← Book details Hariji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 18

Sashe 6

Hariji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yina bada baya ta doka tsalle ,ta kama waya da ƙawarta
"Ke common aiki yaci,yanzu ya biyoni harda tukwuicin kira (shiru tayi tana sauraran daya sashen) ...hmmm na zama ƴar gata fa ,
kedai bari kuɗinki na dabam ne,nasan yau ban fita sai na shaƙi miliyoyi,,hmm yi haƙuri garan baya transacting da banki saboda rashin gaskiya kuɗinshi saidai ya haƙa rami ya zuba ko in ya mutu ya iyalansa zasu sani oho!
Ohk bye
ta katse da sauri ta ɗauko shu'umar humran ta goga ,ta murza powderda bokanta ya bata a fuska,ta ɗakko wata dakakkiyar shadda yasha stone work ta baza gamida kafa ɗauri
koda ta fito saida ta kewaya ta babbar tsakar gidan yanda duk matar za suga wucewarta part ɗinsa a maimakon ta shiga ta ƙofar da yayi ma kowaccen su provided don shiga ɗakinsa

Aikuwa haqarta ta cimma ruwa,caraf a idon dukkansu dake varendar ɗin ɗakin uwargida ,sun kira me lalle tana masu red henna...
da gayya take canja salon tafiyarta ,saida tazo gifta su ,sannan tace "sannunku da ado"
"yawwa sannu da wankan iska" suka bata amsa a jere
Saidai maimakon taji haushi saima ta basar
"biki zamuyi ne akeyarfa lalle haka "
"hmm gayu wa miji"
"hmm i see"
"Ke kuma ina Zaki kin kafo dauri kamar gwaggoron da"
fari tayi,still bata nuna taji tadamu ba akan zagin daurinta da sukayi ba
"Wallahi ku dai bari,wai me gidan ne jaraban tsufa ta tashi,amma na san bai wuce in masa tausa ba,kunsan isashiyar mace ita ke shiga turakar miji da tsakar rana" tana kaiwa nan,aikuwa Nnenna ta biyota da gudu
"Inkin isa ki ci mun kwana allah ya qona ni"
"Yooo dama maraban kahuri dajahannama mutuwa,maga isashshe"
taruga da gudu,ta kewaya sassanta ta shige ta kofar da ta dace.ta rurrufe sauran qofofin sannan ta fara duddubasa ,amma ko ina bayanan ,wani ɗaki da bata taɓa ganinsa a buɗe ba ta gani ya buɗe
A cikin sanɗa tayi peeping ,kuɗi ta hango a tuttutse a ƙasa kamar bolan takardu...A take maitarta ya ƙaru
"Wow sai kace ina production room a central bank?"

Shiga tayi kai tsaye,saidai me ? suddenly ,tayi tuntuɓe da jikin ƙuliya,yashe a ƙasa ,da tuntsiraren mug na coffee
Damm!!
gabanta ya faɗi
da gudu tayi kansa tana girgiza shi ,"Allhaji lafiya,wayyo alhaji karka mutu ka barni,in ka mutu ka barni da marayun qananun yara wallahi nima binka zanyi!
shiru tayi jin still be motsa ba
Kai kodai ya mutu ne?!
da sauri ta kafa kunne akan qirjinsa saidai ba numfashi ba alamarsa
"Na shiga uku!"
da sauri ta dauki wayarta ta fara dialling number doctorn ta
"Hllo likita meye alamun mutuwa?"
"Mutuwa ai shine complete cessation of brain activities"
"likita ya zan gane mutum ya mutu,bayan daukewa numfashi?".
"ki danna jijiyar gefen hannun mutumin in baya harbawa to sai hkury,amma waye ya mutu,na jiki a ruɗe?"

