Sashe 2
Gangar Jikinsa Na Aura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da iya abu ta fita takaba sai maigari ya hado malaman garin da masu fada aji na garin da yanuwan malam Habu don raba gadonsa ga iyalansa.A zauren gidan aka zazzauna ga iya abu gayayanta kakaf mata da maza ga hanna a gefe.Itama da iya salmai. Maigari yace'' a karantawamamacin kulhuwallahu kafa uku uku, da inna a'adaina kalkausar uku uku aka shafa Allah yakaikabarinsa. Sai maigari ya fara da cewa'' malamHabu ya rasu yabar mace daya da yaya takwas.Dukiyarsa kuwa wannan gidan ne da kumakatuwar gona. Amma tun ranar daya mutu akabiya masa basussuka da ake binsa da dan kudin daya bari. Ga manyan malamai nan zasu raba gado.Ga sunayen 'yayan nan a wajensu zasu shiga cikingidan su tsatstsaga su bawa kowa nasa bangaren.Iya abu ta nisa tace ina da magana nidai nicematarsa uwar yayansa kuma bare daya ce Hannedon haka a tabbata an bata bangarenta daban kar a saka min ita cikin kason 'yayana azo ana rigima.Maigari yace'' ai abu rabon gado ba'a cewa bareAllah ne ya raba da kansa don haka duk yadda takama haka za'ayi. Malamai sun yi iya kokarinsu sunkacaccala dan mitsitsin gidan nan d gona. Allahcikin ikonsa hanna bata tashi da komai ba sai rumbun ajiyar abinci,wani dam mitsitsine kasace turmus a kasan da gidan tururuwa sai dan wanibangare karami a tsakar gida shine kashin hanna agona kuwa bata ciki. Murna ta lullube iya abu gonada gaba daya dakunan gidan nata ne da yayanta sai tace'' wannan rabo yayi daidai to yanzu ta tashidaga dakin nan'' mai gari yace haba abu har yanzutsangwamar da kike yiwa hanne baki bari ba harmahaifinta ya mutu bakya rangwama mata ba''iyaabu tace a'a babu wani rangwame yan haya zansaa sauran dakunan ina karbar kudi wannan abu ne fa na gado. Nan fa duk suka hadu suna ta bawa iyaAbu hakuri ta barHanna taci gaba da zama a dakinda take har Allah ya yanke mata wannan zamatunda komai dadewa aure zata yi. Iya Abu takekashe idanuwanta ta ce in anga ta yadda Hannayauta sake kwana cikin dakin nan nata to ta bata kudin haya ne a matsayin tana haya.A cikin mutanen dake wajen harda Alh bilya ya ceto tunda Abu tace haka shi yayi alkawari zai dingabiyawa Hanne kudin haya daga yau ya tambayiAbu ko nawa ne kudin hayar dakin da hanne keciki ta kai kaice ta zambada kudi ya zaro ya biya ba tare da ya nemi ragi ba, ya biya na shekara ya saniya abu kora da hali take yiwa Hanne ta zambadakudi dan ace yayi tsada a kama mata a wani gidacikin ikon Allah sai taga ya biya.Mai gari da sauran mutanen dake wajen suka dingashiwa Alh bilya albarka, Hanne ita da baba Uba ne kadai suka san manufar Alh Bilya shi a nufinsaauren hanna zaiyi shi yasa ya fara mata hidima,wani gululun bakin ciki ne ya dira a zuciyar Hannamusamman da ya biya mata kudin haya ta san lallaida gaske yake auren nata yake so yayi ita ko garaa kasheta da a daura mata aure da wannan mutumin kamar tace bata son kudin hayar baza tazauna a gidan ba karya biya sai tayi tunanin in bagidan uban nata ba a ina zata zauna saita hakurakawai tayi shiru idan tace zata koma gidan iyaSalmai to ai daki daya ne kacal a gidan dan karamiita da wada suke kwana a dakin ba zaiyu ita ta hadu da Wada a daki daya ba saboda