← Book details Heedayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 100

Sashe 19

Heedayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sannan ya daga "hello?" Meshi yace "oga sir! Gashy nan mun gama komi motocin suna inda kace muyi parking nasu, anyi kamar yadda kace honda accord V8 kawai muga ragar musu" alhj lawal yace "aikin ku yayi kyau bari ynxunnan zakaji alert" meshi ya amsa da "toh oga sir godiya muke" yayi hanging. Yace ga alhj ismail "the did is done! Komi is in place ynxu acikin motoci guda shidan nan zamu siyar da duka amman zan baka guda daya" alhj ismail yace "kaifa? Baka so ne? Baraka dau dayan ba kaima" alhj lawal yace nafison ka ne dan uwa na, zan baka *TOYOTA PRADO* (masu karatu ko zaku iya tuna toyota prado'n da alhj lawal ke son bama alhj ismail itace motar heedayah?) Alhj ismail yace "toh nagode dan uwa", kallonsa kawai alhj lawal keyi yana murmushi yafara maganan zuciya "Allah sarki dan uwa na, motan nan ba abinda zata kara maka illa tsana dan na tabbata duk sanda hjy hafsa da 'yarta heedayah suka ganka da motan, se sunji kamar su kasheka"****
Dr yace "toh alhamdulillah nasamu nayi stopping bleeding din nd Allah yaso ba internal bleeding ga magungunan nan se yana sha in shaa Allah shknan, Allah sawaqa" mummy tace "toh dr mungode" ta dawo da kallonta kan mal musa tace "Allah sawwaka sannu" yace "ameen" da kyar. Sannan suka fice masa daga daki sukayi site nasu ita da heedayah. Ciwon cikin nannay yadanyi sauki kadan so takoma kitchen tana girki a yayinda mummy ke zaune a parlour tayi tagumi da hawaye nabin kan kumatunta heedayah na share mata, shigowar matar alhj lawal sukajiyo atake suka jiyo tace "hjy hafsa! Dan Allah kar ki gayamun dagaske ne, barayi sun shigo sun muku aika aika?" Daga idanta da tayi taga ba TV' a parlourn taga kuma an tattara kayaki cikin kwalaye dayawa kamar ana packing nanfa ta sake kidimewa. Ta kira sunan mummy, mummy ta amsa, tace "wai hjy hafsa meke faruwa? Yana ganki haka?" Mummy tace "barayi ne suka shigo mana da safen nan suka tattara motocin gdannan kap daya suka rage sannan suka sassace duk wani abu me kyau da kkasani agidannan, bayan nan suka ma musa da idi duka" "innalilliahi wa inna ilaihi raji'un" abinda umman mustapha keta fadi knan "shine kuma kke zaune a nan baraki kira police suzo ba?" mummy tayi dariyan takaici sannan tace "suzo suyi me? Zasu iya maido min da motoci nane? Ba abibda zasu iya illa investigation na qarya" umman mustpha ta matuqan tausayawa mumy sosai ta taso tayi hugging nata tana bata hkr ta kuma ce mata ta kwantar da hankalinta zatayi wa mijinta mgn in shaa Allah zai taimaketa, mummy tace ba seta fda ba masa bama tabary kawai umman mustapha tayi insisting sannan ta tambayi mummy "wannan kayaki kuma danaga anata shiryasu cikin kwalaye fa? Lafya?" Mummy tace "packing mukeyi..." kafin ta karasa umman mustapha ta katse ta "Pa...meh? Packing kuje ina? Mesa zaku tashy?" Mummy bataso gaya mata gaskiyar zancen ba tace mata kawai zata canza gda ne tunda barayi sun gano nan din, ba yadda umman mustapha batayi da mummy data hakura su cigaba da zaman su ba amma taqi seda azahar sannan tama mummy sallama ta fice. Isarta gda ta zarce dakin mijinta alhj lawal ta irga masa komi takuma buqacesa daya taimaka wa mummy, alhj lawal kamar dagaske yace wa umman mustapha karta damu he'll try his possible best harda wai dagani wannan barayi turosu akayi, ki gaya ma kawar taki karta damu za'a kai kara police station ayi invedtigation sosai har se an gano waye master mind dake behind all these mess, umma tamasa godiya sosai nan da nan ta kira mummy ta irga mata yadda sukayi da me gidan ta, mummy tadanji sanyi a ranta sannan ta mata godiya ta ajiye wayar ta cigaba da packing kayakinta dake heedayah na karatu, nanny kuwa cikinta na ciwo. Kiran maman don moha umma tayi ta labarta mata abinda ya faru itama ta tausaya wa mummy matuqa atake ta shirya tazo tamata jaje itama ta roki mummy da tayi hkr ta cigaba da zama kar ta tashy amman mummy taki nd itama bata gaya mata mesa zata bar gdan ba dan tasan muddin tagaya mata auren maman don moha da alhj ismail ze iya samun matasala dan cewa zatayi barata zauna da maci amana kamarsa ba wanda ita mummy barata so hakan ya faru ba, ahaka maman don moha ta taya mummy sukata packing kayakin se bayan la'asar ta koma gda taje tasamu mijinta ta gaya masa meke faruwa be wani nuna mata damuwarsa ba kawai de yace mata "Allah kiyaye aukuwan na gaba" itade mama batasan mesa alhj ismail ke behaving haka ba sekace alhj s.u ba amininsa bane (batasan duk ba a hankalinsa yakeyin abinda yakeyi ba, asiri alhj lawal ya masa)
[10/10, 2:22 PM] 🍬🛍💍Salma💍🛍🍬: 👮👮👩👩💥💥💥💥💥
HEEDAYAH!
💥💥💥💥💥👩👩👮👮
2⃣6⃣
written by miemie👄