kashe wayar tayi ba tare da ta bashi amsar ba,ta danna jijiyar shiru,aikuwa da sauri ta daka shillo ta ɗare ƙirjinsa,ta fara kiran an uwanta
"Ehooo babbar giwa ya faɗi,zamuja kaya,ina faɗa maku akwai get together a murtala avenue gobe,wow sai munci uwar naira"
"ke badai ƙulia bane ya mutu?"
"Aikuwa ya noshi basket ya wula barzahu"
"kedai,ya kika sani"
"ke yanzu na shigo wani private room dinsa na ganshi a mace allah yasa wannan arzikin rabo nane,sai yanzu na gane na dakina ba komai bane...inajin mugun ya tafasa kofee ne da ruwan tsaka bai sani ba ,garin rashin yardarsa ya kashe kansa
Ta qarashe wayarta gamida daura qafa daya kan daya,sannan ta fara kiran en uwan zamanta tana kwatsa ihu da kururuwa alhaji ya mutu
tana jin gida ya birkice da ihu,ta kamosa ta yar a tsakiyar palo,tasa mop ta gogo ruwan koffen ta zuba a cup din tamaida private room din ta datse ta cire makullin ta saka a aljihun doguwar rigan ta
"In adana kar ya shiga rububin gado!".
Nnenna ma daki ta koma ta kira saurayinta "Adams ,jubilee jubilee,you have to join me to jubilate ,as am telling you my alhaji kick d basket"
"what a cheerful moment,lellai we have to rejoice" cewar sauraynta daga ɗaya ɓangaren
36&37

Jimawa kadan suka fara shigowa kowa da kalar style din kukanta,wanda a zahiri duk qarya ne,me dan dama dama a ciki,banufiyar matarsa da take kuka saboda sosai taso shiga zuriyar *Ahlan musannah* ko ta baiwa idonta abincin madaran izzah da al'adun larabawa da suka riqe ,kuma sike amfani dashi kawo yau,don haka kuka sosai takeyi tana jujjuyasa.
kafin ta duqa a gaban fuskarsa ta tallafo gemunsa ,ta watsa masa rinannun idanuwarta a kansa
mijina ya za kayimun haka? ya zaka mutu a lokacin da nike ɗaukin zama dakai?ka tashi ka fada mun ba mutuwa kayi ba,ni ina zargin wannan matar tana da hannu a kashemun miji,wayyo allah na na shiga ukuna ina za nine?..."
seat room dinsa aka wuce dashi anan za ayi masa wanka akaisa makwancinsa,saidai ana kaisa maganin da yasha da zai dauke masa numfashinsa da duk wani psycho motor activities dinsa ya daina aiki,instantly ya fara kokarin recap,amma ya kasa,sai dai yasan cctv dinsa ya nadar masa komai
Itakuma bayarbiya uwar ƴan son kuɗi ghana must go ta kira en uwanta suka zo mata dashi bandir bandir,ta ringa ciccika kudi tana sakawa ana firfita mata da kudin gidan
ta hada zufa jagwa6,tana kan jan ghana must go na biyar,ta zo dai dai kofar dakin tayi arba dashi a tsaye cikin farin alawayyo da ake nade gawawwaki,yayi yafe dashi a kafada kamar wanda yake aikin umrah

Ta baya ya damqi damtsen hannunta ,a gigice ta kwantsama ihun da saida ya girgiza duk wasu window glasses na dakin,sannan ya jawo attention din en gidan

"Wayyo allah fatalwa,kayi hakury ban shirya mutuwa yanzu ba,karka kasheni ko kace in bika..."

murmushi yayi yina tuna ayar Qur'an da yike cewa "Lallai matayenku,yaranku da dukiyoyinku fitina ne ,ku gujesu..."

zurrrr hawaye ya sirnano masa a kunci,sannan ya jinjina kai ya furta a hankula "sadaqal lahul azim"(Allah madaukakin sarki kayi gaskiya)

hannunta ya rike kam kam akuma dai dai nan en gidan suka shigo ,itakuwa sai gunjin kuka takeyi

Ai suna ganinsa suka fara jada baya
"Kuliya ya za kayi mana haka ,you rest in peace ,karka 6ata makwancinka"
"Ke shiru !(ya daka masu tsawa)"
"Nasan Allah ya jarraveni da nasaba da arziki maras gaba,shi yasa nasha magani don inga in na mutu wa zai damu? sai na gane duk dukiyata kukeso ,ita wannan ma,out of greed,tun yanzu ta fara futa da jakunkunan kudi,to kuyi mun afuwa,A matsayina na Alkalin Alkalai na qasa ,zan yanke mata hukuncin da ya dace da ita a musulunce wanda ko gaban allah naje zai bani lada...

Yina kaiwa nan,ya saketa ya kama hanyar dakinsa
.
Suwait jikinsu yayi sanyi ,itakuwa da gudu taje ta wawuso kafarsa ,tana kuka kanta a qasa.

