Sashe 8
Gangar Jikinsa Na Aura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GANGARJIKINSA NA AURA 2 Part 2 Posted by ANaM Dorayi on 03:14 PM, 30-Apr-15 Under: Gangarjikinsa ta Aura Yace '' hanna an kwashe miki lefenki ko? Kiyihakuri zan suyo miki wasu insha Allah idan muka yialbashi wani watan'' hanna ta dago cikin ladabi datattausar murya tace'' ni na yafe duniya da lahira basai ka biyani ba wahalar zata yi maka yawa. Kawubello babu abinda zance maka sai godiya da wannan gara daka yimin Allah ya saka da alheridomin ka kwatar min yancina tun daga ranar daaka kawo inna bata sake yimin gori ba. Yanzu zanyizaman farin ciki a gidan aurena: yayai murmushiyace'' farin cikin ki shine nawa Hanna, Allah ya karasanya ki a farin ciki fiye dana yanzu'' tace amin na gode. Karshen wata nayi da bello ya dau albashi saida ya sisiyawa hanna kayayyakinta damahaifiyarsa ta kwashe cikin dare ya kawowahanna a boye yace ai hakkintane dole ya biya ta.Hanna tayi godiya ta karba haka hanna da bellosuka kasance yana kyautata mata a boye komai ya gani na sakawa kona marmari sai ya suyo mata dadaddare ya shigo mata dashi ya bata a boye ba taredaya bari mahaifiyarsa ta gani ba. Bello yana karason hanna saboda ladabinta hankali da nutsuwada uwa uba tsananin hakurinta da tawakkali itakuwa hanna har yau har wayewar gobe ta kasa masanya gurbin haisam ta mayar da bello zuciyarta.Idan bacci take yi tana kwance da bello ammamafarkin haisam take. Idan tunani take yi haisamkawai take hangowa a zuciyarta. Tana kokarin tamayar da soyayyar da take yiwa haisam kan bellosaboda ita ma ta saka masa da soyayyar, sabida irin kyautata mata da yake amma abu ya faskara hakadai take dagewa tana nunawa bello tana sonsawanda a zuciyarta ba haka bane. Wasu lokuta dayawa idan suka tashi da safe. Bello yakan ce matayaya haisam? Don jiya kina kiransa a mafarki.Hakika hanna duk sanda ta kwanta mafarkin haisam take yi ashe har ambatonsa take a fili.Saboda tsananin son da bello yake yi mata ya yardaya amince kuma zai zauna da ita a haka. Bai tabanuna mata bacin ransa ba. Ita kuma hanna sai tajitausayinsa ya kama ta nauyi da kunyarsa talullubeta. Amma yaya zata yi tunda GANGAR JIKINTA YA AURA ZUCIYARTA na wajen haisam.Matsalar gara ta wuce tsakaninta da surukarta saikuma matsalar da inna haule ta dakko ta dorawahanna ita ce har yanzu hanna ko batan wata batayiba balle ta samu ciki fada da gori a wajen innahaule babu dare babu rana. Bello yayi kokari ya wayar mata dakai akan cewa ba laifin hanna baneciki Allah ke badawa amma abu yaci tura inna hauletaki ta saurarawa hanna cewa take ga sa'anninaurenta nan dukka ciki garesu wata bakwaibakwai tunda yanzu watan hanna bakwai da aure.Yau hanna tun karfe biyun dare take kai kawo a tsakar gida bacci ya gagari idanuwanta. Duk budeidon da bello zayyi sai yaga hanna tana fita ko tanashigowa cikin dakin kaman a mafarki yake ganinta. Can yaji ana kiraye kirayen sallar asuba tayi. Yasahannu ta laluba gefensa yaji hann bata nan. Yayifirgigit ya tashi ya fito tsakar gida ya hango hanna a gaban murhu tana hura wuta ya karasa inda takeyace.' Hanna yau lafiyarkikalau kuwa tun dare kike shige da fice kinki kikwanta yanxu da asubar nan wutar me kikehurawa? Hanna ta danyi murmushi tace'' kawu kamanta yau da duku duku oganka yace zai aiko damota za kuje