2 days later, su mummy sun gama packing kap, an wanke musu sabon gdansu, taje tayi hayan masu mota irin trailers dinnan suka iso, har sun fara sa kaya cikin mota. Heedayah tana sch dake exams sukeyi but ranan friday zasu gama. Bayan manya manyan trailers sun gama kwashe kayakin tas suka fara tafiya, mal idi na cikin mota yana leading nasu to new home. Da mutane kadan mummy tayi sallama bataso shiga gdan alhj ismail ba so kawai tayi wa matarsa waya ta gaya mata, bayan sun gama waya mummy taja daddy cikin mota da taimakon nanny sannan ta rufo gdan ta bama mal musa keys din gdan daya kai wa mal ismail, hakan kuwa akayi, bayan ya kai masa ya dawo su mummy suka fice suma, basu dau lokaci dayawa ba suka iso sabon gdansu dake unguwar danjuma goje. Gdan de ba yabo ba fallasa yana da kyau ba laifi 3 bedroom flat ne da parlour, dinning seda kitchen store. Nan da nan aka shiga sauqe kaya su mummy suna shiryawa a inda ya kamata kafin a dauko heedayah sun kusan shan rabin aikin, lokaci nayi mal idi yaje ya dauko heedayah, tana ganin a canza hanyan gda ta tambayesa dalilin hakan, be boye mata ba yagaya mata shiru ne ya biyo baya haka har suka isa sabon gdan nasu tafito daga mota ta tsaya kallon gdan ba garden inda aka ajiye mata swings da slides nata, ba inda ake aje musu numerous motocinsu ba BQ inda ta dan saba labewa sometimes...mal idi yace "mushiga daga ciki ko heedayah?" Batace komi ba tabi bayansa suka shiga adaidai lokacin mummy ke fitowa daga wata daki tamata oyoyo heedayah ta kariso gun mummy, mummy tace "ya exams?" Heedayah ta amsa da "fine" mummy tace "good Allah bada sa'a, zo muje kiga dakinki ko?" heedayah bata ce komi ba, mummy ta riko fuskarta tace "stop worrying dear everythng is going to be alright in shaa Allah, anjima kadan za'a zo a hada miki swings dinki ko?" Heedayah ta gyada mata kai suka wuce dakinta yadda yake a can babban gdansu haka yake ma a nan ba abunda ya canza, arrangements din komi irin na canne hakan kuwa ba qaramin dadi yayi wa heedayah ba sede dakin can yafi wannan girma ta dago idanunta tace "thank you mummy, ina daddy?" Mummy tace "yana daki, ki canza kaya sekije ki samesa" tabata peck a goshi heedayah ta ce "toh" mummy ta fice heedayah tacire uniform nata tasaka wata yar kantinta sannan ta fito parlour taga dakuna biyu, daya na facing dakinta daya kuma na can ta duba na kusa da dakintan bata ga kowa ba sannan ta wuce dayan tana budewa taga daddy takarasa da gudu tayi hugging nasa se faman murmushi yake mata tace "daddy do you like our new home?" Daddy yamata murmushi sannan ya gayada kai tace "nima inaso amman nafison wancan, wannan gdan bekai wancan girma ba daddy" daddy ya gyada mata kai tacigaba "don't worry xanyi karatu sosai sena zama prosecutor se inyi arresting daddy'n don moha mu karbo gdanmu ko?" Murmushi sosai daddy keyi ya gyada mata kai, yafara kokarin daga hannunsa dan yashafa kanta amman ya kasa tamasa murmushi ta dago hannunsa ta rike tana wasa dashy tana basa labarin abinda ya faru sch.
[10/10, 2:22 PM] 🍬🛍💍Salma💍🛍🍬: 👮👮👩👩💥💥💥💥💥
HEEDAYAH!
💥💥💥💥💥👩👩👮👮
2⃣7⃣
written by miemie👄
Chapter 19 · 0% Book details