Haquri ta ringa bashi tana roqon en uwan zamanta su tayata rokonsa

Saidai sunna fara magana,ya dakatar dasu da cewa

"Meye hukuncin da musulunci ya tanazarwa 6arawo?"
shiru sukayi sun kasa magana ,sai haqury da suke cigaba da bashi

Murmushi ,irin wanda yafi kuka ciwo yayi.
Shi kenan ɗan tsumayeni...
ya bata umurni sannan ya shige study room ɗinsa
jimawa kaɗan sai gashi ya fito hannunsa ɗauke da envelope ,yaje kan kujeransa ya zauna ,yaja wani matsakaicin tebur dake a gefen sa mai ɗauke da tarho
saida ya waina ,sannan ya saka mariƙin a kunnensa
"Kazo yanzu cikin sashena with your tools"
dikda basu san ko wayeba saida gabansu ya fadi dam!

wani ƙosashshen soja ya shigo fuskarsa ba annuri,banda maiƙo da yikeyi na alamun rashin Imani
yina shigowa bai kalli kowa ba ya isa gabansa ya ƙame tare da sara masa
Sannan ya duƙa ya buɗe jakar bayansa ya fiddo wani ƙatuwar ƙulli ,ya kwance a gabansa
wuƙaƙe ne ,masu ban tsoro harda almakasai masu mariƙan noti

cikin wani irin frighten voice,yace "Ina victim ɗin chief?"
Juya yatsarsa yayi ya sauke akanta,sannan ya daura da cewa "A dazu na tambayeku ,hukuncin wacce tayi sata ,kunki fada mun,so ni zan amfani da sani na ..
Junaid ka datse mata hannun ta na hagu."

Ya baiwa mutumin umurni cikin qaraji
zaro idanuwasu dikkan su sukayi daidai nan mutumin ya damketa ya fara daureta kamar kullin goro..

"Alhaji wannan ai kafurci ne,billahillazi kana datse hnnunta nabar auren ka!!"
cewar banufiyar matarsa...

"Mtsewww,to se me? a yau inna ji dama ,zan aura wanda suka fiku komai🤷🏻‍♂️"

"ƙuliya inci darajar zuriyar da muka haifa tare dakai,alhaji duba yanda yike ƙulleni".

Dafe ƙirji yayi,ji yayi kamar ta daɗa kunna masa wutar tsanarta.

"Wannan lokacine da ya dace in sanitizing gidana,don haka,ni islamic shari'a zan amfani dashi ,dole a yanke maki hannu ko don ya zamarwa na bayanki aya ...yara kuwa da kike cewa,to kin ja masu,don kamar yanda na rubuta maki takardan sakinki anan,haka zaki kwashe gayyar yaranki ku tafi.

saida ya furzo numfashi sannan yace
Mind all of you,Yaro daya allah ya bani ,kuma shine *Mohammadul Adnan* ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka

yina kaiwa nan ya cilla mata envelope ɗin a fuska,ga sakin ki nan..

"junaid me kake jira!" da sauri ya dauki wani pintcher me hannun scissors ya saka a wuyar hannunta ya dauko wata wuqa tana tsananin sheki tsabagen kaifi ya aza akan tsakankanun qashin ...

Tsam quliyar ya bar wajen
A take taji wani nadama ya shigeta ,ji take kamar ta hadiye ranta saboda kukan da yike zuwa mata,tana hadiyeshi
yau daya ta tsani auren me dukiya...

Suma qwaqwalen sauran hutun wucin gadi suka tafi ,kenan yina nufin duk yaranmu ba nasa bane?

Razananniyar ƙaarar da ta saki shi ya dawo dasu hankalinsu

A Furgice suka miƙe ,a yayinda abunda Nnenna taga yana faruwa da ƴar uwarta ya sata sulalewa ƙasa sumammiya
Tasan ƙuliya in yasan nata tas zaisa a kasheta
tana ganin malaman gyaran jiki ,zata hau yi mata ihu gamida sambatu
"wallahi bazan qara shan komai ba,in ba wani hali kuke neman jefa ni ba"
amma haka zata murje qasa ta tubure tana d'irka mata kayan ɗa'a ...lolz inji hausawa iyayenmu

Biki sai qara qaratowa yikeyi,gashi yau saura kwana biyu biki,jikin ummy yayi luwai luwai ,saboda gyara da ya samu,nonuwanta sunyi tsantsan suna wani irin sheƙi ,sun gaggallatso riga kamar zasu faso riga
Chapter 6 · 0% Book details