Agadas shine nake dora maka ruwan wanka naji yau garin da sanyi sanyi''Yayi murmushiya ce'' Ai jinsa nayi kawai meye abun turo mota daduku duku sai kace zamubar kasar'' Hanna tace''Agadas ai da nisa shi yasa kuma wata kila bakwana zakuyiba ko ? Yace' Gaskiya agadas da nisaba kuma cikin garin zamu shiga ba local government zamu je ina ganin wajen 450 Km nekuma bana jin zamu kwana ziyarar aiki zai kaimucan mu kuma yan rakiya'' Hanna tace '' Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya. Ina jin kiran assalatukafin ruwan yayi zafi ga buta ka fara yin yin Sallah ?Ta mika masa buta ta durkusa har kasa. Bello ya tsaya yana kallonta kawai saboda wata tsantsarsoyayyarta ce take kara sarke masa zuciya.Musamman wannan kulawa da ladabi da Hannatake masa, ya karbi butar ya shiga bandaki, kafinya idar da sallar Hanna ta hada masa ruwa wanka .Ya tashi ya shiga wanka. Kafin ya fito ta debo wankakkaun kayansa data wanke ta goge masa tadora akan gado ta goge masa takalmin da zai sakamar yadda tasaba masa kullum. Bayan yakammala yana goge gogensa da yan shafe shafesai ya dauko kayan da Hanna ta fitar masa ya saka.Tazo tana balle masa maballin wuyan rigarsa. Yayi murmushi yace'' Hanna na gode da irin wannahidima da kulawa da kike nunamin wannan yasaina kara sonki dari bisa dari, idan akwai soyyya datafi dari bisa dari ina miki Hanna sai dai ni anyakuwa na sami kwaya dayan nan kacal da nake so asanmin a cikin darin da ake yiwa haisam ?Cikin kunya hanna tace'' Haba daya kacal ai kafiguda daya'' yace '' a.a zancen gaskiya muke, nawaaka karamin ? Tayi dariya tace'' kawu ka wucegoma ma zaka kai sha biyar'' su duka suka tuntsireda dariya. Yace '' to tunda a wata bakwai na samigoma sha biyar nan da shekara bakwai zan iya tadda haisam'' suka sake tuntsirewa da dariya.Muryar inna haule ce ta katse musu dariyar da sukeyi tana bakin kofar dakinsu tana cewa'' tun dazumagana nake muku baku jini ba kun shige dakikuna tuntsira dariya da duku dukun safiyar nan tomotar ofishinku ce tazo suna ta kwankwasa gida . Daman Hanna abinda kika sani kenan ki shiga dakida miji kina dariya aikin kenan ciki fal kashi, babugurbin kwanciyar Da sai gurbin tarin kashi'' Hannatayi kasake yayi sanyi fara.ar da take yi ta koma cikiranta ya baci damin da ana siyar da ciki da ta suyohaka kuma da a wani waje ake nemoshi da taje ta nemo duk wahala koda kuwa zata mutu ne. Ko tahuta da zagin da gorin da ake yi mata. Bello yayiajiyar zuciya yace'' inna gani nan zuwa shiryawanake'' ta wuce ta tafi tana tsaki tana cewa'' Kaje kadawo dai daga tafiyar kazo mu zauna muyimaganar saboda bazai yuba, in zuba muku ido haka kawai aure wata bakwai kenan babu ciki baalamarsa kaina da kafafuwana turawa yarinyaabinci nake sai dai taci tayi kashi kawai. Ai ba dantazo ta cika mana shadda muka aurota ba mumamuna so muga dan jariri a gidanmu. Tunda tashanye ka ta asurce ka baka ganin lefinta to ni bata asurceni ba dole ka karo aure idan ma baza kasake taba, kai dole ma ka sake ta ka auro maihaihuwa don daki daya garemu a gidan nan'' Harinna haule tayi nisa ta juyo ta dawo ta tsaya a kofardakinsu Hanna tace'' Hanna kiyi ki fito daga dakinnan yau duk ke zaki yi aikin gidan nan shara wanke wanke surfe da girki ki fara debo ruwatukunna idan kin cika randunan gidan kakaf sai kifara aikin gida da yamma kuma