← Book details Heedayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 100

Sashe 20

Heedayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhj ismail kuwa ana kaimasa key'n gdan alhj s.u ya daga kafa ya wuce gdan alhj ismail ya kaimasa, alhj lawal yayi praising nasa sannan yabasa key'n motar heedayah wato prado shiko ya amsa se faman godiya yakeyi can seyayi shiru alhj lawal ya tambayesa "ko lfy?" Yace "dan uwa ynxu in kai motan nan gda kanaganin ba matsala?" Alhj lawal cikin rashin fahimta yace "wace erin matsala kuma?" Alhj ismail yace "iyali na man, in ta ganni da motar ai zata san motar gdan alhj s.u ne dan kowa ya sansu da mota" alhj lawal yayi wata jaririyar dariya sannan yace "ya kake magana haka? Da sukadai ne masu prado a kano gaba dai? In zaka dau motarka katafi toh in bahaka ba zan saida ita" alhj ismail yace "toh shknan" Alhj lawal yace "toh ko kaifa? Kaga ko an tambaya sekace ka siya wa yaranka ne ana kaisu makaranta...(masu karatu ku dubi wani hada gu a wurin alhj lawal wato yana so ne bayan an fara kai yaran alhj ismail wato muhammad da safyan makaranta da motar heedayah, mummy taga motar ta tabbata shi alhj ismail dinne ya turo musu barayi dan dama can a baya alhj lawal ya gayamata kan barayin nan turo su akayi. Anan ke nan se maganan shi alhj lawal din ya tabbata, mummy tasake trusting dinsa nd bara ta taba suspecting nasa ba) Ni zanyi tafiya ma gbe nakeji, zani abuja inje in duba company na alhj s.u dake can, alhj ismail yamasa fatan alheri sannan ya shiga motar da alhj lawal yabasa ya dawo gda yayi parking dinta a inda yake parking motocinsa. Can da yamma matarsa ta dawo frm office taje parking motarta taga sabuwar prado a gda, ta gyara parking na motar ta sannan ta shige ciki ta wuce dakin alhj ismail yamata sannu da zuwa sannan take tambayarsa "sabuwar motar dake wajen fa? Wani ne yakawo ajia?' Ya amsa da "na siyo wasu muhammad ne, ana kaisu makaranta" mama tace "wow yaayi kyau sosai Allah kara budi" alhj ismail yace "ameen".
Washegari! Nanny ta shirya heedayah sch mal idi yyi dropping nata acikin honda V8 kasancewar ita kadai ta rage ynxu se mercedes benz E350 4matic na mummy. Bayan ya sauketa sega motar su don moha wato prado'n heedayah tasha gabansu suka fiffito shida qaninsa, heedayah da mal idi suka tsaya kura wa motar ido heedayah tace "tabbas wannan mota tace" mal idi kuwa na fadin "tabbas wannan motar heedayah ce" ze mata magana knan tafara tafiya a hankali don moha ya karaso yakira sunanta ta amsa abin yabasa mamaki dan rabuwarsa data masa mgn ya jima, sannan yace "how are you?" Ta amsa da "fine" tadanyi shiru sannan tace "nice ride erin nawa wanda barayi suka sace mana ranan" don moha yace "ayya in shaa Allah, Allah zai maido dawani karki damu" heedayah bata kuma cewa komi ba har ya kaita class sannan ya juya can yana tafiya seyana tuna abinda heedayah ta fadi mar, wait firstly, "heedayah has not been talking to me, so mesa tamin mgn yau?" Wata zuciyar tace masa "just cuz tana son kushirya ne" wata zuciyar kuma tace "a'a fa zauna kayi tunani bayan da kuka gaisa metace maka?" Don moha yace "cemin fa tayi nice ride ita ansace mata motarta erin wannan" zuciyar takuma cemasa "toh ai tana nufin wannan dinne kenan nata da aka sace" atake wata zuciyar tace "ko kadan ita de kawai tana fada maka ne kasani ka tausaya mata" haka de yata sake sake a zuciya yakasa figuring out komi. Ahaka har aka tashy, mal idi yazo daukan heedayah bece mata komi game da abinda suka gani ba da safe itama haka suna isa gda ta dau jakarta tayi ciki tafara kwala wa mummy kira, mummy na tare da daddy a dakinsa ta amsa heedayah ta karaso tace "mummy, mummy naga mota na da barayi suka sace a wajen driver nasu don moha an kaisu sch dashy yau" mummy tace "whaat??? Heedayah look at me, are you sure?" Heedayah ta gyada mata kai, mummy tace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un alhj ismail! Abinda zaka saka mana dashy knan? Bayan ka siyar mana da gda still be isheka ba sanda ka turo yan fashy suka mana aika aika? To wlh kasani Allah ya fika, mugu, azzalimi, maci amana kawai" ta fashe da kuka heedayah tace "stop crying mummy ki kai karansa gun police auntin mu tace mana in aka mana sata mukai kara gun police because police is our friend ze dawo mana da abunmu" duk wannan mgn da sukeyi daddy na jinsu zuciyarsa wata irin radadi take masa ba abinda yake yi a zuciyarsa se faman jan Allah ya isa wa alhj lawal da alhj ismail. Mummy tace "let him be, in yanaga yana da wayo ai Allah yafisa mude mu dage da addu'a jeki canxa kaya kici abinci, Allah miki albarka my princess" heedayah tace "ameen" tama mummy peck a kumatu sannan ta je gun daddy taga idanunsa duk sunyi ja sun kada tace "dnt cry daddy ta matso kusa da kunnensa tace masa "ba nace zan zama prosecutor watarana ba? Zan karbo mana gdan mu da motan mu, I promise" shima ta basa peck a kumatu sannan taja trolley jakarta ta fice zuwa dakinta
[10/10, 2:22 PM] 🍬🛍💍Salma💍🛍🍬: 👮👮👩👩💥💥💥💥💥
HEEDAYAH!
💥💥💥💥💥👩👩👮👮
2⃣8⃣
written by miemie👄

