← Book details Heedayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 100

Sashe 40

Heedayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta soma bude idanta har ta budesu tas tafara bin dakin da kallo, saidai har ynxu takasa gane ina take ta dan miqe ta zauna nanne idanta suka kai kan wannan tsohuwa ihu ta sakar tsohuwar tace mata "shhhh karki damu baran cutar da ke ba" cikin harshe erin na daxu, heedayah da bata gabe me matar ke fadi ba tacigaba da ihu, daga bisani kuma se tayi shiru ta tsaya zura wa tsohuwar ido sosai can kuma seta fashe da dariya, abin yaba ma wannan tsohuwar mamaki sosai kode mahaukaciya ce yarinyan? Se kalle kalle heedayah keyi har ynxu nan tsohuwar ta matso kusa da heedayah ta dafa kanta tayi casting spell kan heedayah atake heedayah ta sume tsohuwar ta gyara mata kwanciyanta sannan taje ta aza musu girki se can dare around 10:40PM heedayah ta farfado da hannunta riqe akanta tana kokarin tuna abubuwanda suka faru a baya dagani se ynxu ta dawo hankalinta daga bisani tace "dan Allah karku kasheni ku min rai dan Allah" a daidai wannan lokaci tsohuwar tashigo heedayah na ganinta ta tsala ihu bata taba ganin farar mata kamar wannan ba inba dai a film ba gata tsohuwa sekace aljana "baiwar Allah dan Allah kar ki kasheni nasan duk don moha ne ya turo ku dan Allah kiji qaina karki kasheni pls zan gaya muku menake nema a gdansu," nan ne tsohuwar ta gano heedayah bahaushiya ce ta kariso gabar heedayah da in banda bari ba abinda takeyi tsohuwar tace "'yar budurwa kar ki damu ba abinda zan miki kinji? Bar kuka" nanne heedayah tadan samu peace of mind ta sa hannu ta share hawayenta, heedayah tace "ina nike pls? Ina wanda suka daukoni cewar zasu kasheni ina suke? Kuma ina ne nan?" Tana bin dakin da kallo tsohuwar tace nima bansan sunan wannan qauye da muke ciki ba amman de bamu da nisa daga EVIL FOREST inda na tsinto ki....nan ta lbarta ma heedayah duk abinda tasani, cikin kuka heedayah ta daga hannayenta biyu sama tare da gode ma Allah da ya kareta daga sharrin don moha da mutanensa sannan ta dawo da kallonta kan tsohuwar da itama kallonta take tace "dan Allah wace ke?" Tsohuwar tace sunana "aleesha," heedayah tace "musulma ce ke?" Tsohuwar tace "eh kusan haka," heedayah zata sake mata wata tambaya aleesha tace "kefa ya sunanki?" Heedayah tace "heedayah suna na" aleesha tace "sannu heedayah karki taqura wa kanki ynxu ga abinci acan" nan ta tashy ta dibo ma heedayah ta amsa amman takasa ci, aleesha tayi murmushi sannan tce "ci 'yata ba abinda nasa miki aciki you are safe now no one will hurt you," dakyar ta iya takai cokali baki ba gishiri ba maggi salam da kyar ta iya tadan ci kadan dan kora yunwa tana gamawa ta tambayi aleesha ko karfe nawa, aleesha tayi wani magic sannan tace "11:20PM 'yata," cikin tsoro heedayah tace "you use magic? Are u a soccerer?" Aleesha ta gyada mata kai "I was born with it," heedayah takasa fadin komi duk tsoro ya cika ta daga bisani tace "inason inyi alwala" aleesha takuma yin magic sega qwarya cike da ruwa tace "hungo yi," heedayah tace "a'a inajin tsoro," aleesha tace "ba abinda ze miki karki damu" da kyar ta gwada sa er yatsan ta aciki taga ba abinda ruwan yamata sannan ta saki jiki tayi alwala tayi sallah ta nemi gu ta kwanta bata kuma cewa aleesha komi ba haka itama aleeshan. Washegari da safe around 8:30AM heedayah ta tashy da rogowar ruwan datayi alwala dashy jiya tayi yau sannan ta zauna tana kallon aleesha, bayan 'yan mintuna aleesha ta tashy itama, heedayah tayi kamar tana bacci, aleesha tayi murmushi sannan ta fice daga dakin bayan some minutes ta dawo da abinci a hannunta ta ajiye a gaban heedayah, heedayah ta gaishe ta aleesha ta amsa sannan tace "muci abinci ko?" ...bayan sun gama ci aleesha tace "heedayah bani labarinki dan ga dukkan alamu ke ba 'yar nan bace," heedayah tace "eh aleesha ni 'yar maiduguri ce amman a kano nike da zama," aleesha tace "zaki iya kirana da baba" tare da ma heedayah murmushi, heedayah tace "toh baba" itama ta mata murmushin, tacigaba da bama aleesha labarin kanta bata bar koda tsinke ba, aleesha ta mugun tausayawa heedayah sannan tace "Allah sarki 'yata kin sha wahala sosai a rayuwarki gaskia, never trust anyone a wannan zamani amman abinda bangane ba har ynxu heedayah shine mesa don moha yakeson kasheki? Kamar yadda kka ban labari ai yana sonki then mesa ze so ki mutu?" Heedayah tayi shiru sannan tace "wannan kuma se Allah, nima kiban labarin kanki," aleesha taja numfshy sannan ta fara kamar haka...
[10/10, 4:40 PM] 🍬🛍💍Salma💍🛍🍬: 👮👮👩👩💥💥💥💥💥
HEEDAYAH!
💥💥💥💥💥👩👩👮👮
5⃣3⃣
written by miemie👄