kije gona ki tsinkowake da gyada dan sun nuna. Yau wacce kukeaikin tare indo aikenta zanyi magarya wajenkawata. Tunda ba ciki garekiba ba goyo ba ai wannan aikin bazai gagarekiba, sai dai idan kinjikashi sai kiyi a gonar tunda cikinki sai kashi babuhaihuwa. Kinga kuwa kashin naki ya zamar mintaki a gonar kinga kin taimaka kema'' Bello maduya fisata baisan sanda yace'' Haba inna ki dainayiwa hanna gorin haihuwa ba laifinta bane rashin haihuwa Allah ne yake bayarwa inna dama haryanzu Hanna ce take debo ruwa a rafi ina almajiriindana dauko aiki nace zan dinga biyansa. Ita taji daaikin gidan su kuna almajiran suje gonar. Hannatasa hannu ta toshe masa baki tace '' yi shiru karkasa taji haushina, mahaifiyarka ce babu komai duk zanyi aikin. Inna Haule ta rike baki tace'' inyedannan ka fara fada in fada dani akan matarkalallai abun babba ne jeka ka dawo ka sameni donwallahi ina ganin zamanka ya kare da wannanyarinyar mai kama da tumatir ina ganin rabaka takesotayi da kowa a duniya har dani dana haifeka . Ba'a haiyacinka kake ba na sani bayinka bane. Tatafi tana surutanta dai barkatai. Hawaye yana zubashar daga idon Hanna. Bello yasa hannu ya gogemata zuciyarsa cike da tsananin tausayinta ammayafi jin tausayin kansa da kansa. Saboda zaifi hannashiga wani hali,idanmahaifiyarsa tasa ya saketa don shine yafi sontafiye da yadda take sinsa idan ya rabu da hanna yarabu da farin cikin rayuwarsa. Kalma daya ce yasanidan yafadawa Hanna duk irin bacin ran da takezata yi dariya idan ya ambaci sunan Haisam . Yayi dan murmushi ya kalleta yace'' Hanna dama ace ayanzu kina da ciki ki haifanmun da namiji in sakamasa suna haisam. Hanna ta dago ta dubeshiidanuwanta a cike da hawaye sunyi jawur donkuka amma saida murmushi ya subuce mata a taketaji zuciyarta ta fara dan hucewa daga tsananin tafasar da take yi saboda kunar maganganun dainna Haule ta fada mata. Hanna taji wani dan sanyi aranta wani abu ya dasu a zuciyarta da bello yace ''dama ace ana da ciki ta haifi da namiji ya saka masasuna Haisam taji dama ace hakan faru mana. Ammadata tuna yanxu ma haka al'ada take don haka zancen ciki ma babu shi sai ta sake rushewa dakuka. Bello ya jawota ya rungumeta akirjinsa yanashafa lallausan gashinta yace'' Hanna lallai yauranki ya baci sosai har in kira miki Haisam ammakici gaba da kuka kiyi hakuri ki yafewa innata mucigaba da yi mata addu'a Allah yasa ta gane gaskiya Allah ya cusa mata soyayyarki a ranta. Hannatayiajiyar zuciya tace amin'' amma ka tayani addu'aAllah ya bani ciki kafin karshen watan nan inaganin haka zai saka soyayyata a zuciyar inna. Belloyace amin ya Allah, zan dukufa da addu'a kema kiyiAllah ya amsa mana. Ya goge matahawayen idanuwanta ya sumbaci kumtunta yace'' Haisamsunan danmu fa. Hanna ta kyalkyale da dariya tarufe ido sai taji wani farin ciki ya lullubeta. Tatsugunna ta jawo takalminsa ta fara saka masa akafa tana sake goge masa da tsumma. Ta feshemasa jikinsa da turare tace'' Kawu bello Allah ya kiyaye hanya kuje lafiya ku dawo lafiya. Yace aminHanna Allah yasa nazo na sameki lafiya cikin farinciki'' yana tafiya yana waiwayan hanna, itama ta fitohar bakin kofar dakin ta tsaya tana daga masahannu har ya shiga dakin mahaifiyarsa sannanhanna ta koma daki. A zaune a gefen gado Bello ya iske mahaifiyarsa tana tunani tana gayda kai yadurkusa