yanzu Wadashekararsa goma sha takwas yama girme ta dashekara daya don haka ya haramta su cusu a dakidaya bayan nan babu gidan wanda zata iya zuwata zauna duk danginta.Da daddare bayan kowa ya shige bacci ya kwanta hanna na juyi a yar katifar ta kasa bacci tsananinbakin ciki ne ya dameta a ranta bau abinda takenanatawa a ranta sai zancen hayar na. Ita da gidanubanta yau ta zama 'yar haya sai ta rushe da kukahar ta gaji. Tace''Allah kana ji, kuma kana ganina,kana kuma sane da irin abubuwan bakin cikin da nake gani tun ranar da mahaifiyata ta sakoni aduniya Allah ka fitar dani. Kaine gatana ya sarkinsarakuna. A haka Hanna ta kasance har shekaraguda da rasuwar mahaifinta. Yau taci abinci gobe tarasa wannan bai dameta ba sosai irin zurga zurgarda Alh Bilya yake yi a danginta yana cewa shifa yana so ya aureta. Dan har yaje ya sanarwa damaigari. Maigari yasa aka kira Hanna fada ya shaidamata abunda Alh Bilya yake nema a wajenta shin taamince zata aureshi, ta yarda tana so a dauraauren ? Hanna ta fito gar da gar ta fadi gaskiyatace'' ranka ya dade banki jin shawarar da ka bani ba amma dan Allah ina so a barni haka bana so inauri kowa. Gaba daya aka dau salati aka fara yiwaHanna ''cari to ba'a garin nan ba. Duk garin nanwacece ta taba kaiwa shekara goma sha takwas baa yi mata auren fari ba? Hanna tace'' ba zan iyaauren Alh Bilya ba a matsayinsa na mahaifina dan ni tamkar mahaifi yake a wajena. To haka akayi daHanna a fada. Alh bilya yaji haushin Hanna data kiyarda amma yasan tuggun da zai tafka mata yarama.Bayan anyi haka da hanna a fadar maigari dakwana uku. Alh bilya yazo har cikin gidan su hanna da rana tsaka . Hanna na daki a kwance tanajin yunwa tana jiran a kawo mata abinci daga gidaniya salmai tana fargabar ko suma basu yi abincin bane yau sai ta jiyo muryar alh bilya yana rafsasallama iya abu ta fito iya abu tace''yau alhaji dakanka a gidan namu. Yace'' eh wallahi zuwa nayi mu gaisa inji ko yaushe kudin hayar dana biyayake karewa? Iya abu tayi dariya ta sosakwarkwata a kai tace'' ai sauran wata uku ne inajin''ya ce''to ki raba kudin hayar gida hudu ki daukikashi uku naki ki bani kashi daya ragowarwatannin uku ki kori hanne daga dakin da take haya in bata biya ki ba ba ruwana'' iya abu ta batarai tace. To ni yanzu na kashe kudi yaya kake sonayi a ina zan samo kudinka da zan dawo makadashi ? Hanne fakara'u ko sisi bata dashi ina zayasamo wani kudin haya ta biyani? Gaskiya alh bilyakai ya dace kaci gaba da biyan kudin haya don haka kace a gaban maigari''yace''kash ni bakifahimceniba abu ba don in takura miki ba nace kibani sauran kudi ji rike sauran kudin ina nufinyanzun ki koro hanne daga dakin da take donnibada yawuna take zaune a dakin ba kuma ba'akudina ba. Iya abu tayi dariya tace''oh na gane wato yanzu dai in rike ragowar kudin watanniukun da suka rage kenan sannan in koro hannewaje idan bata biyani kudin haya ba ko. Ko bahaka kake nufi ba? Alh bilya yayi dariya yace''hakanake nufi mana.iya abu tace an gama ai a gabankazan koro shegiyar. Gaban hanna ya yanke ya fadi tayi zumbur ta tashi zaune ta dafe kirji tana tainnalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Iya abu ta wangalelabulen dakin ta shiga budik