safgoginsa, Namra kuma ta fita zuwa bangarensu. Fada yayi mata sosai yana ja mata kunne akan abun da ta saka aka yi ma Momy.

“La'ilaha Illallahu ni Ummul Kultoon, yaushe kuma aka yi haka? Ni miye ruwana da Nafisa balle kuma bakinta, yanzu Fisabillahi na rasa me zan saka ayi mata sai fashe tayar baki? Abu dai kamar karamar yarinyar? Ni da nake ta kaina ma? Yaushe na fito daga daji? Kofar daki ma bana sha'awar fita balle kuma har na saka ayi wani abun, shigowar nan da ka yi ma hankalina sai da ya tashi”

“Ni dai na gargadeku, bana son wani tashin hankali kowa ya zauna lafiya kuma ya tsaya a iya matsayinsa, ku bar ni da abun da yake damuna, kullum ni ne cikin fitina kamar akaina aka fara mata aure da mata biyu”
Chapter 22 · 0% Book details