2 days later, baban alhj s.u wato alhj umar kakan heedayah knan ya kira mummy ta daga ta gaishesa cikin girmamawa kamar yadda ta saba, yake cemata kwana biyu shiru, lafya daiko? Mummy bata boye wa sirkinta komi ba ta bayyana masa everything alhj umar yasha mamakin rashin hankalin da dansa wato alhj s.u daddy'n heedayah yyi na signing wa bare files na companies da properties nasa yaba ma mummy hkr yace itama da nata laifin mesa bata kirasa ta gayamasa halin da ake ciki ba yana raye, ta nuna shi ba kowanta bane knan, Mummy tabasa hkr yatambayi lafiyar heedayah, mummy "tace tana lafya" alhj umar yace to ta kwantar da hankalinta ze turo mata maqudan kudi ta kula da heedayah da kanta, ta kuma gaishe da daddy da jiki, yaso shigo musu amman shima baida lfya sosai haka hjy hadiza ma (maman alhj s.u knan), mummy tamasa godiya sosai sannan ya katse wayar.
Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa su mummy acikin small home nasu, kakan heedayah yaturo wa mummy kudade sosai wanda taqi nuna min nima wai dan gulma ta tayi yawa. Dashy ta bude 'yar business nata cikin ikon Allah sana'arta ta sayar dasu provisions, kayan sawa, accesories, bedsheets, kayan kitchen yake ta bunqasa, dubai take zuwa ta siyo su wani sa'in harda heedayah ma take zuwa in suna hutu, daddy kuwa alhmdllh rashin lfyrsa na sauki sosai mummy sun kuma komawa washington DC dr daya taba duba daddy da abaya shi ya kuma dubasa yakuma tabbatar wa mummy cewa ALS disease na daddy ya kusa sauqowa to stage 2 ya rubuta mata sabin magunguna ahaka suka dawo 9ja. Matayen alhj lawal da alhj ismail kuwa basu fasa kaiwa mummy visit ba duda ita bata taba kaimusu ba wani sa'in umman mustapha harda shi mijinta alhj lawal suke zuwa gaishe da mummy yamusu shopping sosai kuwa, alhj ismail kuwa betaba zuwa ba dake alhj lawal ya hanasa. Don moha da heedayah kuwa abun nasu worse yake ta zama dan a sati befi tamasa mgn sau biyu ba, mummy ta nemo wa heedayah malamin islamiya har gda yake zuwa yana karantar da ita nd tana picking sosai. Shekaru da dama sunja, akowace rana kuwa heedayah tashi take da sabor tsanan alhj ismail...

**!9 YEARS LATER!**
Wata kyakkyawar budurwa na hango acikin jifatu store dake jihar KANO. Se diban kaya takeyi kamar hauka takusan cika trolley'n da take ja, tana sanyaye ne dawata jar lace da kwalyarsa green ba qarya tasha dinki me tsada ga kayar daidanta kamar a jikinta aka dinka, riga da skirt ce fitted sosai yafito da dirin wannan budurwa sosai tadau green gyale ta yafa a kai ta nannade sa a wuya da shoe nd bag nata red, se leqe nake inga wace wannan budurwa dan ba qarya tabani class! But nakasa dake ta toshe fuskarta dawata dark sunglasses nide miemie ina biye da ita ina sana'ata ta gulma ahaka tagama diban abinda yamata tajeta gun biya tayi joining layi, bata jima da tsayuwa ba wani hadadden guy ya iso layin shima ya tsaya a bayan mu nide se kallonsa nake nakasa gane ko dan nigeria ne ko erin kyawawa 'yan sudan dinnan masu golden skin ne, layi na xuwa kan wannan budurwa ta miqa kayanta akafara totaling, bayan da aka gama aka gaya mata kudinta N65,760 ta dago side bag nata dake rataye a kafadarta ta ciro bundle din N500 guda ta ajiye a gefe sannan ta ciro ta N100 shima ta ajiye a gefe making N60,000 kenan sauran N5,760 tashiga irga su kamin ta gama wannan guy dake bayan mun ya ajiye wasu kudade masu yawa kamar wanda budurwannan ta ajiye amman sede nasa yadan fi yawa da kadan yace ma wanda ake biya kudin "count this" nan yashiga irgawa, budurwan kuwa ta sake baki wangalan tana kallonsa takasa fadin komi sanda cashier din yagama irgawa yace "sun cika alhj harda chengi ma" ya miqo masa change guy din yace "hold it kasha drinks dashy" cashier se washe baki yake yana masa godiya, nan da nan aka dura kayakin wannan budurwa cikin manya manyan ledoji guy din yakira wasu da su bita su kaimata motarta. Nan ne bakin wannan budurwa ya budu tace excuse me! Tare da ciro dark sunglasses dake fuskarta kyanta yasake bayyana.(ni miemie na bude baki harda digan miyau nike da kyar na rufe nace "wa nake gani kamar 'yar little 8 year old heedayah da na sani shekaru 9 da suka wuce?" Daga sama naji ance min ""ai heedayan ce" na tabe baki nace "gaskia Allah yayi hallita a nan Masha Allah". Heedayah tacigaba da mgna wa guy dinnan...
[10/10, 2:22 PM] 🍬🛍💍Salma💍🛍🍬: 👮👮👩👩💥💥💥💥💥
HEEDAYAH!
💥💥💥💥💥👩👩👮👮
2⃣9⃣
written by miemie👄
Chapter 20 · 0% Book details