ta sami hanna a kankatifa a zaune ta mikawa hanna hannu tace''banikudi. Hanna tace''bani da kudi. Iya abu ta wawurijakar hanna zata wurgar waje hanna ta rike tana mata magita tayi hakuri dan Allah ta rufa mata asiri,amma kamar zuga iya Abu take.Hanna ta fito da gudu daga dakin ta zo ta durkusaa gaban Alh Bilya tana rokonsa dan Allah yayihakuri ya bar mata kudin hayar wata uku kafin nanzatasan yadda zatayi ta sake biya. Amma yayikunne uwar shegu da ita yana cewa''yauwa Abu ki tattaro kakaf kayanta ki watso''ana cikin wannanhali sai ga Wada nan dauke da kwanan abinci yakawowa Hanna abincin rana ya sami Hanna kacekace tana kuka a durkushe a gaban Alh Bilya tanarokonsa iya Abu kuwa tana ta faman watsi dakayanta. Cikin kuka Hanna tace'' wada kaga halin da nake ciki jeka ka kira iya Salmai tazo ta rokarsu.Nan da nan wada ya garzaya dan ya shaidawa iyaSalmai halinda yazo ya tarar da Hanna. Bayantafiyar wada ba dadewa sai ga iya salmai da maigarida tawagarsa sun shigo gidan suka iske hanna acikin wannan hali. Maigari ya ce'' subhanallai Alh Bilya da girmanka meye haka? Alh Bilya yace''ranka ya dade babu yadda za'ayi taci gaba da zamaa cikin kudina bayan bata sona shi yasa nazo na ceto in Abu taga zata bar Hanna taci gaba da zama akyauta to. Amma ba dai nine ke biyan kudin nandole Hanne ta fita don bazan barta taci gaba da zama a kudina ba tunda bata sona. Nan dai akahau bawa Alh Bilya da iya Abu baki ana musuwa'azi da nasihohi akan rayuwa ce kuma sumasuna da yaya zasu iya mutuwa su bar yayansusuma ayi musu haka. Hanna tasa gefen zaninta tagoge hawaye ta mike daga durkusan da take yi ta juya ta kalli su maigari tace'' ku kyalesu ni nahakura da zama a dakin zan koma rumbun inzauna hanna ta fara dibar jakunkunan ta tanashigarwa cikin rumbun nan mai gidan tururuwa dacinnaka ga bunhunhunan dawa da kaikayi.....ANA CIKIN WANNAN hali ne Musa danmakwabtansu ne ya shigo yace'' wasu maza gudabiyu gasu nan a waje wasu farare ne kamarlarabawa sunce suna neman Hanne 'yar gidanMalam Habu. Mai gari yace'' larabawa daga ina ?Musa yace sunce daga Niger suke maigari yace'' to muma ai tafiya zamu yi mu tafi kawai, har Hannasuka yiyo waje wasu samari farare sol sol ne gudabiyu a tsaye a kofar gidan daya daga gani kotambaya babu jinin hanna ne don kamar su dayakamar an tsaga kara maigari yace ''kune bakindaga Niger ? Suka amsa 'eh' sannan suka duka suka gaishe dasu maigari. Hanna ta tsaya a gefetana kallon wadan baki nata bata san suba ammadaya daga cikin samarin kamarsu daya futik dagagani babu tambaya daga tsatso daya suka fito.Maigari yace'' to ga Hanna . Yaya kaman baku sanjuna ba. Mai kama da Hanna yace'' ni sunana Ahmad wannan abokina ne sunansa Bello Madu. Nikanin mahaifiyar hanna ne uwa daya uba daya.Hanne bata taba ganina ba ban taba ganinta bashine nazo na nemota don muga juna'' Hanna najinhaka sai ta daka tsalle ta rungume Ahmad sai itadashi suka rushe da kuka. sai suka rushe da kuka. Maigari da sauran mutane sai suka hau girgiza kaisuna masu tausayinsu. Maigari yace'' Alhamdulillahgara da Allah ya kawo ku sai mu koma daga cikin atattauna. Bayan kowa ya sami waje ya zauna,Hanna ta tashi ta dauki kwano ta kwalfo musuruwan sha a randa ta kawo