"Kamar yadda na gaya miki sunana aleesha, shekaruna 78 a duniya, ni igbo ce gaba da baya na garin Imo, dangi na du christians ne iyayena ma muslinta sukayi, ni kadai suka haifa tun ina 'yar qarama suka rasu due to car accident da sukayi daga lokacin na soma zama gdan wata aunt dina wanda tasa ni nayi ridda nakoma christian, ta tsane ni sosai bawanda ta tsana a fadin duniyar nan kaman ni wani sa'in aljana ma take kirana badan komi ba wai dan fari na yayi yawa haka na girma cikin wahala alokacin da na kai 20yrs ne na fara discovering super natural powers da nike dashy, ba karamin tsorata nayi ba na gwada gaya ma wannan aunt dina ta koreni daga gdan ta acewarta ni witch ce haka uwata ma, i was lonely ba wanda na sani har Allah ya hada ni da miji na wanda yasoni tsakani da Allah christian ne shima, soyayya me qarfi ce ta shiga tsakaninmu wanda har ya kai ga aure ahaka aka mana aure duda iyayensa where against the marriage, ahaka har Allah ya albarkacemu da yarinya ta mace wanda yasa mata sunan mamanshi chidinma, shekarun chidinma 15 a duniya ita da mahaifinta sukayi car accident alokacin dayaje daukota daga sch bayan sunyi hutu, atake chidinma ta tamutu"...ta tsaya ta share hawayenta sannan ta cigaba, "mijina kuwa sanda yayi jinyan wata biyu sannan shima Allah ya dau abinsa, tundaga lokacin in law na tasani a gaba sam wai ni na kashe mata danta haka suka sani nasha ruwan da aka masa wanka, nakuma kwana da gawan sa dan a zatonsu ni na kashe musu da bayan an birne sa ne ta korani daga gdanta haka na ta tafiya batare da nasan inda nike zuwa ba har Allah ya kawoni wannan destination danike yau, da ba dan powers da nike dashy ba dana jima da mutuwa nima, toh fa kinji lbri na knan"...heedayah taja numfashy sannan tace "Allah sarki baba u've been through so much hardships, " aleesha ta mata murmushi sannan tace "yes my fairy god daughter," cikin rashin fahimta heedayah tace "ur fairy god daughter kuma?" Aleesha ta gyada mata kai "nasha mafarki cewa akoi wata budurwan da zata zo ta maye min gurbin 'yata chidinma nd wannan budurwa ba kowa bace illa ke," heedayah tamata murmushi sannan tace "naji kince kinyi ridda, to har ynxu a christian kke?" Aleesha tace "no nakuma zama musulma, musulma ce ni amman saidai bansan komi kan muslunci ba cuz tun ina yar qarama iyayena suka rasu" heedayah tace "toh masha Allah baba zan koya miki duk abinda ya kamata, I need a favor frm you pls, yakamata insan inda nake, I need to get back home inyi fulfilling destiny na nazamo prosecutor," aleesha tace "then we have a very long way to go, dan kinga na farko ban san ina ne nan ba as u can see nikadai ce ke rayuwa a nan amman gaba da evil forest akoi wata qauye acan kinga in har zamu sami mutanen gun zasu iya gaya mana sunan qauyen"...heedayah ta katse ta "what of money? I need money inyi kudin mota dashy," aleesha tace "its been long rabuwa na da kudi nakega tun randa nabar garin mu Imo ban sake sa kudi a idanu na ba" heedayah tace "ba kinada magic ba? Ki fito mana da kudi mana" aleesha tayi murmushi sannan tace "magic dina baida karfi ynxu 'yata daga healing mutum se protection nake iyayi nd nothing more," heedayah bata ji dadin hakan ba tace "toh ynxu ya knan?" Aleesha tace "abu daya nake tunani in xamu iya yin wata 'yar sana'a wanda a kowani asabar in aka bude kasuwa a wani waje dake qasa da nan se mu kai mu siyar ahaka zamu na tara miki har se in ya cika kudin mota" heedayah taji dadin wannan shawara sosai ahaka sukata sorting out abubuwa da dama daga karshe suka yanke hukuncin kai diffrent types of fruits kasuwan tunda aleesha na iya shiga cikin evil forest.
GARIN KANO; motar don moha na hango a unguwar su heedayah, anjima kadan yafito yayi tambaya yakuma komawa motan ya tuqa haka ya tayi har sanda Allah yakowasa gabar gdan su heedayah bayan kwanaki biyar da ya jera yana neman gdansu. Parking yayi a waje yayi knocking me gadi ya bude masa amman kwata kwata mal musa be gane don moha ba shide don moha be ce masa komi ba illa tambayar sa dayayi ko nan ne gdansu heedayah? Mal musa yace "eh nan ne saidai heedayahn batta nan yau kimanin sayi uku knan da batanta ba'a san inda take ba don moha yayi kamar besani ba ya tausayawa mal musa sannan yace "maman ta fa tna nan?" Mal musa ya gyada masa kai "kashiga daga ciki," don moha ya karisa a gaban entrance door din ya tsaya ya danna door bell bayan some seconds nanny ta taho ta bude saidai bata gane fuskar ba dan haka ta tsaya tana kallonsa daga bisani tace "dan saurayi wa kake nema?" Don moha yace "nanny?" Nanne nanny ta gano don moha ne takira sunansa da karfi harda hugging dinsa "yaushe a gari haka? Ashe Allah ze sake hadamu, kai gaskia ka girma sosai ai ban gane ka ba shigo shigo..."
[10/10, 4:40 PM] 🍬🛍💍Salma💍🛍🍬: 👮👮👩👩💥💥💥💥💥
HEEDAYAH!
💥💥💥💥💥👩👩👮👮
5⃣4⃣
written by miemie👄
Chapter 40 · 0% Book details